< Ƙidaya 31 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa,
さて主はモーセに言われた、
2 “Ka ɗaukar wa Isra’ilawa fansa, a kan Midiyawa. Bayan wannan za ka mutu, a kuwa tara ka ga mutanenka.”
「ミデアンびとにイスラエルの人々のあだを報いなさい。その後、あなたはあなたの民に加えられるであろう」。
3 Saboda haka Musa ya ce wa mutane, “Ku shirya waɗansu daga cikin mazanku, su tafi su yi yaƙi da Midiyawa don su ɗaukar wa Ubangiji fansa a kansu.”
モーセは民に言った、「あなたがたのうちから人を選んで戦いのために武装させ、ミデアンびとを攻めて、主のためミデアンびとに復讐しなさい。
4 Ku aiki maza dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila.
すなわちイスラエルのすべての部族から、部族ごとに千人ずつを戦いに送り出さなければならない」。
5 Saboda haka aka samo mayaƙa dubu goma sha biyu shiryayyu don yaƙi, maza dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila.
そこでイスラエルの部族のうちから部族ごとに千人ずつを選び、一万二千人を得て、戦いのために武装させた。
6 Musa ya aike su zuwa yaƙi, dubu ɗaya daga kowace kabila, tare da Finehas ɗan Eleyazar, firist, wanda ya ɗauki kayayyaki daga wuri mai tsarki da ƙahoni don kiran yaƙi.
モーセは各部族から千人ずつを戦いにつかわし、また祭司エレアザルの子ピネハスに、聖なる器と吹き鳴らすラッパとを執らせて、共に戦いにつかわした。
7 Suka yi yaƙi da Midiyawa, suka kashe kowane mutum yadda Ubangiji ya umarci Musa.
彼らは主がモーセに命じられたようにミデアンびとと戦って、その男子をみな殺した。
8 A cikin waɗanda aka kashe kuwa akwai Ewi, Rekem, Zur, Hur da Reba; sarakuna biyar na Mediyawa. Suka kuma kashe Bala’am ɗan Beyor da takobi.
その殺した者のほかにまたミデアンの王五人を殺した。その名はエビ、レケム、ツル、フル、レバである。またベオルの子バラムをも、つるぎにかけて殺した。
9 Isra’ilawa suka kwashe mata da yaran Midiyawa, a matsayin bayi. Suka kwashe shanunsu da tumakinsu da kuma dukan dukiyarsu, a matsayin ganima.
またイスラエルの人々はミデアンの女たちとその子供たちを捕虜にし、その家畜と、羊の群れと、貨財とをことごとく奪い取り、
10 Suka ƙone dukan garuruwan da Midiyawa suke zama, da dukan sansaninsu.
そのすまいのある町々と、その部落とを、ことごとく火で焼いた。
11 Suka kwashe dukan ganima haɗe da mutane da dabbobi,
こうして彼らはすべて奪ったものと、かすめたものとは人をも家畜をも取り、
12 suka kawo bayi da ganiman nan, wurin Musa da Eleyazar firist, da kuma jama’ar Isra’ilawa, a sansaninsu a filayen Mowab kusa da Urdun daga ƙetaren Yeriko.
その生けどった者と、かすめたものと、奪ったものとを携えて、エリコに近いヨルダンのほとりのモアブの平野の宿営におるモーセと祭司エレアザルとイスラエルの人々の会衆のもとへもどってきた。
13 Musa, da Eleyazar firist da dukan shugabannin jama’a, suka fito suka tarye su a bayan sansani.
ときにモーセと祭司エレアザルと会衆のつかさたちはみな宿営の外に出て迎えたが、
14 Musa kuwa ya husata da shugabannin sojojin da suke shugabannin dubbai da shugabannin ɗari-ɗarin da suka dawo daga yaƙi.
モーセは軍勢の将たち、すなわち戦場から帰ってきた千人の長たちと、百人の長たちに対して怒った。
15 Ya tambaye su ya ce, “Kun bar dukan mata da rai?
モーセは彼らに言った、「あなたがたは女たちをみな生かしておいたのか。
16 Su ne waɗanda suka bi shawarar Bala’am suka kuma zama sanadin sa Isra’ilawa suka juya wa Ubangiji baya, har ya kawo abin da ya faru da Feyor, har annoba ya kashe dukan mutanen Ubangiji.
