< Ƙidaya 19 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
וידבר יהוה אל משה ואל אהרן לאמר
2 “Wannan ita ce ƙa’ida wadda Ubangiji ya umarta. Faɗa wa Isra’ilawa su kawo maka jan karsana marar lahani, ko marar aibi wadda ba a taɓa sa ta tă yi noma ba.
זאת חקת התורה אשר צוה יהוה לאמר דבר אל בני ישראל ויקחו אליך פרה אדמה תמימה אשר אין בה מום אשר לא עלה עליה על
3 Ka ba wa Eleyazar firist; a kuma kai ta bayan sansani, a yanka a gaban Eleyazar.
ונתתם אתה אל אלעזר הכהן והוציא אתה אל מחוץ למחנה ושחט אתה לפניו
4 Sa’an nan Eleyazar firist zai ɗiba jininta a yatsarsa, yă yayyafa sau bakwai wajen gaban Tentin Sujada.
ולקח אלעזר הכהן מדמה--באצבעו והזה אל נכח פני אהל מועד מדמה--שבע פעמים
5 Sa’an nan a ƙone dukan karsanar, haɗe da fatarta, naman, jinin da kayan cikin, yayinda Eleyazar yake kallo.
ושרף את הפרה לעיניו את ערה ואת בשרה ואת דמה על פרשה ישרף
6 Firist zai ɗauki itacen al’ul, da hizzob, da jan ulu, yă jefa su a kan karsanar da ake ƙonewa.
ולקח הכהן עץ ארז ואזוב--ושני תולעת והשליך אל תוך שרפת הפרה
7 Bayan haka, dole firist yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka. Sa’an nan zai iya shiga cikin sansani, amma zai kasance da ƙazanta har yamma.
וכבס בגדיו הכהן ורחץ בשרו במים ואחר יבא אל המחנה וטמא הכהן עד הערב
8 Dole mutumin da ya ƙone ta yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka, shi ma zai kasance da ƙazanta har yamma.
והשרף אתה--יכבס בגדיו במים ורחץ בשרו במים וטמא עד הערב
9 “Mutumin da yake da tsarki, zai tara tokar karsanar, yă sa ta a wurin da yake da tsabta a bayan sansani. Jama’ar Isra’ilawa ne za su adana shi don amfani a ruwan tsabtaccewa; wannan domin tsarkakewa ne daga zunubi.
ואסף איש טהור את אפר הפרה והניח מחוץ למחנה במקום טהור והיתה לעדת בני ישראל למשמרת למי נדה--חטאת הוא
10 Dole mutumin da ya tara tokar karsanar yă wanke rigunarsa, zai kuwa kasance da ƙazanta har yamma. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta har abada ga Isra’ilawa, da kuma baƙin da suke zama a cikinsu.
וכבס האסף את אפר הפרה את בגדיו וטמא עד הערב והיתה לבני ישראל ולגר הגר בתוכם--לחקת עולם
11 “Duk wanda ya taɓa gawa, zai kasance da ƙazanta har kwana bakwai.
הנגע במת לכל נפש אדם--וטמא שבעת ימים
12 Dole yă tsarkake kansa da ruwa a rana ta uku, da kuma a rana ta bakwai; sa’an nan zai zama da tsarki. Amma in bai tsarkake kansa a rana ta uku da kuma a rana ta bakwai ba, ba zai kasance da tsarki ba.
הוא יתחטא בו ביום השלישי וביום השביעי--יטהר ואם לא יתחטא ביום השלישי וביום השביעי--לא יטהר
13 Duk wanda ya taɓa gawar wani, bai kuma tsarkake kansa ba, ya ƙazantar da tabanakul na Ubangiji ke nan. Dole a ware wannan mutum daga cikin Isra’ilawa. Gama ba a yayyafa ruwan tsabtaccewa a kansa ba; ya ƙazantu, ya kasance da ƙazanta ke nan.
כל הנגע במת בנפש האדם אשר ימות ולא יתחטא את משכן יהוה טמא--ונכרתה הנפש ההוא מישראל כי מי נדה לא זרק עליו טמא יהיה--עוד טמאתו בו
14 “Ga ƙa’idar da za a bi in mutum ya mutu a cikin tenti. Duk wanda ya shiga tentin, kuma duk wanda yake cikinsa, za su zama da ƙazanta har kwana bakwai,
זאת התורה אדם כי ימות באהל כל הבא אל האהל וכל אשר באהל יטמא שבעת ימים
15 kuma kowane abin da ake zuba kaya, wanda ba shi da murfi a kansa, zai zama da ƙazanta.
וכל כלי פתוח אשר אין צמיד פתיל עליו--טמא הוא
16 “Wanda duk yake a fili, ya kuma taɓa gawa wanda aka kashe da takobi, ko wanda ya mutu mutuwar Allah, ko ƙashin mutum, ko kabari, zai ƙazantu har bakwai.
וכל אשר יגע על פני השדה בחלל חרב או במת או בעצם אדם או בקבר--יטמא שבעת ימים
17 “Ga wanda ya ƙazantu kuwa, a ɗiba toka daga hadaya ta ƙonawa ta tsarkakewa, a zuba a cikin tulu, sa’an nan a zuba ruwa mai gudu a kansu.
ולקחו לטמא מעפר שרפת החטאת ונתן עליו מים חיים אל כלי
18 Sa’an nan wanda yake tsarkakakke, zai ɗauki hizzob yă tsoma a ruwa, yă yayyafa a tentin da dukan kayayyakinsa, da kuma a kan mutanen da suke wurin. Dole kuma yă yayyafa ruwan a kan duk wanda ya taɓa ƙashin mutu, ko kabari, ko kuma wanda aka kashe, ko wanda ya yi mutuwa ta Allah.
ולקח אזוב וטבל במים איש טהור והזה על האהל ועל כל הכלים ועל הנפשות אשר היו שם ועל הנגע בעצם או בחלל או במת או בקבר
19 A rana ta uku, da ta bakwai kuma mai tsarkakewa zai yayyafa wa marar tsarkin ruwa, a rana ta bakwai kuma yă tsarkake shi. Wanda aka tsarkaken kuwa, dole yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka da yamma, zai kuma tsarkaka.
והזה הטהר על הטמא ביום השלישי וביום השביעי וחטאו ביום השביעי וכבס בגדיו ורחץ במים וטהר בערב
20 Amma in wanda yake da ƙazanta bai tsarkake kansa ba, dole a ware shi daga cikin jama’a, domin ya ƙazantar da wuri mai tsarki na Ubangiji. Ba a yayyafa masa ruwa na tsarkakewa ba, ya zama da ƙazanta.
ואיש אשר יטמא ולא יתחטא ונכרתה הנפש ההוא מתוך הקהל כי את מקדש יהוה טמא מי נדה לא זרק עליו--טמא הוא
21 Wannan za tă zama musu dawwammamiyar farilla. “Mutumin da ya yayyafa ruwa na tsarkakewa, shi ma dole yă wanke rigarsa. Duk wanda kuma ya taɓa ruwan tsarkakewa, zai kasance da ƙazanta har yamma.
והיתה להם לחקת עולם ומזה מי הנדה יכבס בגדיו והנגע במי הנדה יטמא עד הערב
22 Duk abin da mai ƙazanta ya taɓa, ya ƙazantu, kowa kuma ya taɓa wannan abu, ya ƙazantu ke nan, har yamma.”
וכל אשר יגע בו הטמא יטמא והנפש הנגעת תטמא עד הערב

< Ƙidaya 19 >