< Ƙidaya 16 >
1 Kora ɗan Izhar, wanda yake Balawe ne daga dangin Kohatawa, wata rana ya nemi Datan da Abiram’ya’yan Eliyab, da On ɗan Felet dukansu daga kabilar Ruben, suka haɗa kai
Now Korah son of Izhar son of Kohath son of Levi, along with Dathan and Abiram sons of Eliab, and On son of Peleth, descendants of Reuben, gathered some men.
2 suka tayar wa Musa. Sai suka nemi goyon bayan sanannun shugabannin Isra’ilawa da aka naɗa a majalisa su guda 250,
They rose up against Moses, along with other men from the people of Israel, two hundred and fifty leaders of the community who were well-known members in the community.
3 tare kuwa suka zo wurin Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun wuce gona da iri! Dukan jama’an nan masu tsarki ne, kowannensu, Ubangiji kuma yana tare da su. Me ya sa kuke ɗaukan kanku fiye da taron jama’ar Ubangiji?”
They assembled themselves together to confront Moses and Aaron. They said to them, “You have gone too far! All the community is set apart, every one of them, and Yahweh is among them. Why do you lift up yourselves above the rest of Yahweh's community?”
4 Da Musa ya ji haka, sai ya fāɗi rubda ciki ya yi addu’a
When Moses heard that, he lay facedown.
5 Sai ya ce wa Kora da dukan waɗannan da suke tare shi, “Da safe, Ubangiji zai nuna wane ne yake nasa, da kuma wane ne yake da tsarki. Zai kuma sa mutumin yă zo kusa da shi. Mutumin da ya zaɓa kuwa zai sa yă zo kusa da shi.
He spoke to Korah and to all those with him, “In the morning Yahweh will make known who belongs to him and who is set apart to him. He will bring that person near to him. The one he chooses he will bring near to himself.
6 Kai Kora da ƙungiyarka, gobe, za ku ɗauki farantai,
Do this, Korah and all your group. Take censers
7 ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa’an nan wanda Ubangiji ya zaɓa a tsakaninmu sh ne mai tsarki. Ku Lawiyawa ku ne kuka wuce gona da iri!”
tomorrow and put fire and incense in them before Yahweh. The one whom Yahweh chooses, that man will be set apart to Yahweh. You have gone too far, you descendants of Levi.”
8 Musa ya kuma ce wa Kora, “Yanzu ku saurara, ku Lawiyawa!
Again, Moses said to Korah, “Now listen, you descendants of Levi:
9 Ashe, bai ishe ku ba, cewa Allah na Isra’ila, ya keɓe ku daga sauran jama’ar Isra’ilawa, ya kuma kawo ku kusa da shi don ku yi aiki a tabanakul na Ubangiji, ku kuma tsaya a gaba jama’a don ku yi musu aiki?
is it a small thing for you that the God of Israel has separated you from the community of Israel, to bring you near to himself, to do work in Yahweh's tabernacle, and to stand before the community to serve them?
10 Ya kawo ku da kuma dukan’yan’uwanku Lawiyawa kusa da shi, amma yanzu kuna ƙoƙari ku karɓi aikin firist.
He has brought you near, and all your kinfolk, the descendants of Levi, with you, yet you are seeking the priesthood also!
11 Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji.”
That is why you and all your group have gathered together against Yahweh. So why are you complaining about Aaron, who obeys Yahweh?”
12 Sai Musa ya aika a kira Datan da Abiram,’ya’yan Eliyab maza, amma suka ce, “Ba za mu zo ba!
Then Moses called for Dathan and Abiram, the sons of Eliab, but they said, “We will not come up.
13 Bai isa ba ne da ka fitar da mu daga ƙasar mai zub da madara da zuma, ka kawo mu nan hamada don ka kashe mu? Yanzu kuma so kake ka mai da kanka sarki a bisanmu?
Is it a small thing that you have brought us up out of a land flowing with milk and honey, to kill us in the wilderness? Now you want to make yourself ruler over us!
14 Ban da haka ma, ai, ba ka riga ka kai mu ƙasar mai zub da madara da zuma ba, ba ka ba mu gādon filaye da gonakin annabi ba, yanzu kuma kana so ka ruɗe mu. Mun ƙi, ba za mun zo ba!”
In addition, you have not brought us into a land flowing with milk and honey, or given us the fields and vineyards as an inheritance. Now do you want to blind us with empty promises? We will not come to you.”
15 Sai Musa ya husata ƙwarai, ya ce wa Ubangiji, “Kada ka karɓi hadayarsu. Ban ƙwace wani jakinsu ba, ban kuwa cuce waninsu ba.”