彼らはバラムのはかりごとによって、イスラエルの人々に、ペオルのことで主に罪を犯させ、ついに主の会衆のうちに疫病を起すに至った。
17 Yanzu ku kashe dukan yara maza, ku kuma kashe kowace macen da ta yi lalata da namiji,
それで今、この子供たちのうちの男の子をみな殺し、また男と寝て、男を知った女をみな殺しなさい。
18 amma ku bar kowace yarinyar da ba tă taɓa yin lalata da namiji ba.
ただし、まだ男と寝ず、男を知らない娘はすべてあなたがたのために生かしておきなさい。
19 “Dukanku da kuka kashe mutum, ko kuka taɓa wani da aka kashe, dole ku kasance a bayan sansani har kwana bakwai. A rana ta uku da rana ta bakwai dole ku tsabtacce kanku da kuma bayinku.
そしてあなたがたは七日のあいだ宿営の外にとどまりなさい。あなたがたのうちすべて人を殺した者、およびすべて殺された者に触れた者は、あなたがた自身も、あなたがたの捕虜も共に、三日目と七日目とに身を清めなければならない。
20 Ku tsarkake kowace taguwa da kuma kome da aka yi da fata, da gashin akuya, ko kuwa itace.”
またすべての衣服と、すべての皮の器と、すべてやぎの毛で作ったものと、すべての木の器とを清めなければならない」。
21 Sa’an nan Eleyazar firist, ya ce wa sojojin da suka je yaƙi, “Wannan ita ce ƙa’idar da Ubangiji ya ba wa Musa.
祭司エレアザルは戦いに出たいくさびとたちに言った、「これは主がモーセに命じられた律法の定めである。
22 Zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, kuza, darma
金、銀、青銅、鉄、すず、鉛など、
23 da dukan abin da wuta ba ta iya ci, dole yă shiga wuta sa’an nan zai zama da tsabta. Amma dole a kuma tsarkake ta da ruwan tsarkakewa. Duk abin da wuta za tă iya ci, dole a shigar da ita a ruwan tsarkakewa.
すべて火に耐える物は火の中を通さなければならない。そうすれば清くなるであろう。なおその上、汚れを清める水で、清めなければならない。しかし、すべて火に耐えないものは水の中を通さなければならない。
24 A rana ta bakwai za ku wanke tufafinku, sa’an nan za ku tsarkaka, bayan haka ku shigo sansani.”
あなたがたは七日目に衣服を洗わなければならない。そして清くなり、その後宿営にはいることができる」。
25 Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce,
主はモーセに言われた、
26 “Da kai da Eleyazar firist, da shugabannin jama’a, ku ƙidaya dukan mutane da dabbobin da aka ci da yaƙi.
「あなたと祭司エレアザルおよび会衆の氏族のかしらたちは、その生けどった人と家畜の獲物の総数を調べ、
27 Ku kasa ganimar kashi biyu, ku ba sojojin da suka tafi yaƙi kashi ɗaya, kashi ɗaya kuma ku ba wa jama’a.
その獲物を戦いに出た勇士と、全会衆とに折半しなさい。
28 Daga sojojin da suka je yaƙin kuwa, ka ware ganima wa Ubangiji, ka ɗauki ɗaya daga cikin mutum ɗari biyar, da shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, da tumaki ɗari biyar.
そして戦いに出たいくさびとに、人または牛、またはろば、または羊を、おのおの五百ごとに一つを取り、みつぎとして主にささげさせなさい。
29 Ka ɗauki wannan sashe daga rabin rabonsu ka ba wa Eleyazar firist, a matsayin sashe na Ubangiji.
すなわち彼らが受ける半分のなかから、それを取り、主にささげる物として祭司エレアザルに渡しなさい。
30 Daga cikin rabin rabon Isra’ilawa, ka zaɓi ɗaya daga kowane hamsin na mutane, shanu, jakuna, tumaki, awaki ko kuma sauran dabbobi. Ka ba wa Lawiyawan da suke lura da tabanakul na Ubangiji.”
またイスラエルの人々が受ける半分のなかから、その獲た人または牛、またはろば、または羊などの家畜を、おのおの五十ごとに一つを取り、主の幕屋の務をするレビびとに与えなさい」。
31 Saboda haka Musa da Eleyazar suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa.
モーセと祭司エレアザルとは主がモーセに命じられたとおりに行った。
32 Yawan ganimar da sojoji suka kawo ita ce tumaki 675,000
そこでその獲物、すなわち、いくさびとたちが奪い取ったものの残りは羊六十七万五千、
33 shanu 72,000
牛七万二千、
34 da jakuna 61,000.
