< Ƙidaya 24 >
1 To, da Bala’am ya ga cewa Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra’ila albarka, bai koma wajen sihiri kamar dā ba, amma ya juya fuskarsa wajen hamada.
Als nun Bileam sah, daß es dem HERRN gefiel, Israel zu segnen, ging er nicht, wie zuvor, nach Wahrsagung aus, sondern richtete sein Angesicht gegen die Wüste.
2 Da Bala’am ya duba sai ya ga Isra’ila sun yi sansani kabila, kabila, Ruhun Allah kuwa ya sauko masa,
Und Bileam hob seine Augen auf und sah Israel, wie es nach seinen Stämmen lagerte. Und der Geist Gottes kam auf ihn.
3 sai ya yi annabcinsa ya ce, “Maganar Bala’am ɗan Beyor, saƙon mutumin da idanunsa ke gani sarai,
Und er hob an seinen Spruch und sprach: Es sagt Bileam, der Sohn Beors, es sagt der Mann, dem das Auge erschlossen ist, es sagt der Hörer göttlicher Reden,
4 maganar mutumin da ya saurari maganar Allah, maganar wanda yake ganin wahayi daga Maɗaukaki, mutumin da ya fāɗi rubda ciki, wanda kuma idanunsa suna a buɗe.
der des Allmächtigen Gesichte sieht, welcher niederfällt, und dem die Augen geöffnet werden:
5 “Ina misalin kyan tentunanka, ya Yaƙub, wuraren zamanka, ya Isra’ila!
Wie schön sind deine Hütten, o Jakob, und deine Wohnungen, o Israel!
6 “Kamar kwaruruka suke a shimfiɗe, kamar lambu kusa da rafi, kamar itatuwan aloyes da Ubangiji ya dasa, kamar itatuwa al’ul kusa da ruwaye.
Wie die Täler, die sich ausbreiten, wie die Gärten am Strom, wie Aloe, die der HERR gepflanzt hat, wie die Zedern am Wasser.
7 Ruwa zai kwararo daga bokitinsu; irinsu za su sami ruwa a yalwace. “Sarkinsu zai fi sarkin Agag; mulkinsu zai ɗaukaka.
Wasser wird aus seinen Eimern fließen, und sein Same wird sein in großen Wassern. Sein König wird höher werden als Agag, und sein Reich wird sich erheben.
8 “Allah ya fitar da su daga Masar; suna da ƙarfin kutunkun ɓauna. Sun cinye abokan gāban, suka kakkarya ƙasusuwansu; da kibiyoyinsu suka sossoke su.
Gott hat ihn aus Ägypten geführt, seine Kraft ist wie die eines Büffels. Er wird die Heiden, seine Widersacher, fressen und ihre Gebeine zermalmen und mit seinen Pfeilen niederstrecken.
9 Kamar zaki sun laɓe sun kwanta, kamar zakanya, wa zai yi ƙarfin hali yă tashe su? “Bari waɗanda suka albarkace ka, su sami albarka waɗanda kuma suka la’anta ka, su la’antu!”
Er ist niedergekniet, er hat sich niedergelegt wie ein Löwe und wie eine Löwin. Wer will ihn aufwecken? Gesegnet sei, wer dich segnet, und verflucht, wer dir flucht!
10 Fushin Balak ya ƙuna a kan Bala’am. Ya tafa hannunsa, ya ce masa, “Na kira ka don ka la’anta abokan gābana, amma sai ga shi ka sa musu albarka har sau uku.
Da ergrimmte Balak im Zorn wider Bileam und schlug die Hände ineinander; und Balak sprach zu Bileam: Ich habe dich gerufen, daß du meinen Feinden fluchest, und siehe, du hast sie nun dreimal gesegnet!
11 Yanzu ka bar nan ka tafi gida! Na ce zan sāka maka da lada mai kyau, amma Ubangiji ya hana ka samun ladan.”
Und nun mach dich fort an deinen Ort! Ich gedachte dich hoch zu ehren; aber siehe, der HERR hat dir die Ehre versagt!
12 Bala’am ya ce wa Balak, “Ban faɗa wa’yan aikan da ka aiko wurina ba cewa,
Bileam antwortete dem Balak: Habe ich nicht auch zu deinen Boten, die du mir sandtest, gesagt und gesprochen:
13 ‘Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba, kuma dole in faɗa abin da Ubangiji ya ce ne kawai’?
