< Ƙidaya 26 >
1 Bayan annobar, sai Ubangiji ya yi magana da Musa da Eleyazar ɗan Haruna, firist ya ce,
2 “Ku ƙidaya dukan jama’ar Isra’ila daga mai shekaru ashirin zuwa gaba da za su iya aikin sojan Isra’ila.”
3 Musa da Eleyazar firist suka yi musu magana a filayen Mowab kusa da Urdun daga ƙetaren Yeriko, suka ce,
4 “Ku ƙidaya maza daga mai shekara ashirin zuwa gaba yadda Ubangiji ya umarci Musa.” Waɗannan su ne Isra’ilawan da suka fito daga Masar.
5 Zuriyar Ruben ɗan fari na Isra’ila, daga Hanok; kabilar Hanokawa; daga Fallu; kabilar Falluyawa;
6 daga Hezron, kabilar Hezronawa; daga Karmi, kabilar Karmiyawa.
7 Waɗannan su ne kabilan Ruben; jimillarsu ta kai 43,730.
8 Ɗan Fallu kuwa shi ne Eliyab,
9 ’ya’yan Eliyab maza kuwa su ne, Nemuwel, Datan da Abiram. Datan da Abiram nan, su ne shugabannin mutanen da suka tayar wa Musa da Haruna, suna kuma cikin waɗanda suka bi Kora sa’ad da ya tayar wa Ubangiji.
10 Ƙasa kuwa ta buɗe ta haɗiye su tare da Kora, wanda ƙungiyarsa ta mutu sa’ad da wuta ta cinye mutum 250. Wannan kuwa ya zama alamar faɗakarwa.
11 Amma fa, zuriyar Kora ba tă mutu ba.
12 Zuriyar Simeyon bisa ga kabilansu, daga Nemuwel, kabilar Nemuwelawa; daga Yamin, kabilar Yaminawa; daga Yakin, kabilar Yakinawa;
13 daga Zera, kabilar Zerawa; daga Sha’ul, kabilar Sha’ul.
14 Waɗannan su ne kabilan Simeyon; jimillarsu ta kai 22,200.
15 Zuriyar Gad bisa ga kabilansu, daga Zafon, kabilar Zafonawa; daga Haggi, kabilar Haggiwa; daga Shuni, kabilar Shunawa;
16 daga Ozni, kabilar Ozniyawa daga Eri, kabilar Eriyawa;
17 daga Arod, kabilar Arodiyawa; daga Areli, kabilar Areliyawa.
18 Waɗannan su ne kabilan Gad, jimillarsu ta kai 40,500.
19 Er da Onan,’ya’yan Yahuda ne, amma sun mutu a Kan’ana.
20 Zuriyar Yahuda bisa ga kabilansu, daga Shela, kabilar Shelayawa daga Ferez, kabilar Ferezawa; daga Zera, kabilar Zerawa;
21 Zuriyar Ferez kuwa, daga Hezron, kabilar Hezronawa; daga Hamul; kabilar Hamulawa.
22 Waɗannan su ne kabilan Yahuda; jimillarsu ta kai 76,500.
23 Zuriyar Issakar bisa ga kabilansu, daga Tola, kabilar Tolatawa; daga Fuwa, kabilar Fuwayawa;
24 daga Yashub, kabilar Yashubawa; daga Shimron, kabilar Shimronawa.
25 Waɗannan su ne kabilan Issakar; jimillarsu ta kai 64,300.
26 Zuriyar Zebulun bisa ga kabilansu, daga Sered, kabilar Seredawa; daga Elon kabilar Elonawa; daga Yaleyel; kabilar Yaleyewa.
27 Waɗannan su ne kabilan Zebulun, jimillarsu ta kai 60,500.
28 Zuriyar Yusuf bisa ga kabilansu ta wurin Manasse da Efraim.
29 Zuriyar Manasse, daga Makir, kabilar Makiriyawa (Makir shi ne mahaifin Gileyad); daga Gileyad, kabilar Gileyadawa.
30 Waɗannan su ne zuriya Gileyad, daga Iyezer, kabilar Iyezerawa; daga Helek, kabilar Helekawa;
31 daga Asriyel, kabilar Asriyelawa; daga Shekem, kabilar Shekem;
32 daga Shemida, kabilar Shemadawa; daga Hefer, kabilar Heferawa.
33 (Zelofehad ɗan Hefer, ba shi da’ya’ya maza;’yan mata ne kaɗai ya haifa, sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza.)
