< Ƙidaya 10 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa,
וידבר יהוה אל משה לאמר
2 “Ka ƙera kakaki guda biyu na azurfa, ka kuma yi amfani da su don kira taron jama’a wuri ɗaya, don kuma ka riƙa sanar da su lokacin tashi daga sansani.
עשה לך שתי חצוצרת כסף--מקשה תעשה אתם והיו לך למקרא העדה ולמסע את המחנות
3 Sa’ad da aka busa su biyu, dukan jama’a za su taru a gabanka a ƙofar Tentin Sujada.
ותקעו בהן--ונועדו אליך כל העדה אל פתח אהל מועד
4 In ɗaya ne kaɗai aka busa, sai shugabannin kabilan Isra’ila, su taru a gabanka.
ואם באחת יתקעו--ונועדו אליך הנשיאים ראשי אלפי ישראל
5 Sa’ad da aka ji karar busar kakaki, sai sansanin da yake a gabashi, su kama hanya.
ותקעתם תרועה--ונסעו המחנות החנים קדמה
6 A kara ta biyu, sansanin da yake a kudanci, su kama hanya. Busan kakaki zai zama alama ta kama hanya.
ותקעתם תרועה שנית--ונסעו המחנות החנים תימנה תרועה יתקעו למסעיהם
7 In don a tara jama’a ne, sai a busa kakaki, amma ba da irin alama ɗaya ba.
ובהקהיל את הקהל--תתקעו ולא תריעו
8 “’Ya’yan Haruna, firistoci ne, za su busa kakaki. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla gare ku da kuma tsararraki masu zuwa.
ובני אהרן הכהנים יתקעו בחצצרות והיו לכם לחקת עולם לדרתיכם
9 Duk lokacin da za ku tafi yaƙi a ƙasarku, in akwai waɗansu da suke matsa muku, za ku yi amfani da waɗannan kakaki ta wurin hura su, alama ce, cewa za a je yaƙi. Sa’an nan Ubangiji Allahnku zai tuna da ku, yă cece ku daga maƙiyanku.
וכי תבאו מלחמה בארצכם על הצר הצרר אתכם--והרעתם בחצצרת ונזכרתם לפני יהוה אלהיכם ונושעתם מאיביכם
10 Haka ma in kuna cikin jin daɗinku, musamman lokacin da kuke bukukkuwanku, kamar Bikin Sabon Wata da dai kowane Bikinku, za ku hura waɗannan kakaki lokacin da kuke miƙa hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama, za su kuma zama muku abin tunawa a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
וביום שמחתכם ובמועדיכם ובראשי חדשיכם--ותקעתם בחצצרת על עלתיכם ועל זבחי שלמיכם והיו לכם לזכרון לפני אלהיכם אני יהוה אלהיכם
11 A rana ta ashirin ga wata na biyu, a shekara ta biyu, sai girgijen ya tashi daga tabanakul na Shaida.
ויהי בשנה השנית בחדש השני--בעשרים בחדש נעלה הענן מעל משכן העדת
12 Sai Isra’ilawa suka tashi daki-daki daga Hamadar Sinai, suna tafiya daga wuri zuwa wuri, har sai da girgijen ya tsaya a Hamadar Faran.
ויסעו בני ישראל למסעיהם ממדבר סיני וישכן הענן במדבר פארן
13 Suka kama hanya, a wannan lokaci, bisa umarnin Ubangiji, ta wurin Musa.
ויסעו בראשנה על פי יהוה ביד משה
14 Ɓangarorin sansanin Yahuda suka fara tashi, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Nashon ɗan Amminadab ne shugaba.
ויסע דגל מחנה בני יהודה בראשנה--לצבאתם ועל צבאו--נחשון בן עמינדב
15 Netanel ɗan Zuwar ne shugaban ɓangaren kabilar Issakar,
ועל צבא--מטה בני יששכר נתנאל בן צוער
16 Eliyab ɗan Helon kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Zebulun.
ועל צבא--מטה בני זבולן אליאב בן חלן
17 Sa’an nan aka saukar da tabanakul ƙasa, Gershonawa da mutanen Merari da suke ɗauke da shi suka kama hanya.
והורד המשכן ונסעו בני גרשון ובני מררי נשאי המשכן
18 Sai ɓangarori sansanin Ruben suka biyo, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Elizur ɗan Shedeyur ne shugaba.
