< Ƙidaya 14 >

1 A daren nan, sai dukan jama’ar suka tā da murya, suka yi kuka da ƙarfi.
ותשא כל העדה ויתנו את קולם ויבכו העם בלילה ההוא
2 Dukan Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, dukan taron kuwa suka ce musu, “Da ma mun mutu a Masar! Ko kuma a wannan hamada ma!
וילנו על משה ועל אהרן כל בני ישראל ויאמרו אלהם כל העדה לו מתנו בארץ מצרים או במדבר הזה לו מתנו
3 Don me Ubangiji yana kawo mu wannan ƙasa yă bar mu kawai mu mutu da takobi? A kuma kwashe matanmu da’ya’yanmu ganima. Ashe, bai fi mana mu koma Masar ba?”
ולמה יהוה מביא אתנו אל הארץ הזאת לנפל בחרב--נשינו וטפנו יהיו לבז הלוא טוב לנו שוב מצרימה
4 Sai suka ce wa junansu, “Mu naɗa wa kanmu shugaba, mu koma Masar.”
ויאמרו איש אל אחיו נתנה ראש ונשובה מצרימה
5 Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki a gaban jama’ar Isra’ilawa da suka taru a can.
ויפל משה ואהרן על פניהם לפני כל קהל עדת בני ישראל
6 Yoshuwa ɗan Nun da Kaleb ɗan Yefunne waɗanda suke tare da masu leƙo asirin ƙasar, suka yayyage tufafinsu
ויהושע בן נון וכלב בן יפנה מן התרים את הארץ--קרעו בגדיהם
7 suka ce wa dukan taron Isra’ilawa, “Ƙasar da muka ratsa, muka kuma leƙi asirinta, tana da kyau sosai.
ויאמרו אל כל עדת בני ישראל לאמר הארץ אשר עברנו בה לתור אתה--טובה הארץ מאד מאד
8 In Ubangiji ya ji daɗinmu, zai kai mu ƙasan nan, ƙasar da take zub da madara da zuma, yă kuwa ba mu ita.
אם חפץ בנו יהוה--והביא אתנו אל הארץ הזאת ונתנה לנו ארץ אשר הוא זבת חלב ודבש
9 Sai dai kada ku tayar wa Ubangiji. Kada kuma ku ji tsoron mutane ƙasar, domin za mu gama da su. Kāriyarsu ta gama, amma Ubangiji yana nan tare da mu. Kada ku ji tsoronsu.”
אך ביהוה אל תמרדו ואתם אל תיראו את עם הארץ כי לחמנו הם סר צלם מעליהם ויהוה אתנו אל תיראם
10 Amma taron jama’a suka ce za su jajjefe su da duwatsu. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana a Tentin Sujada ga dukan Isra’ilawa.
ויאמרו כל העדה לרגום אתם באבנים וכבוד יהוה נראה באהל מועד אל כל בני ישראל
11 Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe mutanen nan za su rena ni? Har yaushe za su ƙi gaskata da ni, duk da yawan mu’ujizan da nake yi a cikinsu?
ויאמר יהוה אל משה עד אנה ינאצני העם הזה ועד אנה לא יאמינו בי בכל האתות אשר עשיתי בקרבו
12 Zan buge su duka da annoba, in hallaka su, amma zan mai da kai al’umma mai girma, da kuma ƙarfi fiye da su.”
אכנו בדבר ואורשנו ואעשה אתך לגוי גדול ועצום ממנו
13 Sai Musa ya ce wa Ubangiji, “Ai, Masarawa za su ji game da wannan! Da ikonka ka fitar da mutanen nan daga cikinsu.
ויאמר משה אל יהוה ושמעו מצרים כי העלית בכחך את העם הזה מקרבו
14 Za su kuwa gaya wa mutanen wannan ƙasa. Sun riga sun ji cewa kai, ya Ubangiji, kana tare da waɗannan mutane, kuma cewa kai, ya Ubangiji, an gan ka fuska da fuska, cewa girgijenka ya tsaya bisansu, cewa kana tafiya a gabansu cikin ginshiƙin girgije da rana, da ginshiƙin wuta kuma da dare.