Wenn mir Balak sein Haus voll Silber und Gold gäbe, so könnte ich doch das Gebot des HERRN nicht übertreten, Böses oder Gutes zu tun nach meinem Herzen; sondern was der HERR reden werde, das werde ich auch reden?
14 Yanzu zan koma wajen mutanena, amma bari in gargaɗe ka game da abin da mutanen nan za su yi wa mutanenka cikin kwanaki masu zuwa.”
Und nun siehe, da ich zu meinem Volk ziehe, so komm, ich will dir sagen, was dieses Volk deinem Volk in spätern Tagen tun wird!
15 Sa’an nan ya furta saƙonsa. “Maganar Bala’am ɗan Beyor, saƙon mutumin da idanunsa ke gani sarai,
Und er hob an seinen Spruch und sprach: Es sagt Bileam, der Sohn Beors, es sagt der Mann, dem das Auge erschlossen ist,
16 maganar mutumin da ya saurari maganar Allah, wanda yake da sani daga Mafi Ɗaukaka, wanda yake ganin wahayi daga Maɗaukaki, wanda ya fāɗi rubda ciki, wanda kuma idanunsa suna a buɗe.
es sagt der Hörer göttlicher Reden, und der die Erkenntnis des Höchsten hat, der die Gesichte des Allmächtigen sieht und niederfällt, und dem die Augen geöffnet werden:
17 “Na gan shi, amma ba yanzu ba; na hange shi, amma ba kusa ba. Tauraro zai fito daga Yaƙub; sandan mulki zai fito daga Isra’ila. Zai ragargaje goshin Mowab, kawunan dukan’ya’yan Set.
Ich sehe ihn, aber jetzt noch nicht; ich schaue ihn, aber noch nicht in der Nähe. Ein Stern tritt aus Jakob hervor, und ein Zepter kommt aus Israel. Er schlägt Moab auf beide Seiten und alle Kinder Set aufs Haupt.
18 Za a ci Edom da yaƙi; za a ci Seyir, abokiyar gābanta, amma Isra’ila zai ƙara ƙarfi.
Edom wird seine Besitzung, und Seir zum Besitztum seiner Feinde; Israel aber wird tapfere Taten tun.
19 Mai mulki zai fito daga Yaƙub yă hallaka waɗanda suka ragu a birnin.”
Von Jakob wird der ausgehen, der herrschen wird, und er wird umbringen, was von den Städten übrig ist.
20 Sai Bala’am ya ga Amalek, ya kuma furta maganarsa. “Amalek yana cikin al’ummai na fari, amma zai zama na ƙarshen da za a hallaka.”
Und als er Amalek sah, hob er an seinen Spruch und sprach: Amalek ist der Erstling der Heiden, und zuletzt wird er untergehen.
21 Sai ya ga Keniyawa, ya kuma furta maganarsa. “Wurin zamanku lafiya yake, an kuma sa sheƙarku a cikin duwatsu;
Und als er die Keniter sah, hob er an seinen Spruch und sprach: Deine Wohnung ist fest, und du hast dein Nest in einen Felsen gelegt;
22 duk da haka, za a hallaka ku Keniyawa sa’ad da Asshur ya kame ku.”
aber du wirst, o Kain, verwüstet werden! Wie lange geht es noch, bis dich Assur gefangen nimmt?
23 Sai ya furta maganarsa ya ce, “Wayyo, wa zai rayu sa’ad da Allah ya yi haka?
Und er hob abermal seinen Spruch an und sprach: Wehe! wer wird leben, wenn Gott solches erfüllt?
24 Jiragen ruwa za su zo daga Kittim; za su murƙushe Asshur da Eber, amma su ma za a hallaka su.”
Und Schiffe aus Kittim werden Assur bezwingen und werden auch den Heber bezwingen; und auch er wird untergehen!
25 Sa’an nan Bala’am ya tashi ya koma gidan, Balak kuma ya yi tafiyarsa.
Darnach machte sich Bileam auf und ging und kehrte an seinen Ort zurück; und Balak ging auch seines Weges.