ונסע דגל מחנה ראובן--לצבאתם ועל צבאו--אליצור בן שדיאור
19 Shelumiyel ɗan Zurishaddai ne shugaban ɓangaren kabilar Simeyon,
ועל צבא--מטה בני שמעון שלמיאל בן צורישדי
20 Eliyasaf ɗan Deyuwel kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Gad.
ועל צבא מטה בני גד אליסף בן דעואל
21 Sai Kohatawa suka kama hanya, ɗauke da kayayyaki masu tsarki, domin kafin su kai wurin da za a kafa sansani, a riga an kafa tabanakul.
ונסעו הקהתים נשאי המקדש והקימו את המשכן עד באם
22 Biye da waɗannan kuma sai ɓangaren sansanin kabilar Efraim suka biyo bisa ga ƙa’ida da aka yi, aka kuma umarta. Elishama ɗan Ammihud ne shugaba.
ונסע דגל מחנה בני אפרים--לצבאתם ועל צבאו--אלישמע בן עמיהוד
23 Gamaliyel ɗan Fedazur ne shugaban ɓangaren kabilar Manasse,
ועל צבא--מטה בני מנשה גמליאל בן פדהצור
24 Abidan ɗan Gideyoni kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Benyamin.
ועל צבא--מטה בני בנימן אבידן בן גדעוני
25 A ƙarshe, a matsayi masu gadin bayan dukan ɓangarori, sai ɓangaren sansanin Dan suka tashi bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Ahiyezer ɗan Ammishaddai ne shugaba.
ונסע דגל מחנה בני דן--מאסף לכל המחנת לצבאתם ועל צבאו--אחיעזר בן עמישדי
26 Fagiyel ɗan Okran ne shugaban ɓangaren kabilan Asher,
ועל צבא--מטה בני אשר פגעיאל בן עכרן
27 Ahira ɗan Enan kuma shi ne shugaban kabilar Naftali.
ועל צבא--מטה בני נפתלי אחירע בן עינן
28 Wannan shi ne tsarin tafiyar ɓangarorin Isra’ilawa, sa’ad da sukan kama hanya.
אלה מסעי בני ישראל לצבאתם ויסעו
29 Sai Musa ya ce wa Hobab ɗan Reyuwel Bamidiyane surukinsa, “Yanzu fa, muna shirin tashi ne daga nan, domin mu tafi inda Ubangiji ya ce, ‘Zan ba ku.’ Ka zo tare da mu, za mu kuwa yi maka alheri, gama Ubangiji ya yi wa Isra’ilawa alkawari abubuwa masu kyau.”
ויאמר משה לחבב בן רעואל המדיני חתן משה נסעים אנחנו אל המקום אשר אמר יהוה אתו אתן לכם לכה אתנו והטבנו לך כי יהוה דבר טוב על ישראל
30 Ya amsa, ya ce “A’a, ba zan tafi ba; zan koma ƙasata da kuma wurin mutanena.”
ויאמר אליו לא אלך כי אם אל ארצי ואל מולדתי אלך
31 Amma Musa ya ce, “Ina roƙonka kada ka rabu da mu. Ka san inda ya kamata mu kafa sansani a hamada, za ka kuma zama idanunmu.
ויאמר אל נא תעזב אתנו כי על כן ידעת חנתנו במדבר והיית לנו לעינים
32 In ka zo tare da mu, za mu raba duk abin alherin Ubangiji ya ba mu tare da kai.”
והיה כי תלך עמנו והיה הטוב ההוא אשר ייטיב יהוה עמנו--והטבנו לך
33 Saboda haka suka kama hanya daga dutsen Ubangiji, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji ya ja gabansu a waɗannan kwanaki uku, don yă samo musu masauƙi.
ויסעו מהר יהוה דרך שלשת ימים וארון ברית יהוה נסע לפניהם דרך שלשת ימים לתור להם מנוחה
34 A duk lokacin da suka tashi daga sansani, girgijen Ubangiji ya inuwantar da su da rana.
וענן יהוה עליהם יומם בנסעם מן המחנה ]
35 Duk kuma sa’ad da akwatin ya kama hanya, sai Musa ya ce, “Ka tashi, ya Ubangiji! Ka sa maƙiyanka su warwatse; masu ƙinka kuma su gudu a gabanka.”
ויהי בנסע הארן ויאמר משה קומה יהוה ויפצו איביך וינסו משנאיך מפניך
36 Duk sa’ad da akwatin ya sauka kuma, sai Musa ya ce, “Ka komo, ya Ubangiji, a wurin dubban da ba a iya ƙidayawa na iyalan Isra’ila.”
ובנחה יאמר שובה יהוה רבבות אלפי ישראל ]

< Ƙidaya 10 >