< Ƙidaya 11 >
1 Da Ubangiji ya ji gunagunin da mutanen suke yi saboda wahalarsu, sai ya husata ƙwarai. Sai wuta daga Ubangiji ta yi ta ci a cikinsu har ta ƙone waɗansu wurare na sansanin.
καὶ ἦν ὁ λαὸς γογγύζων πονηρὰ ἔναντι κυρίου καὶ ἤκουσεν κύριος καὶ ἐθυμώθη ὀργῇ καὶ ἐξεκαύθη ἐν αὐτοῖς πῦρ παρὰ κυρίου καὶ κατέφαγεν μέρος τι τῆς παρεμβολῆς
2 Da jama’ar suka yi wa Musa kuka, sai ya yi addu’a ga Ubangiji, wutar kuwa ta mutu.
καὶ ἐκέκραξεν ὁ λαὸς πρὸς Μωυσῆν καὶ ηὔξατο Μωυσῆς πρὸς κύριον καὶ ἐκόπασεν τὸ πῦρ
3 Saboda haka aka kira wannan wuri Tabera, gama a wurin ne wuta daga Ubangiji ta ƙuna a cikinsu.
καὶ ἐκλήθη τὸ ὄνομα τοῦ τόπου ἐκείνου ἐμπυρισμός ὅτι ἐξεκαύθη ἐν αὐτοῖς πῦρ παρὰ κυρίου
4 Wata rana, baƙin da suke cikinsu, suka fara kwaɗayin waɗansu abinci, har suka sa Isra’ilawa suka fara kuka, suna cewa, “Da mun sami nama mun ci mana!
καὶ ὁ ἐπίμικτος ὁ ἐν αὐτοῖς ἐπεθύμησαν ἐπιθυμίαν καὶ καθίσαντες ἔκλαιον καὶ οἱ υἱοὶ Ισραηλ καὶ εἶπαν τίς ἡμᾶς ψωμιεῖ κρέα
5 Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, haka ma kayan lambu irin su kukumba, guna, safa, albasa da kuma tafarnuwa.
ἐμνήσθημεν τοὺς ἰχθύας οὓς ἠσθίομεν ἐν Αἰγύπτῳ δωρεάν καὶ τοὺς σικύας καὶ τοὺς πέπονας καὶ τὰ πράσα καὶ τὰ κρόμμυα καὶ τὰ σκόρδα
6 Amma ga shi yanzu ba mu da wani abin marmari; in ba wannan Manna ba!”
νυνὶ δὲ ἡ ψυχὴ ἡμῶν κατάξηρος οὐδὲν πλὴν εἰς τὸ μαννα οἱ ὀφθαλμοὶ ἡμῶν
7 Manna kuwa kamar tsabar riɗi take, kamanninta kuma kamar ƙaro ne.
τὸ δὲ μαννα ὡσεὶ σπέρμα κορίου ἐστίν καὶ τὸ εἶδος αὐτοῦ εἶδος κρυστάλλου
8 Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa a dutsen niƙa, ko kuwa su daka a turmi. Su dafa, ko su yi waina da ita. Ɗanɗanonta yakan yi kamar abin da aka yi da man zaitun.
καὶ διεπορεύετο ὁ λαὸς καὶ συνέλεγον καὶ ἤληθον αὐτὸ ἐν τῷ μύλῳ καὶ ἔτριβον ἐν τῇ θυίᾳ καὶ ἥψουν αὐτὸ ἐν τῇ χύτρᾳ καὶ ἐποίουν αὐτὸ ἐγκρυφίας καὶ ἦν ἡ ἡδονὴ αὐτοῦ ὡσεὶ γεῦμα ἐγκρὶς ἐξ ἐλαίου
9 Sa’ad da raɓa tana saukowa da dad dare a kan sansani, Manna ma takan sauko.
καὶ ὅταν κατέβη ἡ δρόσος ἐπὶ τὴν παρεμβολὴν νυκτός κατέβαινεν τὸ μαννα ἐπ’ αὐτῆς
10 Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko’ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar tentinsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai, sai Musa ya damu.
καὶ ἤκουσεν Μωυσῆς κλαιόντων αὐτῶν κατὰ δήμους αὐτῶν ἕκαστον ἐπὶ τῆς θύρας αὐτοῦ καὶ ἐθυμώθη ὀργῇ κύριος σφόδρα καὶ ἔναντι Μωυσῆ ἦν πονηρόν
11 Sai ya ce wa Ubangiji, “Me ya sa ka kawo wannan damuwar a kan bawanka? Me na yi da ya ɓata maka rai har ka ɗora dukan nauyin mutanen nan a kaina?
