Aionian Verses

Dukan’ya’yansa maza da mata, suka zo don su ta’azantar da shi, amma ya ƙi yă ta’azantu. Ya ce, “A’a, cikin makoki zan gangara zuwa kabari wurin ɗana.” Saboda haka, mahaifin Yusuf ya yi kuka saboda shi. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Amma Yaƙub ya ce, “Ɗana ba zai gangara zuwa can tare da ku ba, ɗan’uwansa ya rasu, shi ne kaɗai ya rage. In wani abu ya faru da shi a tafiyar da za ku yi, za ku sa furfurata ta gangara zuwa kabari cikin baƙin ciki.” (Sheol h7585)
(parallel missing)
In kun ɗauki wannan daga wurina shi ma wani abu ya same shi, za ku kawo furfura kaina zuwa kabari cikin baƙin ciki.’ (Sheol h7585)
(parallel missing)
ya ga cewa saurayin ba ya nan, zai mutu. Bayinka za su sa bawanka, mahaifinmu, yă mutu cikin baƙin ciki, da tsufansa. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Amma in Ubangiji ya kawo wani abu sabo, ya sa ƙasa ta buɗe bakinta, ta haɗiye su da dukan abin da suke da shi, suka gangara cikin kabari a raye, ta haka za ku sani mutanen nan sun rena Ubangiji.” (Sheol h7585)
(parallel missing)
Suka gangara cikin kabari da rai, tare dukan mallakarsu; ƙasa ta rufe su, suka hallaka, suka rabu da jama’ar. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Gama fushina ya kama wuta, tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za tă cinye duniya da girbinta, tă kuma sa wuta a tussan duwatsu. (Sheol h7585)
(parallel missing)
“Ubangiji ne ke kawo mutuwa, yă kuma rayar yana kai ga kabari, yă kuma tā da. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe ni; tarkuna kuma suka auka mini. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Ka yi da shi gwargwadon hikimarka, amma kada ka bari yă gangara kabari da furfura cikin salama. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Amma yanzu, kada ka ɗauke shi marar laifi. Kai mutum ne mai hikima; za ka san abin da za ka yi da shi. Ka kawo furfuransa zuwa kabari da jini.” (Sheol h7585)
(parallel missing)
Kamar yadda girgije yakan ɓace yă tafi, haka mutum yake shige zuwa kabari ba kuwa zai dawo ba. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Sun fi nisan sama tudu, me za ka iya yi? Sun fi zurfin kabari zurfi, me za ka sani? (Sheol h7585)
(parallel missing)
“Da ma za ka ɓoye ni a cikin kabari ka ɓoye ni har sai fushinka ya wuce! In da za ka keɓe mini lokaci sa’an nan ka tuna da ni! (Sheol h7585)
(parallel missing)
In kabari ne begen da nake da shi kaɗai, in na shimfiɗa gadona a cikin duhu, (Sheol h7585)
(parallel missing)
Ko begena zai tafi tare da ni zuwa kabari ne? Ko tare za a bizne mu cikin ƙura?” (Sheol h7585)
(parallel missing)
Suna yin rayuwarsu cikin arziki kuma su mutu cikin salama. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Kamar yadda zafi da fări suke shanye ƙanƙarar da ta narke, haka kabari zai ƙwace waɗanda suka yi zunubi. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Mutuwa tsirara take a gaban Allah; haka kuma hallaka take a buɗe. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu. Wa ke yabonka daga kabari? (Sheol h7585)
(parallel missing)
Mugaye za su koma kabari, dukan al’umman da suka manta da Allah. (Sheol h7585)
(parallel missing)
domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe kewaye da ni; tarkon mutuwa ya yi mini arangama. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari; ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Kada ka bari in sha kunya, ya Ubangiji, gama na yi kuka gare ka; amma bari mugaye su sha kunya su kuma kwanta shiru a cikin kabari. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari; za su kuwa zama abincin mutuwa amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe. Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari, nesa da gidajensu masu tsada. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. (Sela) (Sheol h7585)
(parallel missing)
Bari mutuwa ta ɗauki abokan gābana ba labari; bari su gangara da rai zuwa cikin kabari, gama mugunta tana samun masauƙi a cikinsu. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Gama ƙaunarka da girma take gare ni; kai ka cece ni daga zurfafa, daga mazaunin matattu. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Gama raina yana cike da wahala rayuwata tana gab da kabari. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Wanda mutum ne zai rayu da ba zai ga mutuwa ba, ko yă cece kansa daga ikon kabari? (Sela) (Sheol h7585)
(parallel missing)
Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni, wahalar kabari sun zo a kaina; na cika da wahala da ɓacin rai. (Sheol h7585)
(parallel missing)
In na haura zuwa sammai, kana a can; in na yi gado a zurfafa, kana a can. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Za su ce, “Kamar yadda mutum kan yi huda yă tsage ƙasa, haka aka watsar da ƙasusuwanmu a bakin kabari.” (Sheol h7585)
(parallel missing)
mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami; (Sheol h7585)
(parallel missing)
Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa; sawunta na jagora kai tsaye zuwa kabari. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Amma ba su san cewa matattu suna a can ba, cewa baƙinta suna a can cikin zurfin kabari ba. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Mutuwa da Hallaka suna nan a fili a gaban Ubangiji, balle fa zukatan mutane! (Sheol h7585)
(parallel missing)
Hanyar rai na yin jagora ya haura wa masu hikima don ta kiyaye shi daga gangarawa zuwa kabari. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Ka hukunta shi da sanda ka ceci ransa daga mutuwa. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Mutuwa da Hallaka ba sa ƙoshi, haka idanun mutum ba sa ƙoshi da gani. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Kabari, mahaifar da ba ta haihuwa, ƙasa, wadda ba ta taɓa ƙoshi da ruwa, da kuma wuta, wadda ba ta taɓa cewa ‘Ya isa!’ (Sheol h7585)
(parallel missing)
Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Ka sa ni kamar hatimi a zuciyarka, kamar hatimi a hannunka; gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa, kishinta yana kamar muguntar kabari, yana ƙuna kamar wuta mai ci, kamar gagarumar wuta. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Saboda haka kabari ya fadada marmarinsa ya kuma buɗe bakinsa babu iyaka; cikinsa manyan mutanensu da talakawansu za su gangara tare da dukan masu hayaniyarsu da masu murnansu. (Sheol h7585)
(parallel missing)
“Ka roƙi Ubangiji Allahnka yă ba ka alama, ko daga zurfafa masu zurfi ko kuwa daga can cikin sama.” (Sheol h7585)
(parallel missing)
Kabari a ƙarƙashi duk ya shirya don yă sadu da kai a zuwanka; yana tā da ruhohin da suka rasu don su gaishe ka, dukan waɗanda sun taɓa zama shugabanni a duniya; ya sa suka tashi daga kujerun sarauta, dukan waɗanda suke sarakuna a kan al’ummai. (Sheol h7585)
(parallel missing)
