< Ƙidaya 15 >
1 Ubangiji ya ce wa Musa,
耶和华对摩西说:
2 “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Bayan kun shiga ƙasar da nake ba ku a matsayin gida,
“你晓谕以色列人说:你们到了我所赐给你们居住的地,
3 kuka yi hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji, daga cikin shanu, ko tumaki, abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa, ko hadayu don alkawura na musamman, ko hadayar yardar rai, ko kuma hadaya ta biki,
若愿意从牛群羊群中取牛羊作火祭,献给耶和华,无论是燔祭是平安祭,为要还特许的愿,或是作甘心祭,或是逢你们节期献的,都要奉给耶和华为馨香之祭。
4 sai shi wanda ya kawo hadayar yă miƙa wa Ubangiji hadaya ta gari mai laushi mai kyau, kashi ɗaya bisa goma na efa wanda aka kwaɓa da kwalaba ɗaya na mai.
那献供物的就要将细面伊法十分之一,并油一欣四分之一,调和作素祭,献给耶和华。
5 Da kowane ɗan rago don hadaya ta ƙonawa, a shirya kwalaba ɗaya na ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha.
无论是燔祭是平安祭,你要为每只绵羊羔,一同预备奠祭的酒一欣四分之一。
6 “‘In da rago ne za a miƙa, to, sai a shirya hadaya ta gari mai laushi, garin yă zama kashi biyu bisa goma na efa. A kwaɓa shi da kashi ɗaya bisa uku na garwan mai,
为公绵羊预备细面伊法十分之二,并油一欣三分之一,调和作素祭,
7 da kashi ɗaya bisa uku na garwan ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha. A miƙa ta abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.
又用酒一欣三分之一作奠祭,献给耶和华为馨香之祭。
8 “‘Sa’ad da kuka shirya rago don hadaya ta ƙonawa saboda alkawari na musamman, ko hadaya ta salama ga Ubangiji,
你预备公牛作燔祭,或是作平安祭,为要还特许的愿,或是作平安祭,献给耶和华,
9 sai ku kawo hadaya ta gari tare da bijimi, kashi ɗaya bisa uku na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da rabin garwan mai.
就要把细面伊法十分之三,并油半欣,调和作素祭,和公牛一同献上,
10 A kuma kawo rabin garwan ruwan inabi na hadaya ta sha. Za tă zama hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
又用酒半欣作奠祭,献给耶和华为馨香的火祭。
11 Haka za a yi da kowane bijimi, ko rago, ko ɗan rago, ko bunsuru.
“献公牛、公绵羊、绵羊羔、山羊羔,每只都要这样办理。
12 Haka za a yi da kowannensu bisa ga abin da aka shirya.
照你们所预备的数目,按着只数都要这样办理。
13 “‘Duk wanda yake ɗan ƙasa, ta haka ne dole zai aikata waɗannan abubuwa sa’ad da ya kawo hadaya da akan yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
凡本地人将馨香的火祭献给耶和华,都要这样办理。
14 Idan baƙon da yake baƙunci a cikinku, ko kowane ne da yake tare da ku a dukan zamananku, yana so yă ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, dole yă yi kamar yadda kuke yi.
若有外人和你们同居,或有人世世代代住在你们中间,愿意将馨香的火祭献给耶和华,你们怎样办理,他也要照样办理。
15 Ƙa’ida ɗaya ce ga jama’a da kuma baƙin da suke zama a cikinku, wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a dukan tsararraki masu zuwa. Da ku, da baƙi, za ku zama ɗaya a gaban Ubangiji.
至于会众,你们和同居的外人都归一例,作为你们世世代代永远的定例,在耶和华面前,你们怎样,寄居的也要怎样。
16 Doka ɗaya da ƙa’ida ɗaya za a yi aiki da ita a kan ku da kuma baƙin da suke zama a cikinku.’”
你们并与你们同居的外人当有一样的条例,一样的典章。”
17 Ubangiji ya ce wa Musa,
耶和华对摩西说:
18 “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da ina kai ku,
“你晓谕以色列人说:你们到了我所领你们进去的那地,
19 kuka ci abincin ƙasar, ku miƙa wani sashe na amfanin ƙasar a matsayin hadaya ga Ubangiji.
吃那地的粮食,就要把举祭献给耶和华。
20 Ku kawo waina daga nunan fari na ɓarzajjen hatsinku, ku kuma miƙa shi a matsayin hadaya daga masussuka.
你们要用初熟的麦子磨面,做饼当举祭奉献;你们举上,好像举禾场的举祭一样。
21 A duk tsararraki masu zuwa, za ku miƙa wannan hadaya daga nunan fari na ɓarzajjen hatsinku ga Ubangiji.
你们世世代代要用初熟的麦子磨面,当举祭献给耶和华。
22 “‘To, in ku a matsayin jama’a, da gangan kuka ƙi kiyaye waɗannan ƙa’idodi da Ubangiji ya ba wa Musa ba,
“你们有错误的时候,不守耶和华所晓谕摩西的这一切命令,
23 ko wani daga cikin umarnan da Ubangiji ya ba ku ta wurinsa, daga ranar da Ubangiji ya ba da su, har zuwa tsararraki masu zuwa,
就是耶和华借摩西一切所吩咐你们的,自那日以至你们的世世代代,
24 in kuwa aka yi haka ba da gangan ba, kuma da rashin sani, sai duk jama’a su miƙa ɗan bijimi don hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, tare da ƙayyadadden hadaya ta gari, da hadaya ta sha, da kuma bunsuru na hadaya don zunubi.
