< Ƙidaya 3 >
1 Waɗannan su ne zuriyar Haruna da Musa a lokacin da Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai.
2 Sunayen’ya’yan Haruna su ne, Nadab ɗan fari, da Abihu, da Eleyazar da Itamar.
3 Waɗannan su ne sunayen’ya’yan Haruna, shafaffun firistocin da aka naɗa domin su yi aiki firist.
4 Amma Nadab da Abihu suka fāɗi suka mutu a gaban Ubangiji a Hamadar Sinai a sa’ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta a gabansa. Ba su kuwa da’ya’ya; saboda haka Eleyazar da Itamar kaɗai suka yi aiki firist a zamanin mahaifinsu Haruna.
5 Ubangiji ya ce wa Musa,
6 “Ka kawo mutanen Lawi, ka kuma gabatar da su ga Haruna firist, don su taya shi aiki.
7 Za su yi wa Haruna da dukan al’umma aikace-aikace a Tentin Sujada, ta wurin yin aikin tabanakul.
8 Za su lura da dukan kayayyakin Tentin Sujada, suna cika hakkin Isra’ilawa ta wurin yin aiki a tabanakul.
9 Ka ba da Lawiyawa ga Haruna da’ya’yansa; su ne za su zama Isra’ilawan da za a ba da su ɗungum gare shi.
10 Ka naɗa Haruna da’ya’yansa su yi aiki firistoci; duk wanda ya yi shisshigi a wuri mai tsarki kuwa dole a kashe shi.”
11 Ubangiji ya kuma ce wa Musa,
12 “Ga shi na ɗauki Lawiyawa daga cikin Isra’ilawa a maimakon ɗan fari na kowace mace a Isra’ila. Lawiyawa nawa ne,
13 gama duk’ya’yan fari nawa ne. Lokacin da karkashe duk’ya’yan fari a Masar, na keɓe wa kaina kowane ɗan fari a Isra’ila, ko mutum, ko dabba. Za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.”
14 Ubangiji ya yi magana da Musa a Hamadar Sinai ya ce,
15 “Ka ƙidaya Lawiyawa bisa ga iyalansu da kabilarsu. Ka ƙidaya kowane ɗan jinjiri mai wata ɗaya ko fiye.”
16 Saboda haka Musa ya ƙidaya su duka, kamar yadda maganar Ubangiji ta umarta.
17 Ga sunayen’ya’yan Lawi, Gershon, Kohat da Merari.
18 Ga sunayen mutanen Gershon, Libni, da Shimeyi
19 Sunayen mutanen Kohat kuwa su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
20 Dangin Merari su ne. Mali da Mushi. Ga kabilan Lawiyawa bisa ga iyalansu.
21 A wajen Gershonawa, kabilarsa su ne Libniyawa, da Shimeyiyawa; waɗannan su ne mutanen Gershom.
22 Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya zuwa gaba da haihuwa su kai 7,500.
23 Kabilar Gershonawa za su yi sansani ta fuskar yamma, a bayan tabanakul.
24 Eliyasaf ɗan Layel shi ne shugaban iyalan Gershonawa.
25 A Tentin Sujada, Gershonawa su ne za su lura da mazauni da tabanakul da kuma tentin, abubuwan rufensa, labule a ƙofar Tentin Sujada,
26 da labulen filin da yake kewaye da tabanakul da kuma bagade, da igiyoyi, da kuma kowane abin da ya danganci aikinsu.
27 Kabilar Kohat su ne, Amramawa da Izharawa da Hebronawa da Uzziyelawa; waɗannan su ne kabilar Kohatawa.
28 Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 8,600 ne. Kohatawa ne suke lura da wuri mai tsarki.
29 Kohatawa za su yi sansani a kudu da tabanakul.
30 Shugaban kabilar Kohatawa shi ne Elizafan ɗan Uzziyel.
31 Su ne da hakkin kula da akwatin alkawari, tebur, wurin ajiye fitila, bagade, kayayyakin wuri mai tsarki da ake amfani da su a sujada, labule, da kuma kome da ya danganci aikinsu.
32 Babban shugaban Lawiyawa shi ne Eleyazar ɗan Haruna, firist. An naɗa shi a kan waɗanda suke kula da wuri mai tsarki.
33 Kabilar Merari su ne Maliyawa da Mushiyawa; waɗannan su ne kabilar Merari.
34 Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 6,200 ne.
35 Shugaban iyalan Merari shi ne Zuriyel ɗan Abihayil. Za su yi sansani arewa da tabanakul.
36 Kabilar Merari ne aka sa su lura da katakan tabanakul, sandunanta, dogayen sandunanta, tarukanta, dukan kayan aiki da kowane abin da ya danganci aikinsu,
37 da ginshiƙai kewaye da filin tare da rammuka da turaku da igiyoyinsu.
38 Musa da Haruna da’ya’yansu za su yi sansani gabas da tabanakul, wajen fitowar rana; a gaban Tentin Sujada. Su ne da hakkin lura da wuri mai tsarki a madadin Isra’ilawa. Duk wani wanda ba ya wannan aiki, ya kuma kusaci wuri mai tsarki, za a kashe shi.
39 Jimillar Lawiyawan da Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga umarnin Ubangiji bisa ga danginsu, haɗe da kowane jariri daga wata ɗaya ko fiye, 22,000 ne.
40 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ƙidaya dukan’ya’yan fari na Isra’ilawa maza daga wata ɗaya da kuma fiye ka kuma rubuta sunayensu.
41 Ka ɗauko mini Lawiyawa a maimakon dukan’ya’yan fari na Isra’ilawa, haka ma na dabbobi na Lawiyawa, a maimakon’ya’yan fari na dabbobin Isra’ilawa. Ni ne Ubangiji.”
42 Haka Musa ya ƙidaya’ya’yan fari na Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya umarce shi.
43 Jimillar’ya’yan fari maza daga wata ɗaya da kuma fiye, da aka rubuta bisa ga sunayensu, 22,273 ne.
44 Sai Ubangiji ya kuma yi magana da Musa ya ce,
45 “Ka ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan’ya’yan fari na Isra’ila, dabbobin Lawiyawa kuma a maimakon dabbobinsu. Lawiyawa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.
46 Don a fanshi’ya’yan fari 273 na Isra’ilawa da suka fi Lawiyawa yawa,
47 ka karɓi shekel biyar domin kowannensu, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda yake da nauyin gera ashirin.
48 Ka ba wa Haruna da’ya’yansa kuɗin fansar da ya haura kai na’ya’yan farin Isra’ilawa.”
49 Haka, Musa ya karɓi kuɗin fansar waɗanda suka haura yawan Lawiyawa.
50 Daga’ya’yan fari na Isra’ilawa, ya karɓi azurfa masu nauyin shekel 1,365, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.
51 Sa’an nan Musa ya ba da kuɗin fansar ga Haruna da’ya’yansa, yadda maganar Ubangiji ta umarce shi.