An yi ƙasa da dukan alfarmarka zuwa kabari, tare da surutan garayunka; tsutsotsi sun bazu a ƙarƙashinka tsutsotsi kuma suka rufe ka. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari, zuwa zurfafan rami. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Kuna fariya cewa, “Mun yi alkawari da mutuwa, mun kuma yi yarjejjeniya da kabari. Sa’ad da zafi ya ratsa, ba zai taɓa mu ba, gama mun mai da ƙarya mafakarmu ruɗu kuma wurin ɓuyanmu.” (Sheol h7585)
(parallel missing)
Za a soke alkawarinku da mutuwa; yarjejjeniyarku da kabari ba zai zaunu ba. Sa’ad da zafi mai ɓarna ya ratsa, zai hallaka ku. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Na ce, “Cikin tsakiyar rayuwata dole in bi ta ƙofofin mutuwa a kuma raba ni da sauran shekaruna?” (Sheol h7585)
(parallel missing)
Gama kabari ba zai yabe ka ba, matattu ba za su rera yabonka ba; waɗanda suka gangara zuwa rami ba za su sa zuciya ga amincinka ba. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Kuka tafi wurin Molek da man zaitun kuka kuma riɓaɓɓanya turarenku. Kuka aika jakadunku can da nisa; kuka gangara zuwa cikin kabari kansa! (Sheol h7585)
(parallel missing)
“‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da aka yi ƙasa da shi zuwa kabari na rufe zurfafa maɓulɓulai da makoki dominsa; na janye rafuffukansa, aka kuma hana yalwan ruwansa. Saboda shi na rufe Lebanon da baƙin ciki, dukan itatuwan kurmi suka bushe. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Na sa al’ummai suka yi rawar jiki da jin ƙarar fāɗuwarsa sa’ad da na yi ƙasa da shi zuwa kabari tare da waɗanda suka gangara rami. Sai dukan itatuwan Eden, zaɓaɓɓu da kuma mafi kyau na Lebanon, dukan itatuwan da aka yi musu banruwa, sun ta’azantu a ƙarƙashin ƙasa. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Waɗanda suka zauna a inuwarsa, dukan masu tarayyarsa a cikin al’ummai, su ma sun gangara zuwa kabari tare da shi, sun haɗu da waɗanda aka kashe da takobi. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Daga cikin kabari manyan shugabanni za su yi maganar Masar da abokanta su ce, ‘Sun gangara sun kuma kwanta da marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi.’ (Sheol h7585)
(parallel missing)
Ba sun kwanta tare da sauran jarumawa marasa kaciyan da aka kashe, waɗanda suka gangara kabari tare da makaman yaƙinsu, waɗanda aka yi musu matashin kai da takubansu ba? Hukuncin zunubansu yana a bisa ƙasusuwansu, ko da yake tsoron waɗannan jarumawa ya manne cikin ƙasar masu rai. (Sheol h7585)
(parallel missing)
“Zan fanshe su daga ikon kabari; zan cece su daga mutuwa. Ina annobanki, ya mutuwa? Ina hallakarka, ya kabari? “Ba zan ji tausayi ba, (Sheol h7585)
(parallel missing)
Ko da sun tona rami kamar zurfin kabari, daga can hannuna zai fitar da su. Ko da sun hau can sama daga can zan sauko da su. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Ya ce, “A cikin damuwata na yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini. Daga cikin zurfi kabari na yi kiran neman taimako, ka kuwa saurari kukata. (Sheol h7585)
(parallel missing)
ba shakka, ruwan inabi ya yaudare shi; yana fariya kuma ba ya hutu. Domin shi mai haɗama ne kamar kabari kuma kamar mutuwa, ba ya ƙoshi; yakan tattara dukan al’ummai wa kansa yana kuma kama dukan mutane su zama kamammu. (Sheol h7585)
(parallel missing)
Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta. (Geenna g1067)
Ki kitan'ĭstopuau annŏk' ksĭstapĭstsĭm'iuōk ox'okoă ai'akesetsĭmaie okŏk'itsĭmani; ki annŏk' ak'anĭstsiuŏk ox'okoa Raca, aiakesetsimaie okok'itsĭmani: ki annŏk' ak'anĭstsiuŏk, kĭtŭt'tsapsi, ai'akesetsĭmaie Gihenni ots'tsiĭmiaie. (Geenna g1067)
