< Ƙidaya 20 >

1 A watan fari, dukan jama’ar Isra’ilawa suka iso Hamadan Zin. Suka sauka a Kadesh. A nan ne Miriyam ta mutu, aka kuma bizne ta.
ויבאו בני ישראל כל העדה מדבר צן בחדש הראשון וישב העם בקדש ותמת שם מרים ותקבר שם
2 Sai aka rasa ruwa da jama’a za su sha, mutane suka taru, suka tayar wa Musa da Haruna.
ולא היה מים לעדה ויקהלו על משה ועל אהרן
3 Suka yi gunaguni wa Musa suka ce, “Da ma mun mutu sa’ad da’yan’uwanmu suka mutu a gaban Ubangiji!
וירב העם עם משה ויאמרו לאמר ולו גוענו בגוע אחינו לפני יהוה
4 Don me ka kawo jama’ar Ubangiji a wannan hamada, don mu da dabbobinmu mu mutu a nan ke nan?
ולמה הבאתם את קהל יהוה אל המדבר הזה למות שם אנחנו ובעירנו
5 Don me ka fitar da mu daga Masar zuwa wannan banzan wuri, inda babu hatsi ko ɓaure, inabi ko rumman. Kuma babu ruwan da za a sha?”
ולמה העליתנו ממצרים להביא אתנו אל המקום הרע הזה לא מקום זרע ותאנה וגפן ורמון ומים אין לשתות
6 Sai Musa da Haruna suka tashi daga taron, suka tafi ƙofar Tentin Sujada, suka fāɗi rubda ciki, sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana musu.
ויבא משה ואהרן מפני הקהל אל פתח אהל מועד ויפלו על פניהם וירא כבוד יהוה אליהם
7 Ubangiji ya ce wa Musa,
וידבר יהוה אל משה לאמר
8 “Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan’uwanka, ku tara jama’a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama’a da garkunansu ruwan sha.”
קח את המטה והקהל את העדה אתה ואהרן אחיך ודברתם אל הסלע לעיניהם ונתן מימיו והוצאת להם מים מן הסלע והשקית את העדה ואת בעירם
9 Sai Musa ya je ya ɗauki sandan kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
ויקח משה את המטה מלפני יהוה כאשר צוהו
10 Shi da Haruna, suka tara jama’a a gaban dutsen, Musa ya ce musu, “Ku saurara, ku’yan tawaye, dole mu kawo muku ruwa daga wannan dutse?”
ויקהלו משה ואהרן את הקהל--אל פני הסלע ויאמר להם שמעו נא המרים--המן הסלע הזה נוציא לכם מים
11 Sai Musa ya ɗaga hannu, ya bugi dutsen sau biyu da sandansa. Ruwa kuwa ya yi ta kwararowa, jama’a da dabbobinsu suka sha.
וירם משה את ידו ויך את הסלע במטהו--פעמים ויצאו מים רבים ותשת העדה ובעירם
12 Amma Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna. “Tun da yake ba ku gaskata ni ba, ba ku kuwa ɗaukaka ni a idon Isra’ilawa ba, to, ba za ku kai taron jama’an nan a ƙasar da na ba su ba.”
ויאמר יהוה אל משה ואל אהרן יען לא האמנתם בי להקדישני לעיני בני ישראל--לכן לא תביאו את הקהל הזה אל הארץ אשר נתתי להם
13 Waɗannan su ne ruwan Meriba, inda Isra’ilawa suka yi wa Ubangiji gunaguni, inda kuma ya nuna kansa mai tsarki a cikinsu.
המה מי מריבה אשר רבו בני ישראל את יהוה ויקדש בם
14 Musa ya aiki manzanni daga Kadesh zuwa wurin sarkin Edom cewa, “Ga abin da ɗan’uwanka Isra’ila ya ce ka san duk irin wahalolin da ya same mu.
וישלח משה מלאכים מקדש אל מלך אדום כה אמר אחיך ישראל אתה ידעת את כל התלאה אשר מצאתנו
15 Kakanninmu sun gangaro zuwa Masar, muka zauna can shekaru da yawa. Masarawa suka wulaƙanta mu, da kuma kakanninmu,
וירדו אבתינו מצרימה ונשב במצרים ימים רבים וירעו לנו מצרים ולאבתינו
16 amma da muka yi kuka a gaban Ubangiji, ya kuwa ji mu, sai ya aiko mala’ika, ya fitar da mu daga Masar. “Yanzu ga mu a Kadesh, garin da yake kan iyakar yankinka.
