< Ƙidaya 21 >

1 Sa’ad da sarkin Arad, mutumin Kan’ana, wanda yake zaune a Negeb, da ya ji cewa Isra’ila yana zuwa ta hanyar Atarim, sai ya fito, yă yaƙi Isra’ilawa, yă kuma kama waɗansunsu.
住南地的迦南人亞拉得王,聽說以色列人從亞他林路來,就和以色列人爭戰,擄了他們幾個人。
2 Sai Isra’ila suka yi alkawari wa Ubangiji suka ce, “In ka ba da waɗannan mutane a hannunmu, za mu hallaka dukan garuruwansu ƙaf.”
以色列人向耶和華發願說:「你若將這民交付我手,我就把他們的城邑盡行毀滅。」
3 Ubangiji kuwa ya saurari kukan Isra’ila, ya kuma ba da Kan’aniyawa a gare su. Suka hallaka su da biranensu ƙaf; saboda haka aka sa wa wurin suna Horma.
耶和華應允了以色列人,把迦南人交付他們,他們就把迦南人和迦南人的城邑盡行毀滅。那地方的名便叫何珥瑪。
4 Suka kama hanya daga Dutsen Hor ta hanya zuwa Jan Teku, don su kauce wa Edom. Amma mutane suka rasa haƙuri a hanya;
他們從何珥山起行,往紅海那條路走,要繞過以東地。百姓因這路難行,心中甚是煩躁,
5 suka yi wa Allah da Musa gunaguni, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu mu mutu a wannan hamada? Babu abinci! Babu ruwa! Mu dai mun gaji da wannan abinci marar amfani!”
就怨讟上帝和摩西說:「你們為甚麼把我們從埃及領出來、使我們死在曠野呢?這裏沒有糧,沒有水,我們的心厭惡這淡薄的食物。」
6 Sai Ubangiji ya aiko da macizai masu dafin a cikinsu, suka sassari mutane, Isra’ilawa masu yawa kuwa suka mutu.
於是耶和華使火蛇進入百姓中間,蛇就咬他們。以色列人中死了許多。
7 Mutanen suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi, da muka yi wa Ubangiji da kai gunaguni. Ka yi addu’a don Ubangiji yă ɗauke mana macizan nan.” Saboda haka Musa ya yi addu’a domin mutane.
百姓到摩西那裏,說:「我們怨讟耶和華和你,有罪了。求你禱告耶和華,叫這些蛇離開我們。」於是摩西為百姓禱告。
8 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera siffar maciji ka rataye shi a bisa doguwar sanda; kowa da maciji ya sare shi, idan ya dubi macijin nan da ka rataye, zai rayu.”
耶和華對摩西說:「你製造一條火蛇,掛在杆子上;凡被咬的,一望這蛇,就必得活。」
9 Saboda haka Musa ya ƙera macijin tagulla, ya kuma rataye shi bisa doguwar sanda. Sa’an nan duk wanda maciji ya sare shi, ya kuma dubi macijin tagullar, zai warke.
摩西便製造一條銅蛇,掛在杆子上;凡被蛇咬的,一望這銅蛇就活了。
10 Isra’ilawa suka kama hanya, suka yi sansani a Obot.
以色列人起行,安營在阿伯。
11 Sai suka tashi daga Obot, suka yi sansani a Iye Abarim a hamadar da take fuskantar Mowab, wajen fitowar rana.
又從阿伯起行,安營在以耶‧亞巴琳,與摩押相對的曠野,向日出之地。
12 Daga nan kuma suka ci gaba, suka yi sansani a Kwarin Zered.
從那裏起行,安營在撒烈谷。
13 Suka tashi daga nan, suka sauka kusa da Arnon wanda yake a hamadar da ta miƙe zuwa iyakar Amoriyawa. Arnon shi ne iyakar Mowab, wanda yake tsakanin Mowab da Amoriyawa.
從那裏起行,安營在亞嫩河那邊。這亞嫩河是在曠野,從亞摩利的境界流出來的;原來亞嫩河是摩押的邊界,在摩押和亞摩利人搭界的地方。
14 Shi ya sa Littafin Yaƙoƙin Ubangiji ya ce, “Waheb ta cikin yankin Sufa, da kwaruruka na tuddan Arnon,
所以耶和華的戰記上說:「蘇法的哇哈伯與亞嫩河的谷,
15 da gangaren kwaruruka, wanda ya nausa zuwa garin Ar, ya kuma dangana da kan iyakar Mowab.”
並向亞珥城眾谷的下坡,是靠近摩押的境界。」
16 Daga can, suka gangara zuwa Beyer, wato, rijiyar da Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattara mutane duka, zan kuwa ba su ruwa.”
以色列人從那裏起行,到了比珥。從前耶和華吩咐摩西說:「招聚百姓,我好給他們水喝」,說的就是這井。
17 Sai Isra’ilawa suka rera wannan waƙa, “Ki ɓuɓɓugo da ruwa, Ke rijiya! Rera waƙa game da ita,
當時,以色列人唱歌說: 井啊,湧上水來! 你們要向這井歌唱。
18 game da rijiyar da’ya’yan sarki suka haƙa, rijiyar da manyan mutane masu sandunan sarauta suka nuna da sandunansu.” Sa’an nan suka tashi daga hamadar, suka tafi Mattana,
這井是首領和民中的尊貴人 用圭用杖所挖所掘的。 以色列人從曠野往瑪他拿去,
19 daga Mattana, suka tafi Nahaliyel, daga Nahaliyel, suka tafi Bamot,
從瑪他拿到拿哈列,從拿哈列到巴末,
20 daga Bamot kuma suka tafi kwarin da yake cikin Mowab inda ƙwanƙolin Fisga yake fuskantar hamada.