ואמרו אל יושב הארץ הזאת שמעו כי אתה יהוה בקרב העם הזה אשר עין בעין נראה אתה יהוה ועננך עמד עלהם ובעמד ענן אתה הלך לפניהם יומם ובעמוד אש לילה
15 In ka kashe dukan mutanen nan gaba ɗaya, al’ummai da suka ji wannan labari game da kai za su ce,
והמתה את העם הזה כאיש אחד ואמרו הגוים אשר שמעו את שמעך לאמר
16 ‘Ubangiji ya kāsa kai waɗannan mutane a ƙasar da ya yi alkawari da rantsuwa ne, shi ya sa ya kashe su a hamada.’
מבלתי יכלת יהוה להביא את העם הזה אל הארץ אשר נשבע להם וישחטם במדבר
17 “Yanzu bari Ubangiji yă nuna ikonsa, kamar dai yadda ka furta.
ועתה יגדל נא כח אדני כאשר דברת לאמר
18 ‘Ubangiji mai jinkiri fushi ne, mai yawan ƙauna, mai gafarta zunubi da tawaye. Duk da haka ba ya ƙyale mai laifi, babu horo. Yana horin’ya’ya saboda zunubin iyayensu har tsara ta uku, da ta huɗu.’
יהוה ארך אפים ורב חסד נשא עון ופשע ונקה לא ינקה--פקד עון אבות על בנים על שלשים ועל רבעים
19 Bisa ga ƙaunarka mai girma, ka gafarta zunubin mutanen nan, kamar dai yadda ka gafarta musu daga lokacin da suka bar Masar har zuwa yanzu.”
סלח נא לעון העם הזה--כגדל חסדך וכאשר נשאתה לעם הזה ממצרים ועד הנה
20 Ubangiji ya amsa ya ce, “Na gafarta musu, yadda ka roƙa.
ויאמר יהוה סלחתי כדברך
21 Duk da haka, muddin ina raye, kuma muddin ɗaukakar Ubangiji ta cika dukan duniya,
ואולם חי אני וימלא כבוד יהוה את כל הארץ
22 ko ɗaya daga cikinsu da suka ga ɗaukakata da mu’ujizai da na yi a Masar, da kuma a cikin hamada, da suka ƙi yin mini biyayya, suka kuma gwada ni har sau goma,
כי כל האנשים הראים את כבדי ואת אתתי אשר עשיתי במצרים ובמדבר וינסו אתי זה עשר פעמים ולא שמעו בקולי
23 ba ko ɗayansu da zai gan ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa zan ba wa kakanninsu. Ba ko ɗaya da ya rena ni, da zai taɓa ganinta.
אם יראו את הארץ אשר נשבעתי לאבתם וכל מנאצי לא יראוה
24 Amma domin Kaleb bawana ya kasance da ruhu dabam, ya kuma bi ni da zuciya ɗaya, zan kai shi cikin ƙasar da ya je, zuriyarsa kuwa za su gāje ta.
ועבדי כלב עקב היתה רוח אחרת עמו וימלא אחרי--והביאתיו אל הארץ אשר בא שמה וזרעו יורשנה
25 Da yake Amalekawa da Kan’aniyawa suna zama a kwarin, gobe sai ka koma baya, ka nufi wajen hamada ta hanyar Jan Teku.”
והעמלקי והכנעני יושב בעמק מחר פנו וסעו לכם המדבר--דרך ים סוף
26 Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
וידבר יהוה אל משה ואל אהרן לאמר
27 “Har yaushe wannan muguwar al’umma za tă yi gunaguni a kaina? Na ji koke-koken waɗannan Isra’ilawa masu gunaguni.
עד מתי לעדה הרעה הזאת אשר המה מלינים עלי את תלנות בני ישראל אשר המה מלינים עלי--שמעתי
28 Saboda haka ka gaya musu cewa, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji, zan yi muku daidai da abin da na ji kuke faɗa.
אמר אלהם חי אני נאם יהוה אם לא כאשר דברתם באזני כן אעשה לכם
29 A cikin wannan hamadan, jikunanku za su fāɗi, kowanne a cikinku mai shekara ashirin ko fiye, wanda aka ƙirga shi cikin ƙidaya, wanda kuma ya yi gunaguni a kaina, da zai shiga wannan ƙasa.
במדבר הזה יפלו פגריכם וכל פקדיכם לכל מספרכם מבן עשרים שנה ומעלה אשר הלינתם עלי
30 Ba ko ɗaya daga cikinku da zai shiga ƙasar da na ɗaga hannu na rantse, za tă zama gidanku, sai dai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.
