< Ƙidaya 12 >

1 Miriyam da Haruna suka fara zargin Musa saboda matarsa’yar ƙasar Kush da ya aura.
And Mariam and Aaron spoke against Moses, because of the Ethiopian woman whom Moses took; for he had taken an Ethiopian woman.
2 Suka ce, “Ubangiji ya yi magana ta wurin Musa ne kaɗai? Ashe, bai yi magana ta wurinmu mu ma ba?” Ubangiji kuwa ya ji wannan.
And they said, Has the Lord spoken to Moses only? has he not also spoken to us? and the Lord heard it.
3 (Musa kuwa mutum ne mai tawali’u ƙwarai, mafi tawali’u fiye da kowane mutum a duniya.)
And the man Moses was very meek beyond all the men that were upon the earth.
4 Nan da nan Ubangiji ya ce wa Musa, da Haruna da kuma Miriyam, “Ku fita ku tafi Tentin Sujada, dukanku uku.” Sai dukansu uku suka tafi.
And the Lord said immediately to Moses and Aaron and Mariam, Come forth all three of you to the tabernacle of witness.
5 Sai Ubangiji ya sauko a cikin ginshiƙin girgije; ya tsaya a bakin ƙofar Tenti, ya kira Haruna da Miriyam. Sa’ad da su biyu suka gusa gaba,
And the three came forth to the tabernacle of witness; and the Lord descended in a pillar of a cloud, and stood at the door of the tabernacle of witness; and Aaron and Mariam were called; and both came forth.
6 sai ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa, “Duk lokacin da akwai annabin Ubangiji a cikinku, nakan bayyana kaina gare shi cikin wahayi, in yi magana da shi cikin mafarkai.
And he said to them, Hear my words: If there should be of you a prophet to the Lord, I will be made known to him in a vision, and in sleep will I speak to him.
7 Amma ba haka nake magana da Musa bawana ba; na sa shi yă lura da dukan jama’ata Isra’ila.
My servant Moses [is] not so; he is faithful in all my house.
8 Da shi nake magana fuska da fuska, a fili kuma, ba a kacici-kacici ba; yakan ga siffar Ubangiji. To, me ya sa ba ku ji tsoro ku yi magana a kan bawana Musa ba?”
I will speak to him mouth to mouth apparently, and not in dark speeches; and he has seen the glory of the Lord; and why were ye not afraid to speak against my servant Moses?
9 Sai fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kansu, ya kuma rabu da su.
And the great anger of the Lord [was] upon them, and he departed.
10 Da girgijen ya tashi daga bisa Tentin, sai ga Miriyam tsaye, kuturwa, fari fat. Haruna kuwa ya juya wajenta ya ga ta kuturce;
And the cloud departed from the tabernacle; and, behold, Mariam was leprous, [white] as snow; and Aaron looked upon Mariam, and, behold, she [was] leprous.
11 sai Haruna ya ce wa Musa, “Ranka yă daɗe, ina roƙonka kada ka hukunta mu, gama zunubin da muka yi, mun yi ne cikin wauta.
And Aaron said to Moses, I beseech thee, my lord, do not lay sin upon us, for we were ignorant wherein we sinned.
12 Kada ka sa ta zama kamar haifaffen mataccen jariri daga cikin mahaifiya wanda rabin jikin ruɓaɓɓe ne.”
Let her not be as it were like death, as an abortion coming out of his mother's womb, when [the disease] devours the half of the flesh.
13 Saboda haka sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Allah, ina roƙonka ka warkar da ita!”
And Moses cried to the Lord, saying, O God, I beseech thee, heal her.
14 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata miyau a fuskarta, ashe, ba za tă ji kunya har kwana bakwai ba? A fitar da ita bayan sansani kwana bakwai; bayan haka za a iya dawo da ita.”
And the Lord said to Moses, If her father had only spit in her face, would she not be ashamed seven days? let her be set apart seven days without the camp, and afterwards she shall come in.
15 Haka aka fitar da Miriyam bayan sansani kwana bakwai, mutane kuwa ba su ci gaba da tafiya ba sai da aka dawo da ita.
And Mariam was separated without the camp seven days; and the people moved not forward till Mariam was cleansed.
16 Bayan haka sai mutane suka bar Hazerot suka sauka a Hamadan Faran.
And afterwards the people set forth from Aseroth, and encamped in the wilderness of Pharan.

< Ƙidaya 12 >