ונצעק אל יהוה וישמע קלנו וישלח מלאך ויצאנו ממצרים והנה אנחנו בקדש עיר קצה גבולך
17 Muna roƙonka, ka yarda mana mu bi ta ƙasarka. Ba za mu bi ta wani fili, ko gonar inabi ba, ko mu sha ruwa daga wata rijiya ba. Za mu bi ta babban hanyar sarki, ba kuwa za mu kauce dama, ko hagu ba, har mu wuce yankinka.”
נעברה נא בארצך לא נעבר בשדה ובכרם ולא נשתה מי באר דרך המלך נלך לא נטה ימין ושמאול עד אשר נעבר גבלך
18 Amma Edom ya amsa ya ce, “Ba za ku bi ta nan ba; in kuka kuskura, za mu fito, mu yaƙe ku da takobi.”
ויאמר אליו אדום לא תעבר בי--פן בחרב אצא לקראתך
19 Sai Isra’ilawa suka amsa, suka ce, “Za mu bi ta babbar hanya, in mu, ko dabbobinmu suka sha ruwanku, za mu biya. Mu dai muna so mu wuce ne kawai.”
ויאמרו אליו בני ישראל במסלה נעלה ואם מימיך נשתה אני ומקני ונתתי מכרם רק אין דבר ברגלי אעברה
20 Sai mutanen Edom suka sāke amsa suka ce, “Ba za ku bi nan ba dai.” Sai Edom ya fito da runduna mai ƙarfi da yawa gaske a kan Isra’ila.
ויאמר לא תעבר ויצא אדום לקראתו בעם כבד וביד חזקה
21 Da yake Edom suka ƙi su bar su su ratsa yankinsu, sai Isra’ila suka juya suka janye daga gare su.
וימאן אדום נתן את ישראל עבר בגבלו ויט ישראל מעליו
22 Dukan Jama’ar Isra’ilawa suka tashi daga Kadesh, suka zo Dutsen Hor.
ויסעו מקדש ויבאו בני ישראל כל העדה הר ההר
23 A Dutsen Hor, kusa da iyakar Edom, Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
ויאמר יהוה אל משה ואל אהרן בהר ההר על גבול ארץ אדום לאמר
24 “Haruna zai rasu. Ba zai shiga ƙasar da na ba Isra’ilawa ba, domin ku biyu, kun ƙi ku bi umarnina a ruwan Meriba.
יאסף אהרן אל עמיו כי לא יבא אל הארץ אשר נתתי לבני ישראל--על אשר מריתם את פי למי מריבה
25 Ka kawo Haruna da ɗansa Eleyazar, ka kai su a bisan Dutsen Hor.
קח את אהרן ואת אלעזר בנו והעל אתם הר ההר
26 Ka tuɓe taguwar Haruna ka sa wa ɗansa Eleyazar, gama Haruna zai rasu a can.”
והפשט את אהרן את בגדיו והלבשתם את אלעזר בנו ואהרן יאסף ומת שם
27 Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarta. Suka hau Dutsen Hor a idon dukan jama’a.
ויעש משה כאשר צוה יהוה ויעלו אל הר ההר לעיני כל העדה
28 Musa ya tuɓe taguwar Haruna, ya kuma sa wa Eleyazar ɗan Haruna. Nan kuwa Haruna ya mutu a bisa dutsen. Sa’an nan Musa da Eleyazar suka sauka daga dutsen,
ויפשט משה את אהרן את בגדיו וילבש אתם את אלעזר בנו וימת אהרן שם בראש ההר וירד משה ואלעזר מן ההר
29 sa’ad da dukan jama’a kuwa suka ji cewa Haruna ya mutu, sai dukan gidan Isra’ila suka yi makoki dominsa har kwana talatin.
ויראו כל העדה כי גוע אהרן ויבכו את אהרן שלשים יום כל בית ישראל

< Ƙidaya 20 >