< Ƙidaya 22 >
1 Sai Isra’ilawa suka kama hanya, suka tafi filayen Mowab, a wajen Urdun, a ƙetare Yeriko, suka yi sansani a can.
2 To, fa, Balak ɗan Ziffor ya ga duk abin da Isra’ila suka yi da Amoriyawa.
3 Sai Mowab ya firgita ƙwarai saboda yawan mutanen. Tsoron Isra’ilawa ya kama su.
4 Sai Mowabawa suka ce wa dattawan Midiyawa, “Wannan taron zai lashe duk abin da ya kewaye mu kamar yadda saniya takan lashe ciyawa a fili.” Saboda haka Balak ɗan Ziffor, wanda yake sarkin Mowab a lokacin,
5 ya aika manzanni su zo da Bala’am ɗan Beyor, wanda yake a Fetor, kusa da Kogi, a ƙasar haihuwarsa. Balak ya ce, “Ga mutane sun fito daga Masar; sun mamaye ƙasar, suka kuma yi sansani kusa da ni.
6 Ka zo yanzu ka la’anta waɗannan mutane, domin sun fi ƙarfina. Wataƙila zan iya cin nasara a kansu, in kuma kore su daga ƙasar. Gama na sani duk waɗanda ka sa musu albarka, sun zama masu albarka ke nan, waɗanda kuma ka la’anta, sun la’antu ke nan.”
7 Sai dattawan Mowab da na Midiyawa suka tashi, suka ɗauki kuɗi don duba. Da suka zo wurin Bala’am sai suka faɗa masa abin da Balak ya ce.
8 Bala’am ya ce musu, “Ku kwana a nan, ni kuwa zan faɗa muku abin da Ubangiji ya faɗa mini.” Saboda haka dattawan sarkin Mowab suka zauna da shi.
9 Sai Allah ya zo wurin Bala’am ya ce, “Su wane ne waɗannan tare da kai?”
10 Bala’am ya ce wa Allah, “Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab ne, ya aiko mini wannan saƙo cewa,
11 ‘Ga mutane sun fito daga Masar sun mamaye ƙasar. Ka zo yanzu ka la’anta mini su. Wataƙila ta haka zan yi nasara a kansu, in kuma kore su.’”
12 Amma Allah ya ce wa Bala’am, “Kada ka tafi tare da su. Kada ka la’anta mutanen nan, gama su masu albarka ne.”
13 Kashegari Bala’am ya tashi ya ce wa dattawan Balak, “Ku koma ƙasarku, domin Ubangiji ya hana ni in tafi tare da ku.”
14 Saboda haka dattawan Mowab suka koma wurin Balak suka ce, “Bala’am ya ƙi yă zo tare da mu.”
15 Sai Balak ya aika waɗansu dattawa masu yawa, masu daraja kuma fiye da na dā.
16 Suka zo wurin Bala’am suka ce, “Ga abin da Balak ɗan Ziffor ya ce, Kada ka bar wani abu yă hana ka zuwa wurina,
17 gama zan ba ka lada mai yawa in kuma yi duk abin da ka ce. Ka zo ka la’anta mini waɗannan mutane.”
18 Amma Bala’am ya amsa musu ya ce, “Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba.
19 To, fa, sai ku kwana a nan kamar yadda waɗancan suka yi, ni kuma in roƙi Ubangiji, in ji, wace magana zai ce mini.”
20 A wannan dare, Allah ya zo wurin Bala’am ya ce, “Da yake waɗannan mutane sun zo su tafi da kai, to, ka tafi tare da su, sai dai ka yi abin da na ce ka yi ne kaɗai.”
21 Bala’am ya tashi da safe, ya ɗaura wa jakarsa sirdi, ya tafi tare da dattawan Mowab.
22 Amma Allah ya husata sa’ad da ya tafi, mala’ikan Ubangiji kuwa ya tsaya a hanya don yă hana shi. Bala’am kuwa yana kan jakarsa tare da bayinsa biyu.
23 Da jakar ta hangi mala’ikan Ubangiji tsaye a hanya da takobi a hannunsa, sai ta kauce daga hanya, ta shiga jeji. Bala’am kuwa ya buge ta don tă koma hanya.
24 Sai mala’ikan Ubangiji ya tsaya a wata matsattsiyar hanya tsakanin gonaki inabi biyu, da bango a kowane gefe.
25 Sa’ad da jakar ta ga mala’ikan Ubangiji, sai ta matse a jikin bango, ta goge ƙafar Bala’am da bangon. Saboda haka sai Bala’am ya sāke bugunta.
26 Sai mala’ikan Ubangiji ya sha gabansa, ya tsaya a ƙunƙuntaccen wuri inda ba wurin juyawa dama ko hagu.
27 Da jakar ta ga mala’ikan Ubangiji, sai ta kwanta a ƙasa, Bala’am kuwa ya husata, sai ya buge ta da sandansa.
28 Ubangiji ya buɗe bakin jakar, sai jakar ta ce wa Bala’am, “Me na yi maka da ka buge ni har sau uku?”
29 Bala’am ya ce wa jakar “Domin kin wulaƙanta ni! Da a ce ina da takobi a hannuna da zan kashe ki nan take.”
30 Jakar ta ce wa Bala’am, “Ni ba jakarka ba ce wadda kake hawa kullum, har yă zuwa yau? Na taɓa yin maka haka?” Bala’am ya ce, “A’a.”
31 Sa’an nan Ubangiji ya buɗe idanun Bala’am, ya kuwa ga mala’ikan Ubangiji tsaye a hanya da takobi a zāre. Sai ya sunkuyar da kansa, ya fāɗi rubda ciki.
32 Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya tambaye shi, “Don me ka buge jakarka har sau uku? Na fito ne don in hana ka, gama hanyarka ba daidai ba ce a gabana.
33 Jakar ta gan ni, ta kauce mini har sau uku. Da a ce ba tă kauce ba, lalle da na kashe ka, in kuwa bar ta da rai.”
34 Bala’am ya ce wa mala’ikan Ubangiji, “Na yi zunubi. Ban san ka tsaya a hanya don ka hana ni ba. Yanzu in ba ka ji daɗin tafiyata, sai in koma.”
35 Mala’ikan Ubangiji ya ce wa Bala’am, “Ka tafi tare da mutanen, amma abin da na faɗa maka ne kaɗai za ka faɗa.” Saboda haka Bala’am ya tafi tare da dattawan Balak.
36 Da Balak ya ji cewa Bala’am yana zuwa, sai ya fito, ya tarye shi a garin Mowabawa da suke a iyakar Arnon, a ƙarshen yankinsa.
37 Balak ya ce wa Bala’am, “Ban aika maka saƙo cikin gagawa ba? Me ya sa ba ka zo ba? Ko ban isa in sāka maka ba ne?”
38 Bala’am ya amsa ya ce, “To, ai, ga shi, na zo yanzu. Ina da wani ikon yin wata magana ne? Dole in faɗa abin da Allah ya ce in faɗa ne kawai.”
39 Sa’an nan Bala’am ya tafi tare da Balak zuwa Kiriyat-Huzot,
40 a can ya yi hadaya da shanu da tumaki, ya kuwa aika wa Bala’am da dattawan da suke tare da shi.
41 Kashegari, Balak ya ɗauki Bala’am ya kai shi kan Bamot Ba’al, daga can ya iya ganin sassan sansanin Isra’ilawa.