Moses was very angry and said to Yahweh, “Do not respect their offering. I have not taken one donkey from them, and I have not harmed any of them.”
16 Musa ya ce wa Kora, “Da kai da kuma dukan ƙungiyarka za ku bayyana a gaban Ubangiji gobe, kai da su. Haruna ma zai kasance a can.
Then Moses said to Korah, “Tomorrow you and all your company must go before Yahweh—you and they, and Aaron.
17 Kowannenku zai ɗauki faranti yă zuba turare a ciki. Wato, farantai 250 ke nan, a kuma miƙa su a gaban Ubangiji. Kai da Haruna za ku miƙa farantanku, ku ma.”
Each of you must take his censer and put incense in it. Then each man must bring before Yahweh his censer, two hundred and fifty censers. You and Aaron, also, must each bring your censer.”
18 Sai kowane mutum ya ɗauki farantinsa, ya sa wuta da kuma turare a ciki, suka tsaya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada.
So every man took his censer, put fire in it, laid incense in it, and stood at the entrance to the tent of meeting with Moses and Aaron.
19 Sa’ad da Kora ya tara mabiyansa don su yi hamayya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada, sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan taron.
Korah assembled all the community against Moses and Aaron at the entrance to the tent of meeting, and Yahweh's glory appeared to all the community.
20 Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
Then Yahweh spoke to Moses and to Aaron:
21 “Ku ware kanku daga taron nan don in gama da su nan take.”
“Separate yourselves from among this community that I may consume them immediately.”
22 Amma Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki suka tā da murya suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin dukan’yan adam, za ka husata da dukan taron ne, bayan mutum ɗaya ne ya yi zunubi?”
Moses and Aaron lay facedown and said, “God, the God of the spirits of all humanity, if one man sins, must you be angry with all the community?”
23 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
Yahweh replied to Moses. He said,
24 “Faɗa wa taron cewa, ‘Ku nisanci tentin Kora, da na Datan, da na Abiram.’”
“Speak to the community. Say, 'Get away from the tents of Korah, Dathan, and Abiram.'”
25 Musa ya tashi ya tafi wurin Datan da Abiram, dattawan Isra’ilawa kuwa suka bi shi.
Then Moses rose up and went to Dathan and Abiram; the elders of Israel followed him.
26 Ya gargaɗe taron ya ce, “Ku ƙaurace wa tentin waɗannan mugayen mutane! Kada ku taɓa kome da yake nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.”
He spoke to the community and said, “Now leave the tents of these wicked men and touch nothing of theirs, or you will be consumed by all their sins.”
27 Sai suka tashi daga inda tentin Kora, da Datan, da Abiram suke. Datan da Abiram kuwa suka fita suna tsaye tare da matansu da’ya’yansu da’yan ƙananansu a ƙofar tentinsu.
So the community on every side of the tents of Korah, Dathan, and Abiram left them. Dathan and Abiram came out and stood at the entrance to their tents, with their wives, sons, and their little ones.
28 Sai Musa ya ce musu, “Da haka za ku san cewa Ubangiji ne ya aiko ni, in yi dukan waɗannan abubuwa, ba da nufin kaina na yi su ba.
Then Moses said, “By this you will know that Yahweh has sent me to do all these works, for I have not done them of my own accord.
29 In waɗannan mutane sun mutu kamar yadda mutane suke mutuwa, in abin da yakan sami kowa shi ne ya same su, to, ba Ubangiji ne ya aiko ni ba.
If these men die a natural death such as normally happens, then Yahweh has not sent me.
30 Amma in Ubangiji ya kawo wani abu sabo, ya sa ƙasa ta buɗe bakinta, ta haɗiye su da dukan abin da suke da shi, suka gangara cikin kabari a raye, ta haka za ku sani mutanen nan sun rena Ubangiji.” (Sheol )
But if Yahweh creates something new, and the earth opens its mouth and swallows them, with everything that they possess, and they go down alive into Sheol, then you must understand that these men have despised Yahweh.” (Sheol )
31 Nan da nan da ya gama faɗi wannan, sai ƙasa ta tsage inda Datan da Abiram suke tsaye,
As soon as Moses finished speaking all these words, the ground opened under those men.
32 ta kuma buɗe bakinta, ta haɗiye su tare da mutanen gidansu da dukan mutanen Kora da dukan abin da yake mallakarsu.
The earth opened its mouth and swallowed them, their families, and all the people who belonged to Korah, as well as all their possessions.
