< Ƙidaya 25 >
1 Lokacin da Isra’ila suke a sansani a Shittim, sai maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa,
以色列人住在什亭,百姓與摩押女子行起淫亂。
2 waɗanda suka gayyace su zuwa wajen hadayu na allolinsu. Mutane suka ci suka kuma yi wa waɗannan alloli sujada.
因為這女子叫百姓來,一同給她們的神獻祭,百姓就吃她們的祭物,跪拜她們的神。
3 Ta haka Isra’ila suka sa kai a bautar gumaka Ba’al-Feyor. Ubangiji kuwa ya husata da su.
以色列人與巴力‧毗珥連合,耶和華的怒氣就向以色列人發作。
4 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kama dukan shugabannin mutanen nan, ka kashe su, ka kuma bar su a tsakar rana a gaban Ubangiji, don Ubangiji yă huce daga fushin da nake yi da Isra’ila.”
耶和華吩咐摩西說:「將百姓中所有的族長在我面前對着日頭懸掛,使我向以色列人所發的怒氣可以消了。」
5 Saboda haka Musa ya ce wa alƙalan Isra’ila, “Dole kowannenku yă kashe mutanen nan da suka haɗa kai cikin bautar Ba’al-Feyor.”
於是摩西吩咐以色列的審判官說:「凡屬你們的人,有與巴力‧毗珥連合的,你們各人要把他們殺了。」
6 Sa’an nan wani mutumin Isra’ila ya kawo wata Bamidiyana a iyalinsa a idon Musa da dukan taron jama’ar Isra’ila, yayinda suke kuka a ƙofar Tentin Sujada.
摩西和以色列全會眾正在會幕門前哭泣的時候,誰知,有以色列中的一個人,當他們眼前,帶着一個米甸女人到他弟兄那裏去。
7 Da Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya ga haka, sai ya bar taron, ya ɗauki māshi
祭司亞倫的孫子,以利亞撒的兒子非尼哈看見了,就從會中起來,手裏拿着槍,
8 ya bi mutumin Isra’ilan nan cikin tenti, ya soke dukansu biyu, māshin ya ratsa jikin mutumin Isra’ilan har zuwa jikin macen. Sa’an nan aka tsai da annoban nan a kan Isra’ilawa.
跟隨那以色列人進亭子裏去,便將以色列人和那女人由腹中刺透。這樣,在以色列人中瘟疫就止息了。
9 Waɗanda suka mutu a wannan annoba, sun kai mutum 24,000.
那時遭瘟疫死的,有二萬四千人。
10 Ubangiji ya ce wa Musa,
耶和華曉諭摩西說:
11 “Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya kawar da fushina daga Isra’ilawa; saboda ya yi kishi irin nawa a gabansu, don haka saboda ɗaukakata ban kawo ƙarshensu ba.
「祭司亞倫的孫子,以利亞撒的兒子非尼哈,使我向以色列人所發的怒消了;因他在他們中間,以我的忌邪為心,使我不在忌邪中把他們除滅。
12 Saboda haka ka faɗa masa cewa zan yi alkawarin salama da shi.
因此,你要說:『我將我平安的約賜給他。
13 Shi da zuriyarsa za su kasance da alkawari na zama firist har abada, saboda kishinsa domin ɗaukakar Allahnsa, ya kuma yi kafara domin Isra’ilawa.”
這約要給他和他的後裔,作為永遠當祭司職任的約;因他為上帝有忌邪的心,為以色列人贖罪。』」
14 Sunan mutumin Isra’ilan da aka kashe tare da macen nan Bamidiyana kuwa Zimri ne, ɗan Salu, shugaban mutanen Simeyon.
那與米甸女人一同被殺的以色列人,名叫心利,是撒路的兒子,是西緬一個宗族的首領。
15 Sunan macen nan Bamidiyana da aka kashe kuwa Kozbi ne,’yar Zur, wani basaraken iyalin Midiyawa.
那被殺的米甸女人,名叫哥斯比,是蘇珥的女兒;這蘇珥是米甸一個宗族的首領。
16 Ubangiji ya ce wa Musa,
耶和華曉諭摩西說:
17 “Ka ɗauki Midiyawa a matsayin abokan gāba, ka kuma kashe su,
「你要擾害米甸人,擊殺他們;
18 gama sun ɗauke ku a matsayin abokan gāba, sa’ad da suka ruɗe ku a kan al’amuran Feyor da’yar’uwarsu Kozbi’yar shugaban Midiyawa, macen da aka kashe a annoba ta dalili Feyor.”
因為他們用詭計擾害你們,在毗珥的事上和他們的姊妹、米甸首領的女兒哥斯比的事上,用這詭計誘惑了你們;這哥斯比,當瘟疫流行的日子,因毗珥的事被殺了。」