ろば六万一千、
35 Akwai kuma mata 32,000 da ba su yi lalata ba da namiji ba.
人三万二千、これはみな男と寝ず、男を知らない女であった。
36 Kashin da aka ba sojoji waɗanda suka tafi yaƙi shi ne, tumaki 337,500,
そしてその半分、すなわち戦いに出た者の分は羊三十三万七千五百、
37 tumakin da aka ware wa Ubangiji kuwa 657 ne;
主にみつぎとした羊は六百七十五。
38 shanu 36,000, shanun da aka ware wa Ubangiji kuwa 72 ne;
牛は三万六千、そのうちから主にみつぎとしたものは七十二。
39 jakuna 30,500, jakunan da aka ware wa Ubangiji kuwa 61 ne;
ろばは三万五百、そのうちから主にみつぎとしたものは六十一。
40 mutane 16,000, mutanen da aka ware wa Ubangiji kuwa 32 ne.
人は一万六千、そのうちから主にみつぎとしたものは三十二人であった。
41 Musa ya ba wa Eleyazar abin da aka ware wa Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
モーセはそのみつぎを主にささげる物として祭司エレアザルに渡した。主がモーセに命じられたとおりである。
42 Kashin da aka ba wa Isra’ilawa, wanda Musa ya ware daga cikin na waɗanda suka tafi yaƙi,
モーセが戦いに出た人々とは別にイスラエルの人々に与えた半分、
43 kashin da aka ba wa jama’a kuwa tumaki 337,500 ne,
すなわち会衆の受けた半分は羊三十三万七千五百、
44 shanu 36,000,
牛三万六千、
45 jakuna 30,500
ろば三万五百、
46 da mutane 16,000.
人一万六千であって、
47 Daga rabin kashi na Isra’ilawa, Musa ya ɗauki ɗaya daga cikin hamsin na mutane da na dabbobi, yadda Ubangiji ya umarce shi, ya ba wa Lawiyawan da suke lura da tabanakul na Ubangiji.
モーセはイスラエルの人々の受けた半分のなかから、人および獣をおのおの五十ごとに一つを取って、主の幕屋の務をするレビびとに与えた。主がモーセに命じられたとおりである。
48 Sai shugabannin da suka shugabancin rundunar yaƙin, shugabanni na dubu-dubu da shugabanni na ɗari-ɗari, suka zo wurin Musa
時に軍勢の将であったものども、すなわち千人の長たちと百人の長たちとがモーセのところにきて、
49 suka ce masa, “Barorinka sun ƙidaya mayaƙan da suke ƙarƙashinmu, babu ko ɗayan ya ɓace.
モーセに言った、「しもべらは、指揮下のいくさびとを数えましたが、われわれのうち、ひとりも欠けた者はありませんでした。
50 Saboda haka mun kawo wa Ubangiji hadaya na kayan zinariya da kowannenmu ya samu, mundaye, ƙawane,’yan kunne da duwatsun wuya, don yin wa kanmu kafara a gaban Ubangiji.”
それで、われわれは、おのおの手に入れた金の飾り物、すなわち腕飾り、腕輪、指輪、耳輪、首飾りなどを主に携えてきて供え物とし、主の前にわれわれの命のあがないをしようと思います」。
51 Musa da Eleyazar firist, suka karɓi zinariya da kayan adon duka daga gare su.
モーセと祭司エレアザルとは、彼らから細工を施した金の飾り物を受け取った。
52 Dukan zinariya da shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, waɗanda Musa da Eleyazar suka karɓa, suka kuma miƙa hadaya ga Ubangiji, nauyinta ta kai shekel 16,750.
千人の長たちと百人の長たちとが、主にささげものとした金は合わせて一万六千七百五十シケル。
53 Kowane soja, ya kwashi ganima wa kansa.
いくさびとは、おのおの自分のぶんどり物を獲た。
54 Musa da Eleyazar firist, suka karɓi zinariya daga shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, suka kawo cikin Tentin Sujada, don su zama abin tuni ga Isra’ilawa a gaban Ubangiji.
モーセと祭司エレアザルとは、千人の長たちと百人の長たちとから、その金を受け取り、それを携えて会見の幕屋に入り、主の前に置いてイスラエルの人々のために記念とした。

< Ƙidaya 31 >