若有误行,是会众所不知道的,后来全会众就要将一只公牛犊作燔祭,并照典章把素祭和奠祭一同献给耶和华为馨香之祭,又献一只公山羊作赎罪祭。
25 Firist kuwa zai yi kafara domin dukan jama’ar Isra’ilawa, za a kuma gafarta musu, gama ba da gangan ba ne suka aikata, kuma sun kawo wa Ubangiji hadayar da akan yi da wuta da kuma hadaya don zunubi saboda laifinsu.
祭司要为以色列全会众赎罪,他们就必蒙赦免,因为这是错误。他们又因自己的错误,把供物,就是向耶和华献的火祭和赎罪祭,一并奉到耶和华面前。
26 Za a gafarta wa dukan jama’ar Isra’ilawa, da baƙin da suke zama a cikinsu, gama duk laifin da aka yi da rashin sani, yakan shafi dukan mutane.
以色列全会众和寄居在他们中间的外人就必蒙赦免,因为这罪是百姓误犯的。
27 “‘Amma in mutum ɗaya ne kaɗai ya yi laifi ba da gangan ba, dole yă kawo akuya domin hadaya don zunubi.
“若有一个人误犯了罪,他就要献一岁的母山羊作赎罪祭。
28 Firist zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mutumin nan da ya aikata laifi ba da gangan ba, in kuwa an yi kafara saboda shi, za a gafarta masa.
那误行的人犯罪的时候,祭司要在耶和华面前为他赎罪,他就必蒙赦免。
29 Ƙa’ida dai za tă zama ɗaya ga duk wanda ya yi laifi ba da gangan ba, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙon da yake zama a cikinku.
以色列中的本地人和寄居在他们中间的外人,若误行了什么事,必归一样的条例。
30 “‘Amma duk wanda ya yi zunubi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko baƙo, ya saɓi Ubangiji, dole a ware wannan mutum daga mutanensa,
但那擅敢行事的,无论是本地人是寄居的,他亵渎了耶和华,必从民中剪除。
31 gama ya rena maganar Ubangiji, ya kuma karya umarninsa. Tabbatacce za a kashe wannan mutum, alhakinsa laifinsa kuwa yana wuyansa.’”
因他藐视耶和华的言语,违背耶和华的命令,那人总要剪除;他的罪孽要归到他身上。”
32 Yayinda Isra’ilawa suke ciki hamada, sai aka sami wani mutum yana tattara itace a ranar Asabbaci.
以色列人在旷野的时候,遇见一个人在安息日捡柴。
33 Waɗanda suka gan shi, suka kawo shi wurin Musa da Haruna da dukan taro,
遇见他捡柴的人,就把他带到摩西、亚伦并全会众那里,
34 sai suka sa shi a gidan waƙafi don ba su riga sun san abin da za a yi da shi ba tukuna.
将他收在监内;因为当怎样办他,还没有指明。
35 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Dole mutumin yă mutu. Dole dukan taron su jajjefe shi a bayan sansani.”
耶和华吩咐摩西说:“总要把那人治死;全会众要在营外用石头把他打死。”
36 Saboda haka taron suka ɗauke shi zuwa bayan sansani, suka kuma jajjefe shi har ya mutu, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
于是全会众将他带到营外,用石头打死他,是照耶和华所吩咐摩西的。
37 Ubangiji ya ce wa Musa,
耶和华晓谕摩西说:
38 “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘A dukan tsararraki masu zuwa, za ku sa tuntaye a gefen rigunarku, su sa zare mai ruwan shuɗi a bisan kowane tuntu.
“你吩咐以色列人,叫他们世世代代在衣服边上做 子,又在底边的 子上钉一根蓝细带子。
39 Tuntayen za su zama muku abin dubawa don ku riƙa tunawa da dukan umarnan Ubangiji, don kada ku bi son zuciyarku, da sha’awar idanunku yadda kuka taɓa yi.
你们佩带这 子,好叫你们看见就记念遵行耶和华一切的命令,不随从自己的心意、眼目行邪淫,像你们素常一样;
40 Sa’an nan za ku riƙa tuna, ku kuma aikata dukan umarnaina ku zama tsarkaka ga Allahnku.
使你们记念遵行我一切的命令,成为圣洁,归与你们的 神。
41 Ni ne Ubangiji Allahnku, da ya fitar da ku daga Masar, don in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.’”
“我是耶和华—你们的 神,曾把你们从埃及地领出来,要作你们的 神。我是耶和华—你们的 神。”