從巴末到摩押地的谷,又到那下望曠野之毗斯迦的山頂。
21 Isra’ila suka aiki manzanni wurin Sihon sarkin Amoriyawa su ce,
以色列人差遣使者去見亞摩利人的王西宏,說:
22 “Ka bari mu ratsa ta ƙasarka. Ba za mu shiga wata gona ba, ba za mu kuma shiga gonar inabi, ko mu sha ruwa daga wata rijiya ba. Za mu bi ta babbar hanyar sarki, har mu fita ƙasarka.”
「求你容我們從你的地經過;我們不偏入田間和葡萄園,也不喝井裏的水,只走大道,直到過了你的境界。」
23 Amma Sihon bai bar Isra’ila su ratsa ta yankinsa ba. Sai ya tara dukan sojojinsa, suka fita zuwa cikin hamada, su yaƙi Isra’ila. Da ya kai Yahaz, sai ya yaƙi Isra’ila.
西宏不容以色列人從他的境界經過,就招聚他的眾民出到曠野,要攻擊以色列人,到了雅雜與以色列人爭戰。
24 Isra’ila fa suka kashe shi da takobi, suka ƙwace ƙasarsa, tun daga kogin Arnon har zuwa kogin Yabbok, zuwa kan iyakar Ammonawa kawai, gama sun yi wa iyakansu katanga.
以色列人用刀殺了他,得了他的地,從亞嫩河到雅博河,直到亞捫人的境界,因為亞捫人的境界多有堅壘。
25 Isra’ila suka ci dukan biranen Amoriyawa, suka kuma zauna a cikinsu, haɗe da babban birnin Heshbon da dukan ƙauyukanta.
以色列人奪取這一切的城邑,也住亞摩利人的城邑,就是希實本與希實本的一切鄉村。
26 Sihon sarkin Amoriyawa ya yi mulkin Heshbon, bayan ya ci sarkin Mowab na dā da yaƙi, ya kuma ƙwace dukan ƙasarsa har zuwa arewancin kogin Arnon.
這希實本是亞摩利王西宏的京城;西宏曾與摩押的先王爭戰,從他手中奪取了全地,直到亞嫩河。
27 Shi ya sa Amoriyawa suka rubuta wannan waƙa game da Heshbon suka ce, “Ku zo mu sāke gina Heshbon, birnin Sihon.
所以那些作詩歌的說: 你們來到希實本; 願西宏的城被修造,被建立。
28 “Mayaƙansa sun fito kamar harshen wuta suka ƙone birnin Ar na Mowab suna hallaka’yan ƙasar tuddan Arnon.
因為有火從希實本發出, 有火焰出於西宏的城, 燒盡摩押的亞珥和亞嫩河邱壇的祭司。
29 Kaitonki, Mowab! Gunkinki Kemosh ya yashe mutanenki; aka kuma kama su, aka kai su bauta wajen Sihon sarkin Amoriyawa.
摩押啊,你有禍了! 基抹的民哪,你們滅亡了! 基抹的男子逃奔, 女子被擄,交付亞摩利的王西宏。
30 “Amma mun tumɓuke su, mun hallaka garuruwan Heshbon har zuwa Dibon. Mun ragargaza su har zuwa Nofa wanda ya miƙe zuwa Medeba.”
我們射了他們; 希實本直到底本盡皆毀滅。 我們使地變成荒場,直到挪法; 這挪法直延到米底巴。
31 Ta haka Isra’ila suka zauna a ƙasar Amoriyawa.
這樣,以色列人就住在亞摩利人之地。
32 Sai Musa ya aika’yan leƙen asiri zuwa Yazer. Daga baya, sai Isra’ilawa suka ci ƙauyukan da suke kewaye, suka kuma kori Amoriyawa da suke zaune a can.
摩西打發人去窺探雅謝,以色列人就佔了雅謝的鎮市,趕出那裏的亞摩利人。
33 Sai suka juya suka haura kan hanya ta zuwa Bashan, inda Og yake sarauta, ya kuwa fito tare da dukan sojojinsa suka yi yaƙi da Isra’ila a Edireyi.
以色列人轉回,向巴珊去。巴珊王噩和他的眾民都出來,在以得來與他們交戰。
34 Ubangiji ya ce wa Musa, “Kada ka ji tsoronsa, gama na ba da shi a gare ka, da dukan sojojinsa da kuma ƙasarsa. Ka yi da shi yadda ka yi da Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon.”
耶和華對摩西說:「不要怕他!因我已將他和他的眾民,並他的地,都交在你手中;你要待他像從前待住希實本的亞摩利王西宏一般。」
35 Ta haka suka kashe shi, tare da’ya’yansa maza da kuma dukan sojojinsa, ba wanda ya ragu. Suka kuma mamaye ƙasarsa.
於是他們殺了他和他的眾子,並他的眾民,沒有留下一個,就得了他的地。

< Ƙidaya 21 >