34 Waɗannan su ne kabilan Manasse, jimillarsu ta kai 52,700.
35 Waɗannan su ne kabilan Efraim bisa ga kabilansu, daga Shutela, kabilar Shutelawa; daga Beker, kabilar Bekerawa; daga Tahan, kabilar Tahanawa.
36 Waɗannan su ne kabilan Shutelawa, daga Eran, kabilar Eranawa.
37 Waɗannan su ne kabilan Efraim; jimillarsu ta kai 32,500. Waɗannan su ne kabilan Yusuf ta wurin kabilansu.
38 Zuriyar Benyamin bisa ga kabilansu, daga Bela, kabilar Belawa; daga Ashbel, kabilar Ashbelawa; daga Ahiram, kabilar Ahiramawa;
39 daga Shufam, kabilar Shufamawa; daga Hufam, kabilar Hufamawa.
40 Zuriyar Bela daga Ard da Na’aman, daga Ard, kabilar Ardawa; daga Na’aman, kabilar Na’amawa;
41 Waɗannan su ne kabilan Benyamin, jimillarsu ta kai 45,600.
42 Waɗannan su ne kabilan Dan bisa ga kabilarsu, daga Shuham, kabilar Shuhamawa. Waɗannan su ne kabilan Dan.
43 Dukansu kabilan Shuhamawa ne, jimillarsu ta kai 64,400.
44 Zuriyar Asher bisa ga kabilansu, daga Imna, kabilar Imnawa daga Ishbi, kabilar Ishbiyawa; daga Beriya, kabilar Beriyawa;
45 daga zuriyar Beriya kuwa, daga Heber, kabilar Heberawa; daga Malkiyel, kabilar Malkiyelawa.
46 (Asher yana da’ya mace da ake kira Sera.)
47 Waɗannan su ne kabilan Asher; jimillarsu ta kai 53,400.
48 Zuriyar Naftali bisa ga kabilansu, daga Yazeyel, kabilar Yazeyelawa; daga Guni, kabilar Guniyawa;
49 daga Yezer, kabilar Yezerawa; daga Shillem, kabilar Shillemawa.
50 Waɗannan su ne kabilan Naftali, jimillarsu ta kai 45,400.
51 Dukan jimillar mazan Isra’ila ta kai 601,730.
52 Ubangiji ya ce wa Musa,
53 “Ka rarraba musu ƙasar a matsayin gādo, bisa ga yawan kabila.
54 Ga ƙungiya mafi girma, ka ba ta rabo mafi girma; ga ƙaramar ƙungiya kuwa, ka ba ta ƙarami rabo; kowane zai karɓa rabonsa ga yawan mutanen da aka rubuta.
55 Ka tabbatar an rarraba ƙasar ta wurin rabo. Abin da kowace ƙungiya ta gāda zai zama bisa ga sunayen kabilar kakanninta.
56 Za a raba kowane gādo bisa ga rabo tsakanin manyan da ƙanana ƙungiyoyi.”
57 Waɗannan su ne Lawiyawa da a ƙidaya bisa ga kabilansu, daga Gershom, kabilar Gershonawa; daga Kohat, kabilar Kohatawa; daga Merari, kabilar Merari.
58 Waɗannan kuma su ne kabilan Lawiyawa, kabilar Libniyawa, kabilar Hebronawa, kabilar Maliyawa, kabilar Mushiyawa, kabilar Korayawa (Kohat shi ne kakan Amram;
59 sunan matan Amram shi ne Yokebed, ita zuriyar Lawi ce, wadda aka haifa wa Lawiyawa a Masar. A wajen Amram kuwa ta haifi Haruna, Musa da kuma’yar’uwarsu Miriyam.
60 Haruna shi ne mahaifin Nadab, Abihu, Eleyazar da kuma Itamar.
61 Amma Nadab da Abihu sun mutu sa’ad da suka miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji.)
62 Dukan’ya’yan Lawiyawa maza daga wata ɗaya zuwa gaba, jimillarsu ta kai 23,000. Ba a ƙidaya su tare da sauran Isra’ilawa ba, domin ba a ba su gādo tare da su ba.
63 Waɗannan su ne waɗanda Musa da Eleyazar firist, suka ƙidaya sa’ad da suka ƙidaya Isra’ilawa a filaye Mowab kusa da Urdun a hayen Yeriko.
64 Ba ko ɗayansu da yake cikin waɗanda Musa da Haruna firist, suka ƙidaya sa’ad da suka ƙidaya Isra’ilawa a Hamadar Sinai.
65 Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa waɗancan Isra’ilawa cewa lalle za su mutu a hamada, kuma ba ko ɗayansu da ya rage, sai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.