In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. (Geenna g1067)
Kinet'oopspi itsuyĭsseeniki, sauau'tos ki mĭs'tŭpapiksĭstsĭs: ŏkh'siu tŭks'kŭma mŏk'saiĭnakuaiĭssi koŏpspi, ŏkstaiĭs'tupapiksĭs kostŭm Gehenna. (Geenna g1067)
In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. (Geenna g1067)
Kinet'otsĭs itsuyĭsse'eniki kawksĭnnĭt', ki mĭs'tŭpapĭxit: ŏkh'siu tuks'kaii kotsĭs'i mŏk'saiĭnakuaiĭssi, ŏkstaiĭs'tŭpapiksĭs kostŭm Gehenna. (Geenna g1067)
Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta. (Geenna g1067)
Ki pinstŭn'nokau anniks'ĭsk akenitomixk mostŭm', ki sta'aw matokotsenĭtsiau'ats: stŭn'nok annŏk' i kots'enĭts iuŏkax mostŭm' ki staaw stakhts'im. (Geenna g1067)
Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaga ki sama ne? A’a, za ki gangara zuwa zurfafa ne. Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne a aka yi a Sodom, da tana nan har yă zuwa yau. (Hadēs g86)
Ki ksĕsto'a Capernaum, kitspĭn'noko spots'im, hades kitaks'ĭnnĭssimoko; omŭk'apotŭksĭsts kitakap'ioyim itap'ĭstutsipiau ittsipstsapistutŭkkiopiau Sodom, ĭs'taisakiaitaitsiopi. (Hadēs g86)
Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa. (aiōn g165)
Annŏk' itŭp'sauokŏmotsepuyiuŏk Nĭn'au Okku'i ak'itsksĭnoau, ki annŏk' itŭpsauokŏmotsepuyiuŏk Atsĭm'iStaaw mat'akitsksĭnoau'ats annom' ksŏk'kum ki aie'nĭssi otsĭs'tŭpipuitappiisĭnni, mat'akitsksĭnoauats. (aiōn g165)
Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi cikin ƙaya kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, sai dai damuwoyin rayuwan nan da jarrabar arzikin duniya sukan shaƙe shi, yă sa maganar ta kāsa amfani. (aiōn g165)
Annŏk' mat'sĭmŏk ĭstsŭpipum'ani ksĭssi'ix, ai'okhtsĭmiu atsĭm'epoawsin; ki annok' pai'tappiisĭnni ĭstap'aitsitani, ki spŭkĭs'sists ito'satstomiauaie atsĭm'epoawsĭnni, ki matsinasiu'ats. (aiōn g165)
abokin gāban da yake shuka su kuwa, Iblis ne. Lokacin girbi kuma shi ne ƙarshen zamani, masu girbin kuwa su ne mala’iku. (aiōn g165)
Katum'a annŏk' ai'sŭppipumattomĕsts, Sauum'itsitappiuă itamiu; pokiak'sĭnni ksŏkkum aiksiuo'si; ki aipo'kiakix, atsĭm'otokatatsĭsau, (aiōn g165)
“Kamar yadda aka tattara ciyayin aka kuma ƙone a wuta, haka zai zama a ƙarshen zamani. (aiōn g165)
Manĭsts'aumoipitŭkkipiau makap'ĭnsĭmmanĭsts ki manĭstse'tsĭnĭtspiau; ak'ŭnĭststsiu aiksiuo'si annom' ksŏk'kum. (aiōn g165)
Haka zai kasance a ƙarshen zamani. Mala’iku za su zo su ware masu mugunta daga masu adalci (aiōn g165)
Ak'otŭmanĭstsiu aiksiuos'i ksŏk'kum: atsĭm'otokatatsix ak'sipuksŭpsŭxiau, ki akai'aketaipiksĭstsiiau Sauum'itsitappix ki mokŏm'otsitappix; (aiōn g165)
Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus, a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hadesba za su rinjaye ta ba. (Hadēs g86)
Ki kita'atanĭsto, ksĕsto'akauk Peter, ki am'om ok'otokŭm nitak'ittokhitokoĭska church; ki Hades istokh'sepĭstanĭsts matakatsiu'atsaie. (Hadēs g86)
In hannunka ko ƙafarka yana sa ka zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da hannu ko ƙafa ɗaya da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu da a jefar da kai cikin madawwamiyar wuta da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu. (aiōnios g166)