33 Suka gangara cikin kabari da rai, tare dukan mallakarsu; ƙasa ta rufe su, suka hallaka, suka rabu da jama’ar. (Sheol )
So they and all that they possessed went down alive into Sheol. The earth closed over them, and they perished from among the community. (Sheol )
34 Da jin kukansu, dukan Isra’ilawa da suke kewaye da su suka gudu, suna ihu, “Ƙasa za tă haɗiye mu, mu ma!”
All Israel around them fled from their cries. They exclaimed, “The earth may swallow us up also!”
35 Sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutane 250 da suke miƙa hadaya da turare.
Then fire flashed out from Yahweh and devoured the 250 men who had offered incense.
36 Ubangiji ya ce wa Musa,
Again Yahweh spoke to Moses and said,
37 “Ka gaya wa Eleyazar ɗan Haruna, firist, yă kawar da farantan ƙona turare daga wurin da wutar ta cinye, yă watsar da gawayin a wani wuri, gama farantan tsarkakakku ne,
“Speak to Eleazar son of Aaron the priest and let him take up the censers out of the flames, for the censers are set apart to me. Then let him scatter the burning coals at a distance.
38 gama an yi amfani da farantan don miƙa mini turare. Sai ka ɗauki farantan mutanen da suka yi zunubin da ya jawo musu mutuwa ka ƙera farantan, ka yi murfin bagade da su, gama an miƙa su a gaban Ubangiji, suka zama tsarkakakku. Bari su zama alama ga Isra’ilawa.”
Take the censers of those who lost their lives because of their sin. Let them be made into hammered plates as a covering over the altar. Those men did offer them before me, so they are set apart to me. They will be a sign of my presence to the people of Israel.”
39 Haka Eleyazar, firist, ya tattara farantan tagulla waɗanda mutanen da aka hallaka suka kawo, ya ƙera murfin bagade da su,
Eleazar the priest took the bronze censers that had been used by the men who were burned up, and they were hammered out into a covering for the altar,
40 yadda Ubangiji ya umarce shi, ta wurin Musa. Wannan ya zama abin tuni ga Isra’ilawa domin kada wani da ba firist ba, bai kuwa fito a cikin zuriyar Haruna ba, yă zo don yă ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada yă zama kamar Kora da mabiyansa.
to be a reminder to the people of Israel, so that no outsider who was not descended from Aaron should come up to burn incense before Yahweh, so they might not become like Korah and his group—just as Yahweh had commanded through Moses.
41 Kashegari dukan taron Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna suka ce, “Kun kashe mutanen Ubangiji.”
But the next morning all the community of the people of Israel complained against Moses and Aaron. They said, “You have killed Yahweh's people.”
42 Bayan haka, sai dukan jama’a suka taru domin su nuna rashin yardansu da abin da suke zato Musa da Haruna ne suka aikata. Da suka fuskanci Tentin Sujada, nan take sai girgije ya rufe shi, ɗaukaka Ubangiji kuwa ta bayyana.
Then it happened, when the community had assembled against Moses and Aaron, that they looked toward the tent of meeting and, behold, the cloud was covering it. Yahweh's glory appeared,
43 Sai Musa da Haruna suka je gaban Tentin Sujada,
and Moses and Aaron came to the front of the tent of meeting.
44 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,
Then Yahweh spoke to Moses. He said,
45 “Ku nisanci wannan taro, gama yanzu nan zan hallaka su.” Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki.
“Go away from in front of this community so that I may consume them immediately.” Then Moses and Aaron lay down with their faces to the ground.
46 Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki farantinka ka sa turare a ciki, da wuta daga bagade, ka yi maza ka tafi wajen taron, ka yi kafara dominsu. Gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko; an kuma fara annoba.”
Moses said to Aaron, “Take the censer, put fire in it from off the altar, put incense in it, carry it quickly to the community, and make atonement for them, because anger is coming from Yahweh. The plague has begun.”
47 Saboda haka Haruna ya yi kamar yadda Musa ya faɗa, ya ruga a guje zuwa tsakiyar taron. An riga an fara annobar a cikin mutane, amma Haruna ya miƙa turaren ya kuma yi kafara dominsu.
So Aaron did as Moses directed. He ran into the middle of the community. The plague had quickly started to spread among the people, so he put in the incense and made atonement for the people.
48 Ya tsaya tsakanin matattu da masu rai, annobar kuwa ta tsaya.
Aaron stood between the dead and the living; in this way the plague was stopped.
49 Amma mutane 14,700 ne suka mutu a annobar, ban da waɗanda suka mutu a sanadin Kora.
Those who died by the plague were 14,700 in number, besides those who had died in the matter of Korah.
50 Sai Haruna ya komo wurin Musa a ƙofar Tentin Sujada, gama annobar ta ƙare.
Aaron returned to Moses at the entrance to the tent of meeting, and the plague ended.