< Ƙidaya 33 >
1 Ga wuraren da Isra’ilawa suka yi sansani sa’ad da suka fito runduna-runduna a ƙarƙashin Musa da Haruna daga Masar.
2 Bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya rubuta wuraren tafiye-tafiyensu da sansaninsu. Ga yadda tafiye-tafiyen suka kasance.
3 Isra’ilawa sun tashi daga Rameses a rana ta goma sha biyar, ga watan fari, kashegarin Bikin Ƙetarewa. Suka fita gabagadi a gaban dukan Masarawa,
4 waɗanda suke binne gawawwakin’ya’yan farinsu da Ubangiji ya karkashe; gama Ubangiji ya hukunta allolinsu.
5 Isra’ilawa suka tashi daga Rameses, suka yi sansani a Sukkot.
6 Suka tashi daga Sukkot, suka yi sansani a Etam, a gefen hamada.
7 Suka tashi daga Etam, suka koma baya zuwa Fi Hahirot, wajen gabashin Ba’al-Zafon, suka yi sansani kusa da Migdol.
8 Suka tashi daga Fi Hahirot, suka ratsa cikin teku zuwa hamada, bayan sun yi tafiya kwana uku a cikin Hamadan Etam, sai suka yi sansani a Mara.
9 Suka tashi daga Mara, suka tafi Elim, inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu, da itatuwan dabino guda saba’in, suka yi sansani a can.
10 Suka tashi daga Elim, suka yi sansani kusa da Jan Teku.
11 Suka tashi daga Jan Teku, suka yi sansani a Hamadan Sin.
12 Suka tashi daga Hamadan Sin, suka yi sansani a Dofka.
13 Suka tashi daga Dofka, suka yi sansani a Alush.
14 Suka tashi daga Alush, suka yi sansani a Refidim, inda babu ruwan da mutane za su sha.
15 Suka tashi daga Refidim, suka yi sansani a Hamadan Sinai.
16 Suka tashi daga Hamadan Sinai, suka yi sansani a Kibrot Hatta’awa.
17 Suka tashi daga Kibrot Hatta’awa, suka yi sansani a Hazerot.
18 Suka tashi daga Hazerot, suka yi sansani a Ritma.
19 Suka tashi daga Ritma, suka yi sansani a Rimmon Ferez.
20 Suka tashi daga Rimmon Ferez, suka yi sansani a Libna.
21 Suka tashi daga Libna, suka yi sansani a Rissa.
22 Suka tashi daga Rissa, suka yi sansani a Kehelata.
23 Suka tashi daga Kehelata, suka yi sansani a Dutsen Shefer.
24 Suka tashi daga Dutsen Shefer, suka yi sansani a Harada.
25 Suka tashi daga Harada, suka yi sansani a Makhelot.
26 Suka tashi daga Makhelot, suka yi sansani a Tahat.
27 Suka tashi daga Tahat, suka yi sansani a Tera.
28 Suka tashi daga Tera, suka yi sansani a Mitka.
29 Suka tashi daga Mitka, suka yi sansani a Hashmona.
30 Suka tashi daga Hashmona, suka yi sansani a Moserot.
31 Suka tashi daga Moserot, suka yi sansani a Bene Ya’akan.
32 Suka tashi daga Bene Ya’akan, suka yi sansani a Hor Haggidgad.
33 Suka tashi daga Hor Haggidgad, suka yi sansani a Yotbata.
34 Suka tashi daga Yotbata, suka yi sansani a Abrona.
35 Suka tashi daga Abrona, suka yi sansani a Eziyon Geber.
36 Suka tashi daga Eziyon Geber, suka yi sansani a Kadesh, cikin Hamadan Zin.
37 Suka tashi daga Kadesh, suka yi sansani a Dutsen Hor, a iyakar Edom.
38 Bisa ga umarni Ubangiji, Haruna firist, ya hau Dutsen Hor, inda ya mutu a rana ta fari ga watan biyar, a shekara ta arba’in, bayan Isra’ilawa suka fito daga Masar.
39 Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku, sa’ad da ya mutu a Dutsen Hor.
40 Sarki Arad Bakan’ane, wanda yake zaune a Negeb na Kan’ana, ya ji labari cewa Isra’ilawa suna zuwa.
41 Suka tashi daga Dutsen Hor, suka yi sansani a Zalmona.
42 Suka tashi daga Zalmona, suka yi sansani a Funon.
43 Suka tashi daga Funon, suka yi sansani a Obot.
44 Suka tashi daga Obot, suka yi sansani a Iye Abarim, a iyakar Mowab.
45 Suka tashi daga Iyim, suka yi sansani a Dibon Gad.
46 Suka tashi daga Dibon Gad, suka yi sansani a Almon Dibilatayim.
47 Suka tashi daga Almon Dibilatayim, suka yi sansani a duwatsun Abarim, kusa da Nebo.
48 Suka tashi daga duwatsun Abarim, suka yi sansani a filayen Mowab kusa da Urdun, ɗaura da Yeriko.
49 A can filayen Mowab, suka yi sansani kusa da Urdun ɗaura da Bet-Yeshimot har zuwa Abel-Shittim.
50 A filayen Mowab kusa da Urdun ɗaura da Yeriko ne Ubangiji ya ce wa Musa,
51 “Ka gaya wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa Kan’ana,
52 ku kori dukan mazaunan ƙasar a gabanku. Ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsu, da siffofinsu na zubi, ku kuma rurrushe dukan masujadansu na kan tudu.
53 Ku mallaki ƙasar, ku kuma zauna a ciki, gama na ba ku ƙasar, ku mallake ta.
54 Ku rarraba ƙasar ta wurin jefan ƙuri’a, bisa ga kabilanku. Kabilar da take babba, a ba ta babban gādo, ƙarami kabila kuwa, a ba ta ƙaramin gādo. Duk abin da ƙuri’a ta ba su, shi zai zama nasu. Ku rarraba wannan bisa zuriyar kakanninku.
55 “‘Amma in ba ku kori mazaunan ƙasar ba, waɗanda kuka bari su ci gaba da zama, za su zama muku hakki a idanunku, da kuma ƙayayyuwa a bayanku. Za su ba ku wahala a ƙasar da kuke zama.
56 Sa’an nan kuwa zan yi muku abin da na shirya yin musu.’”