< Ƙidaya 17 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa,
And Jehovah spoke to Moses, saying,
2 “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka kuma karɓi sanduna goma sha biyu daga wurinsu, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu. Ka rubuta sunan kowa a sandansa.
Speak to the sons of Israel, and take rods from them, one for each father's house, from all their rulers according to their fathers' houses, twelve rods. Write thou every man's name upon his rod.
3 A kan sandan Lawi kuwa ka rubuta sunan Haruna, gama dole a sami sanda ɗaya saboda shugaban gidan kakanninsu.
And thou shall write Aaron's name upon the rod of Levi, for there shall be one rod for each head of their fathers' houses.
4 Ka ajiye su a Tentin Sujada, a gaba akwatin Alkawari, inda zan sadu da kai.
And thou shall lay them up in the tent of meeting before the testimony, where I meet with you.
5 Sandan mutumin da na zaɓa zai yi toho, da haka zan raba kaina da gunagunin da Isra’ilawa suke yi.”
And it shall come to pass, that the rod of the man whom I shall choose shall bud. And I will make to cease from me the murmurings of the sons of Israel, which they murmur against you.
6 Saboda haka Musa ya yi magana da Isra’ilawa, sai shugabanninsu suka ba shi sanduna goma sha biyu, sanda ɗaya don shugaba, bisa ga gidajen kakanninsu, sandan Haruna kuma yana a cikinsu.
And Moses spoke to the sons of Israel. And all their rulers gave him rods, for each ruler one, according to their fathers' houses, even twelve rods, and the rod of Aaron was among their rods.
7 Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada.
And Moses laid up the rods before Jehovah in the tent of the testimony.
8 Kashegari da Musa ya shiga cikin Tentin Sujada sai ga sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi’ya’yan almon.
And it came to pass on the morrow, that Moses went into the tent of the testimony, and, behold, the rod of Aaron for the house of Levi was budded, and put forth buds, and produced blossoms, and bore ripe almonds.
9 Sai Musa ya fitar wa dukan Isra’ilawa dukan sandunan da suke daga gaban Ubangiji. Suka duba, kowa kuma ya ɗauki sandansa.
And Moses brought out all the rods from before Jehovah to all the sons of Israel. And they looked, and took every man his rod.
10 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka mayar da sandan Haruna a akwatin Alkawari, don a ajiye shi alama ga masu tawaye. Wannan zai kawo ƙarshen gunaguninsu a kaina, domin kada su mutu.”
And Jehovah said to Moses, Put back the rod of Aaron before the testimony, to be kept for a sign against the sons of rebellion, that thou may make an end of their murmurings against me, that they not die.
11 Musa kuwa ya aikata kamar dai yadda Ubangiji ya umarce shi.
Thus Moses did. As Jehovah commanded him, so he did.
12 Sai Isra’ilawa suka ce wa Musa, “To, ai in haka ne, mun ƙare ke nan!
And the sons of Israel spoke to Moses, saying, Behold, we perish, we are undone, we are all undone.
13 Idan an ce duk wanda ya zo kusa da tabanakul na Ubangiji zai mutu, ai rayuwarmu kamar mun mutu ke nan.”
Every man who comes near, who comes near to the tabernacle of Jehovah, dies. Shall we all of us perish?

< Ƙidaya 17 >