אם אתם תבאו אל הארץ אשר נשאתי את ידי לשכן אתכם בה--כי אם כלב בן יפנה ויהושע בן נון
31 Amma game da’ya’yanku da kuka ce za a kwashe ganima, zan kawo su cikin ƙasar, su ji daɗin ƙasar wadda kuka ƙi.
וטפכם--אשר אמרתם לבז יהיה והביאתי אתם--וידעו את הארץ אשר מאסתם בה
32 Amma ku, jikunanku za su fāɗi a wannan hamada.
ופגריכם אתם--יפלו במדבר הזה
33 ’Ya’yanku za su zama makiyaya a nan, shekaru arba’in suna shan wahala domin rashin amincinku, har sai mutum na ƙarshe a cikinku ya kwanta a hamada.
ובניכם יהיו רעים במדבר ארבעים שנה ונשאו את זנותיכם--עד תם פגריכם במדבר
34 Shekaru arba’in, shekara ɗaya a madadi kwana ɗaya cikin kwanakin arba’in da kuka ɗauka kuka leƙi asirin ƙasa, za ku sha wahala saboda zunubanku, ku kuma san abin da ake nufi da sa ni in yi gāba da ku.’
במספר הימים אשר תרתם את הארץ ארבעים יום--יום לשנה יום לשנה תשאו את עונתיכם ארבעים שנה וידעתם את תנואתי
35 Ni, Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata waɗannan abubuwa a kan dukan muguwar jama’an nan da suka haɗa kai, suka tayar mini. Za su sadu da ƙarshensu a wannan hamada; a nan za su mutu.”
אני יהוה דברתי אם לא זאת אעשה לכל העדה הרעה הזאת הנועדים עלי במדבר הזה יתמו ושם ימתו
36 Saboda haka mutanen da Musa ya aika, su leƙo asirin ƙasar, waɗanda suka komo, suka sa taron jama’a su yi gunaguni a kansa saboda sun kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar,
והאנשים אשר שלח משה לתור את הארץ וישבו וילונו (וילינו) עליו את כל העדה להוציא דבה על הארץ
37 waɗannan mutanen da suka kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar, annoba ta buge su, suka kuwa mutu a gaban Ubangiji.
וימתו האנשים מוצאי דבת הארץ רעה--במגפה לפני יהוה
38 Daga cikin mutanen da suka leƙo asirin ƙasar, Yoshuwa ɗan Nun, da Kaleb ɗan Yefunne ne, kaɗai suka rayu.
ויהושע בן נון וכלב בן יפנה חיו מן האנשים ההם ההלכים לתור את הארץ
39 Da Musa ya gaya wa dukan Isra’ilawa wannan labari, sai suka yi baƙin ciki ƙwarai.
וידבר משה את הדברים האלה אל כל בני ישראל ויתאבלו העם מאד
40 Kashegari da sassafe suka haura ta wajen ƙasa mai tudu suka ce, “Mun yi zunubi, za mu tafi inda Ubangiji ya yi alkawari.”
וישכמו בבקר ויעלו אל ראש ההר לאמר הננו ועלינו אל המקום אשר אמר יהוה--כי חטאנו
41 Amma Musa ya ce, “Don me kuke rashin biyayya da umarnin Ubangiji? Wannan ba zai yiwu ba!
ויאמר משה למה זה אתם עברים את פי יהוה והוא לא תצלח
42 Kada ku haura, domin Ubangiji, ba ya tare da ku. Magabtanku za su ci nasara a kanku,
אל תעלו כי אין יהוה בקרבכם ולא תנגפו לפני איביכם
43 gama Amalekawa da Kan’aniyawa za su kara da ku a can. Domin kun juya daga Ubangiji, ba zai kasance da ku ba, za a kuma karkashe ku da takobi.”
כי העמלקי והכנעני שם לפניכם ונפלתם בחרב כי על כן שבתם מאחרי יהוה ולא יהיה יהוה עמכם
44 Duk da haka, suka yi tsammani ba zai zama haka ba, sai suka haura ta wajen ƙasa mai tudu, Musa da akwatin alkawarin Ubangiji dai ba su gusa daga sansanin ba.
ויעפלו לעלות אל ראש ההר וארון ברית יהוה ומשה לא משו מקרב המחנה
45 Sai Amalekawa da Kan’aniyawa mazaunan ƙasar tudu, suka gangaro suka auka musu, suka bubbuge su suka kokkore su har Horma.
וירד העמלקי והכנעני הישב בהר ההוא ויכום ויכתום עד החרמה

< Ƙidaya 14 >