καὶ εἶπεν Μωυσῆς πρὸς κύριον ἵνα τί ἐκάκωσας τὸν θεράποντά σου καὶ διὰ τί οὐχ εὕρηκα χάριν ἐναντίον σου ἐπιθεῖναι τὴν ὁρμὴν τοῦ λαοῦ τούτου ἐπ’ ἐμέ
12 Ni ne na yi cikin dukan mutanen nan? Ni ne na haife su? To, me ya sa ka ce in ɗauke su a ƙirjina kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka yi alkawari da rantsuwa za ka ba wa kakanninsu?
μὴ ἐγὼ ἐν γαστρὶ ἔλαβον πάντα τὸν λαὸν τοῦτον ἢ ἐγὼ ἔτεκον αὐτούς ὅτι λέγεις μοι λαβὲ αὐτὸν εἰς τὸν κόλπον σου ὡσεὶ ἄραι τιθηνὸς τὸν θηλάζοντα εἰς τὴν γῆν ἣν ὤμοσας τοῖς πατράσιν αὐτῶν
13 Ina ne zan sami nama in waɗannan mutane? Sun dinga yin mini kuka suna cewa ‘Ka ba mu nama mu ci!’
πόθεν μοι κρέα δοῦναι παντὶ τῷ λαῷ τούτῳ ὅτι κλαίουσιν ἐπ’ ἐμοὶ λέγοντες δὸς ἡμῖν κρέα ἵνα φάγωμεν
14 Ba zan iya ɗaukan dukan mutanen nan ni kaɗai ba, nauyin ya yi mini yawa.
οὐ δυνήσομαι ἐγὼ μόνος φέρειν τὸν λαὸν τοῦτον ὅτι βαρύτερόν μοί ἐστιν τὸ ῥῆμα τοῦτο
15 In haka za ka yi da ni, ka kashe ni yanzu, in na sami tagomashi daga gare ka, kada ka bar ni in rayu in ga wannan baƙin ciki.”
εἰ δὲ οὕτως σὺ ποιεῖς μοι ἀπόκτεινόν με ἀναιρέσει εἰ εὕρηκα ἔλεος παρὰ σοί ἵνα μὴ ἴδω μου τὴν κάκωσιν
16 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattaro mini dattawa saba’in daga cikin mutanen Isra’ila, waɗanda aka sani su ne dattawa da kuma shugabanni a cikin jama’a. Ka sa su zo Tentin Sujada, su tsaya a can tare da kai.
καὶ εἶπεν κύριος πρὸς Μωυσῆν συνάγαγέ μοι ἑβδομήκοντα ἄνδρας ἀπὸ τῶν πρεσβυτέρων Ισραηλ οὓς αὐτὸς σὺ οἶδας ὅτι οὗτοί εἰσιν πρεσβύτεροι τοῦ λαοῦ καὶ γραμματεῖς αὐτῶν καὶ ἄξεις αὐτοὺς πρὸς τὴν σκηνὴν τοῦ μαρτυρίου καὶ στήσονται ἐκεῖ μετὰ σοῦ
17 Zan sauko in yi magana da kai a can, zan kuma ɗauki Ruhun da yake kanka in mai da shi wajensu. Za su taimake ka ɗaukan nauyin mutane, don yă zama ba kai kaɗai ba ne mai ɗaukan kaya.
καὶ καταβήσομαι καὶ λαλήσω ἐκεῖ μετὰ σοῦ καὶ ἀφελῶ ἀπὸ τοῦ πνεύματος τοῦ ἐπὶ σοὶ καὶ ἐπιθήσω ἐπ’ αὐτούς καὶ συναντιλήμψονται μετὰ σοῦ τὴν ὁρμὴν τοῦ λαοῦ καὶ οὐκ οἴσεις αὐτοὺς σὺ μόνος
18 “Ka gaya wa mutane, ‘Ku tsarkake kanku don gobe, za ku ci nama. Ubangiji ya ji ku sa’ad da kuka yi kuka cewa, “Da mun sami nama mun ci mana! Ai, da ba mu da damuwa, gama lokacin da muke zama cikin Masar ba mu da damuwa!” Yanzu Ubangiji zai ba ku nama, za ku kuma ci.
