< Ƙidaya 18 >

1 Ubangiji ya ce wa Haruna, “Kai da’ya’yanka, da kuma iyalin mahaifinka za ku ɗauki hakkin abin da ya shafi Tentin Sujada, kai da’ya’yanka kaɗai za ku ɗauki hakkin aikinku wanda ya shafi firistoci.
ויאמר יהוה אל אהרן אתה ובניך ובית אביך אתך תשאו את עון המקדש ואתה ובניך אתך תשאו את עון כהנתכם
2 Ka kawo’yan’uwanka Lawiyawa daga kabilar kakanka tare da kai, don su taimake ka sa’ad da kai da’ya’yanka kuke hidima a gaban Tentin Sujada.
וגם את אחיך מטה לוי שבט אביך הקרב אתך וילוו עליך וישרתוך ואתה ובניך אתך לפני אהל העדת
3 Za su kasance a ƙarƙashinka, su ne kuma za su yi dukan hidima ta Tenti, amma kada su je kusa da kayayyakin wuri mai tsarki, ko bagade, in ba haka ba, da kai da su, za ku mutu.
ושמרו משמרתך ומשמרת כל האהל אך אל כלי הקדש ואל המזבח לא יקרבו ולא ימתו גם הם גם אתם
4 Za su haɗa hannu tare da kai su ɗauki nauyin lura da Tentin Sujada, dukan ayyuka a Tenti, ba kuma wanda zai zo kusa da inda kake.
ונלוו עליך--ושמרו את משמרת אהל מועד לכל עבדת האהל וזר לא יקרב אליכם
5 “Kai ne za ka ɗauki nauyin lura da wuri mai tsarki da bagade, domin kada fushi yă sāke fāɗa a kan Isra’ilawa.
ושמרתם את משמרת הקדש ואת משמרת המזבח ולא יהיה עוד קצף על בני ישראל
6 Ni da kaina na zaɓo’yan’uwanka Lawiyawa daga cikin Isra’ilawa a matsayin kyauta a gare ku, keɓaɓɓu don Ubangiji, domin su yi hidima a Tentin Sujada.
ואני הנה לקחתי את אחיכם הלוים מתוך בני ישראל--לכם מתנה נתנים ליהוה לעבד את עבדת אהל מועד
7 Amma kai ne kaɗai da’ya’yanka za ku yi aiki a matsayin firistoci game da kowane abu a Tentin Sujada da kuma bayan labule. Ina ba ka aikin firist, yă zama naka. Duk wani kuma da ya zo kusa da wuri mai tsarki, dole a kashe shi.”
ואתה ובניך אתך תשמרו את כהנתכם לכל דבר המזבח ולמבית לפרכת--ועבדתם עבדת מתנה אתן את כהנתכם והזר הקרב יומת
8 Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Na ba ka aikin lura da hadayun da za a miƙa mini, dukan tsarkakan hadayun da Isra’ilawa suka ba ni, na ba ka su su zama rabonka da na’ya’yanka har abada.
וידבר יהוה אל אהרן ואני הנה נתתי לך את משמרת תרומתי לכל קדשי בני ישראל לך נתתים למשחה ולבניך--לחק עולם
9 Kai za ka riƙe sashe mafi tsarki na hadayun da suka ragu daga wuta. Daga dukan kyautai mafi tsarki na hadayun da suka miƙa mini, ko ta gari, ko don zunubi, ko kuma don laifi, wannan kashi naka ne da’ya’yanka.
זה יהיה לך מקדש הקדשים מן האש כל קרבנם לכל מנחתם ולכל חטאתם ולכל אשמם אשר ישיבו לי--קדש קדשים לך הוא ולבניך
10 Ku ci shi a matsayin abu mafi tsarki; kowane namiji zai ci. Dole ku ɗauke shi da tsarki.
בקדש הקדשים תאכלנו כל זכר יאכל אתו קדש יהיה לך
11 “Har yanzu kuma duk abin da aka keɓe daga kyautai na dukan hadayun kaɗawa na Isra’ilawa naka ne. Na ba da wannan gare ka da’ya’yanka maza da mata, a kowane lokaci. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci.
וזה לך תרומת מתנם לכל תנופת בני ישראל--לך נתתים ולבניך ולבנתיך אתך לחק עולם כל טהור בביתך יאכל אתו
12 “Na ba ka duk man zaitun mafi kyau, da ruwan inabi mafi kyau duka, da hatsi mafi kyau duka na nunan farinsu da suke bayarwa ga Ubangiji.
כל חלב יצהר וכל חלב תירוש ודגן--ראשיתם אשר יתנו ליהוה לך נתתים
13 Dukan nunan fari na ƙasar da suke kawo wa Ubangiji, zai zama naka. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci.
בכורי כל אשר בארצם אשר יביאו ליהוה--לך יהיה כל טהור בביתך יאכלנו
14 “Kome a Isra’ila da aka keɓe wa Ubangiji, zai zama naka.
כל חרם בישראל לך יהיה
15 Kowane haihuwar fari, ta mutum, ko ta dabba da suka miƙa wa Ubangiji, naka ne. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram.
כל פטר רחם לכל בשר אשר יקריבו ליהוה באדם ובבהמה--יהיה לך אך פדה תפדה את בכור האדם ואת בכור הבהמה הטמאה תפדה
16 Sa’ad da suke wata ɗaya da haihuwa, dole a fanshe su a bakin shekel biyar-biyar, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri da ake amfani da shi, wanda nauyinsa ya kai gera ashirin.