καὶ τῷ λαῷ ἐρεῖς ἁγνίσασθε εἰς αὔριον καὶ φάγεσθε κρέα ὅτι ἐκλαύσατε ἔναντι κυρίου λέγοντες τίς ἡμᾶς ψωμιεῖ κρέα ὅτι καλὸν ἡμῖν ἐστιν ἐν Αἰγύπτῳ καὶ δώσει κύριος ὑμῖν κρέα φαγεῖν καὶ φάγεσθε κρέα
19 Ba za ku ci shi na kwana ɗaya, ko biyu, ko biyar, ko goma, ko kuma kwana ashirin kaɗai ba,
οὐχ ἡμέραν μίαν φάγεσθε οὐδὲ δύο οὐδὲ πέντε ἡμέρας οὐδὲ δέκα ἡμέρας οὐδὲ εἴκοσι ἡμέρας
20 amma za ku ci har na wata guda cur, sai ya gundure ku a hanci har ku yi ƙyamarsa, domin kun ƙi Ubangiji wanda yake cikinku, kuka yi kuka a gabansa, kuna cewa, “Don me ma muka bar ƙasar Masar?”’”
ἕως μηνὸς ἡμερῶν φάγεσθε ἕως ἂν ἐξέλθῃ ἐκ τῶν μυκτήρων ὑμῶν καὶ ἔσται ὑμῖν εἰς χολέραν ὅτι ἠπειθήσατε κυρίῳ ὅς ἐστιν ἐν ὑμῖν καὶ ἐκλαύσατε ἐναντίον αὐτοῦ λέγοντες ἵνα τί ἡμῖν ἐξελθεῖν ἐξ Αἰγύπτου
21 Amma Musa ya ce, “Ga ni a cikin mutane dubu ɗari shida tafe tare da ni, kana kuma cewa, ‘Zan ba su nama su ci har wata guda cur!’
καὶ εἶπεν Μωυσῆς ἑξακόσιαι χιλιάδες πεζῶν ὁ λαός ἐν οἷς εἰμι ἐν αὐτοῖς καὶ σὺ εἶπας κρέα δώσω αὐτοῖς φαγεῖν καὶ φάγονται μῆνα ἡμερῶν
22 Za su ma sami isashe in har aka yanka musu garkuna tumaki da na shanu? Za su sami isashe in aka kama musu dukan kifin teku?”
μὴ πρόβατα καὶ βόες σφαγήσονται αὐτοῖς καὶ ἀρκέσει αὐτοῖς ἢ πᾶν τὸ ὄψος τῆς θαλάσσης συναχθήσεται αὐτοῖς καὶ ἀρκέσει αὐτοῖς
23 Ubangiji ya ce wa Musa, “Akwai abin da ya fi ƙarfina ne? Bari ka gani ko abin da na ce zan yi, zai faru ko babu.”
καὶ εἶπεν κύριος πρὸς Μωυσῆν μὴ χεὶρ κυρίου οὐκ ἐξαρκέσει ἤδη γνώσει εἰ ἐπικαταλήμψεταί σε ὁ λόγος μου ἢ οὔ
24 Saboda haka Musa ya fita ya gaya wa jama’a abin da Ubangiji ya faɗa. Ya tattaro dattawansu saba’in, ya sa suka tsaya kewaye da Tentin Sujada.
καὶ ἐξῆλθεν Μωυσῆς καὶ ἐλάλησεν πρὸς τὸν λαὸν τὰ ῥήματα κυρίου καὶ συνήγαγεν ἑβδομήκοντα ἄνδρας ἀπὸ τῶν πρεσβυτέρων τοῦ λαοῦ καὶ ἔστησεν αὐτοὺς κύκλῳ τῆς σκηνῆς
25 Sa’an nan Ubangiji ya sauko daga girgije, ya yi magana da shi, ya kuma ɗauke Ruhun da yake kan Musa ya ɗora shi a kan dattawa saba’in nan. Sa’ad da Ruhun ya zauna a kansu, sai suka yi annabci, amma daga wannan ba su ƙara yin haka kuma ba.
καὶ κατέβη κύριος ἐν νεφέλῃ καὶ ἐλάλησεν πρὸς αὐτόν καὶ παρείλατο ἀπὸ τοῦ πνεύματος τοῦ ἐπ’ αὐτῷ καὶ ἐπέθηκεν ἐπὶ τοὺς ἑβδομήκοντα ἄνδρας τοὺς πρεσβυτέρους ὡς δὲ ἐπανεπαύσατο τὸ πνεῦμα ἐπ’ αὐτούς καὶ ἐπροφήτευσαν καὶ οὐκέτι προσέθεντο
26 To, fa, akwai dattawa biyu da suka kasance a sansani, wato, Eldad da Medad. Su ma an lasafta su cikin dattawan, amma ba su fita zuwa Tentin Sujada ba. Duk da haka Ruhun ya sauka a kansu, suka kuma yi annabci a cikin sansanin.
καὶ κατελείφθησαν δύο ἄνδρες ἐν τῇ παρεμβολῇ ὄνομα τῷ ἑνὶ Ελδαδ καὶ ὄνομα τῷ δευτέρῳ Μωδαδ καὶ ἐπανεπαύσατο ἐπ’ αὐτοὺς τὸ πνεῦμα καὶ οὗτοι ἦσαν τῶν καταγεγραμμένων καὶ οὐκ ἦλθον πρὸς τὴν σκηνήν καὶ ἐπροφήτευσαν ἐν τῇ παρεμβολῇ
27 Wani saurayi ya sheƙa a guje zuwa wajen Musa ya ce, “Eldad da Medad suna can suna annabci a sansani.”
καὶ προσδραμὼν ὁ νεανίσκος ἀπήγγειλεν Μωυσῇ καὶ εἶπεν λέγων Ελδαδ καὶ Μωδαδ προφητεύουσιν ἐν τῇ παρεμβολῇ
28 Sai Yoshuwa ɗan Nun, wanda yake mataimakin Musa tun yana saurayi, ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, Musa, ka hana su!”
καὶ ἀποκριθεὶς Ἰησοῦς ὁ τοῦ Ναυη ὁ παρεστηκὼς Μωυσῇ ὁ ἐκελεκτὸς εἶπεν κύριε Μωυσῆ κώλυσον αὐτούς
29 Amma Musa ya amsa ya ce, “Kana kishi domina ne? Da ma a ce dukan mutanen Ubangiji annabawa ne, da ma a kuma ce Ubangiji ya sa Ruhunsa a kansu mana!”
καὶ εἶπεν αὐτῷ Μωυσῆς μὴ ζηλοῖς σύ μοι καὶ τίς δῴη πάντα τὸν λαὸν κυρίου προφήτας ὅταν δῷ κύριος τὸ πνεῦμα αὐτοῦ ἐπ’ αὐτούς
30 Sai Musa da dattawan Isra’ila suka koma sansani.
καὶ ἀπῆλθεν Μωυσῆς εἰς τὴν παρεμβολήν αὐτὸς καὶ οἱ πρεσβύτεροι Ισραηλ
31 Ana nan, sai Ubangiji ya kawo wata iska mai tsanani ta koro makware daga teku. Ta bar su birjik kewaye da sansani, tsayinsu daga ƙasa ya kai kamu biyu, misalin tafiyar nisan yini guda ta kowace fuska.
καὶ πνεῦμα ἐξῆλθεν παρὰ κυρίου καὶ ἐξεπέρασεν ὀρτυγομήτραν ἀπὸ τῆς θαλάσσης καὶ ἐπέβαλεν ἐπὶ τὴν παρεμβολὴν ὁδὸν ἡμέρας ἐντεῦθεν καὶ ὁδὸν ἡμέρας ἐντεῦθεν κύκλῳ τῆς παρεμβολῆς ὡσεὶ δίπηχυ ἀπὸ τῆς γῆς
32 Dukan yini da dukan dare da kuma kashegari, mutane suka fito suka tattara makware. Ba wanda ya kāsa tara ƙasa da garwa goma. Sai suka shanya abinsu kewaye da sansanin.
καὶ ἀναστὰς ὁ λαὸς ὅλην τὴν ἡμέραν καὶ ὅλην τὴν νύκτα καὶ ὅλην τὴν ἡμέραν τὴν ἐπαύριον καὶ συνήγαγον τὴν ὀρτυγομήτραν ὁ τὸ ὀλίγον συνήγαγεν δέκα κόρους καὶ ἔψυξαν ἑαυτοῖς ψυγμοὺς κύκλῳ τῆς παρεμβολῆς
33 Amma da suna cikin cin naman, tun ba su ma haɗiye ba, sai Ubangiji ya husata sosai a kan jama’ar, ya buge su da annoba mai zafi.
τὰ κρέα ἔτι ἦν ἐν τοῖς ὀδοῦσιν αὐτῶν πρὶν ἢ ἐκλείπειν καὶ κύριος ἐθυμώθη εἰς τὸν λαόν καὶ ἐπάταξεν κύριος τὸν λαὸν πληγὴν μεγάλην σφόδρα
34 Saboda haka aka kira wannan wuri Kibrot Hatta’awa, gama a can ne aka binne mutanen nan makwaɗaita.
καὶ ἐκλήθη τὸ ὄνομα τοῦ τόπου ἐκείνου μνήματα τῆς ἐπιθυμίας ὅτι ἐκεῖ ἔθαψαν τὸν λαὸν τὸν ἐπιθυμητήν
35 Daga Kibrot Hatta’awa, mutane suka yi tafiya zuwa Hazerot, a can suka sauka.
ἀπὸ μνημάτων ἐπιθυμίας ἐξῆρεν ὁ λαὸς εἰς Ασηρωθ καὶ ἐγένετο ὁ λαὸς ἐν Ασηρωθ