ופדויו מבן חדש תפדה בערכך כסף חמשת שקלים בשקל הקדש עשרים גרה הוא
17 “Amma kada ka fanshe ɗan fari na saniya, tunkiya, ko akuya; gama suna da tsarki. Ka yayyafa jininsu a bisan bagade, ka kuma ƙone kitsensu kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
אך בכור שור או בכור כשב או בכור עז לא תפדה--קדש הם את דמם תזרק על המזבח ואת חלבם תקטיר--אשה לריח ניחח ליהוה
18 Namansu zai zama naka, haka ma ƙirji na kaɗawa da cinyar dama za su zama naka.
ובשרם יהיה לך כחזה התנופה וכשוק הימין לך יהיה
19 Kome da aka keɓe daga tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da’ya’yanka maza da mata a matsayin zaunannen rabo. Wannan madawwamin alkawarin gishiri ne a gaban Ubangiji dominka da zuriyarka.”
כל תרומת הקדשים אשר ירימו בני ישראל ליהוה--נתתי לך ולבניך ולבנתיך אתך לחק עולם ברית מלח עולם הוא לפני יהוה לך ולזרעך אתך
20 Ubangiji ya ce wa Haruna, “Ba ka da gādo a ƙasarsu, ba kuwa za ka sami rabo daga cikinsu ba; ni ne rabonka da gādonka a cikin Isra’ilawa.
ויאמר יהוה אל אהרן בארצם לא תנחל וחלק לא יהיה לך בתוכם אני חלקך ונחלתך בתוך בני ישראל
21 “Na ba wa Lawiyawa dukan zakka na Isra’ilawa a matsayin gādonsu, saboda aikin da suke yi yayinda suke hidima a Tentin Sujada.
ולבני לוי הנה נתתי כל מעשר בישראל לנחלה חלף עבדתם אשר הם עבדים את עבדת אהל מועד
22 Daga yanzu zuwa gaba, kada Isra’ilawa su yi kusa da Tentin Sujada, in ba haka ba kuwa su sha hukuncin zunubinsu, su kuma mutu.
ולא יקרבו עוד בני ישראל אל אהל מועד לשאת חטא למות
23 Lawiyawa ne za su yi aikin Tentin Sujada, su kuma ɗauki nauyin kowane laifin da aka aikata a wurin. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce daga yanzu har tsararraki masu zuwa. Ba za su sami gādo a cikin Isra’ilawa ba.
ועבד הלוי הוא את עבדת אהל מועד והם ישאו עונם חקת עולם לדרתיכם ובתוך בני ישראל לא ינחלו נחלה
24 A maimako haka, na ba wa Lawiyawa zakka da Isra’ilawa suka kawo domin hadaya ga Ubangiji, a matsayin gādonsu. Shi ya sa na ce game da su, ‘Ba su da gādo a cikin Isra’ilawa.’”
כי את מעשר בני ישראל אשר ירימו ליהוה תרומה נתתי ללוים לנחלה על כן אמרתי להם בתוך בני ישראל לא ינחלו נחלה
25 Ubangiji ya ce wa Musa,
וידבר יהוה אל משה לאמר
26 “Ka yi wa Lawiyawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka karɓi zakka daga Isra’ila da na ba ku gādo, dole ku miƙa kashi ɗaya bisa goma na wannan zakka a matsayin hadaya ga Ubangiji.
ואל הלוים תדבר ואמרת אלהם כי תקחו מאת בני ישראל את המעשר אשר נתתי לכם מאתם בנחלתכם--והרמתם ממנו תרומת יהוה מעשר מן המעשר
27 Za a lissafta hadayarku kamar hatsin da aka sussuka daga masussuka, ko ruwan inabi daga wurin matsewar inabi.
ונחשב לכם תרומתכם--כדגן מן הגרן וכמלאה מן היקב
28 Ta haka za ku miƙa hadaya ga Ubangiji daga cikin dukan zakkar da kuka karɓa daga wurin Isra’ilawa. Daga waɗannan zakka kuwa dole ku ba Haruna firist rabon Ubangiji.
כן תרימו גם אתם תרומת יהוה מכל מעשרתיכם אשר תקחו מאת בני ישראל ונתתם ממנו את תרומת יהוה לאהרן הכהן
29 Dole ku miƙa wa Ubangiji rabo mafi kyau da kuma sashi mafi tsarki na kowane abin da aka ba ku.’
מכל מתנתיכם תרימו את כל תרומת יהוה מכל חלבו--את מקדשו ממנו
30 “Ka faɗa wa Lawiyawa cewa, ‘Sa’ad da kuka miƙa sashi mafi kyau, za a lissafta shi a matsayin abin da ya fito daga masussuka, ko wurin matsewar ruwan inabi ne.
ואמרת אלהם בהרימכם את חלבו ממנו ונחשב ללוים כתבואת גרן וכתבואת יקב
31 Da kai da gidanka, za ku iya cin abin da ya rage a ko’ina, gama ladan aikinku ne a Tentin Sujada.
ואכלתם אתו בכל מקום אתם וביתכם כי שכר הוא לכם חלף עבדתכם באהל מועד
32 Ta wurin miƙa masa sashi mafi kyau, ba za ku zama masu laifi a wannan batu ba; ta haka ba za ku ƙazantar da tsarkakakkun hadayu na Isra’ilawa ba, ba kuwa za ku mutu ba.’”
ולא תשאו עליו חטא בהרימכם את חלבו ממנו ואת קדשי בני ישראל לא תחללו ולא תמותו

< Ƙidaya 18 >