Ŭn'nikaie kotsĭs' ki kokŏt'si ĭstsskĭmskŭkiats'otsenikiau, kŏksĭnit'au, ki mĭs'tŭpapiksĭstaiau: itŏkh'siu kŏk'kitsipĭssi opai' tappiisĭnni kŏks'ĭstsekaiisi ki kŏk'opokŏksi, kŏkstaitŭp'apixĭkŏsi kŭttaiaiapunstsiuasi ki kitai'akokŏtsĭsts ki kitai'akŏtsĭsts. (aiōnios g166)
In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta da idanunka biyu. (Geenna g1067)
Ki koŏps'pi ĭstsskĭm'skŭkiatsotseniki, sauau'tos, ki mĭs'tŭpapiksĭstsĭs: itŏkh'siu kŏk'kitsipĭssi opai'tappiisĭnni tuks'kŭm moŏps'pa; kŏkstaitŭp'apixĭkosi kŭt'taiaiapunstsiuasii, ki kitaiakoŏpspix. (Geenna g1067)
To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?” (aiōnios g166)
Ki, sŭppĭt, tuks'kŭmi itsitotoiĭnaie ki an'iu, Ŏkhsĭn'ai, tsanĭstap'iua nŏk'ŏkhsĭstutsipi, nŏkkuinan'si ŭsk'sipaitappiisĭnni? (aiōnios g166)
Duk kuma wanda ya bar gidaje ko’yan’uwa maza ko’yan’uwa mata ko mahaifi ko mahaifiya ko yara ko gonaki, saboda ni, zai sami abin da ya fi haka riɓi ɗari, yă kuma gāji rai madawwami. (aiōnios g166)
Ki anniks'isk skĭm'ixk oko'auĕsts, ki anniks'isk skĭts' ixk umu'pappiipuauax ki ot'akemoauax ki un'oauax, ki oksist'oauax ki otkem'anoauax ki o'kosoauax, kiotsĭn'sĭmmanoauax, nĕsto'i itskĭm' iauĕsts, kepĭp'pi ak'okuyiau, ki akokuinan'attomiau ŭsk'sipaitappiisĭnni. (aiōnios g166)
Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, “Kada ka ƙara yin’ya’ya!” Nan da nan itacen ya yanƙwane. (aiōn g165)
Ki otsĭtsĭnno'ŏsi moksoku'i omŭx'iniĭstsĭsi, itoto'aie ki matsitokonĭmau'atsaie, nam'itaitsii suio'pokĭsts, ki anĭstsiuaie, Ŭnnianĭst'sauŭsksaiĭn as it ksĕsto'a. Ki omŭx'inĭstsĭs sotŭm'ikŭnipisuiu. (aiōn g165)
“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashe, ku ƙetare teku don ku sami mai tuba ɗaya, sa’ad da ya tuba kuwa, sai ku mai da shi ɗan wuta fiye da ku, har sau biyu. (Geenna g1067)
Kitaks'ksĭnipuau maka'pi ksĕsto'au ai'sĭnakix ki Pharisees, kitsiksĭs'tapokŏmotsitappiansuai kitotka'atau ksŏk'kum ki omŭk'sikĭmi kŏk'itokonoŏsi tuks'kŭmă matap'iuă mŏkĭtanĭs'tsitsitasi kanĭstsitsi'tawpi kitaumaitu'yĭssi, kanĭstŭm'ipuai ksĕsto'au Hell oku'yix kitak'anĭstsĭstokiaiĭstutoauau. (Geenna g1067)
“Ku macizai!’Ya’yan macizai! Ta yaya za ku tsere wa hukuncin jahannama ta wuta? (Geenna g1067)
Pitseksĭnax, opĭx'exĭnasĭnna, Tsa'a kitakanĭstupĭs'tapixsattopats Hell ĭstokŏk'itsimani? (Geenna g1067)
Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, “Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?” (aiōn g165)
Otsĭt'tokhitaupĭssi nitum'moyi Olives, ŭsksĭnĭmats'ax isĭmitoto'iauaie, ki an'iau, Anik'ĭnan Tsanĭstsĭs' akanĭstsiu'astsau? Ki tsa akanĭstsiu'a kitsipuksipusĭnni, ki punsksŏk'kuasĭsi? (aiōn g165)
“Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa. (aiōnios g166)
Akotŭm'anĭstsiuax anniks'isk ote'aksĭsautsĭs itau'pixk, ĭs'tapuk emŭtskax mŏkseĭnsau, ŭsksustsinasii ĭs'tapuk, ek'aisepŭtsĭstotomoiiauax au'tutsokiuă ki oto'tokatatsix: (aiōnios g166)
“Sa’an nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami.” (aiōnios g166)
Ki am'oxi aksĭstŭpitappo'iau ŭsk'sĭtauksĭstototspi: ki mokŏm'otsitappix akittappoiau ŭsk'sipaitappiisĭnni. (aiōnios g166)
kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.” (aiōn g165)
Isksĭnĭmats'okau mŏk'satsĭsauĕsts kĭtan'ĭstopuauĕsts; ki sat'sit, kitŭsks'opoksemopuau anĭstsiksĭs'tsikuĭsts aiksiuo'si ksŏk'kum. (aiōn g165)
Amma duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a taɓa gafara masa ba. Ya aikata madawwamin zunubi ke nan.” (aiōn g165, aiōnios g166)
(parallel missing)
amma damuwar wannan duniya, da son dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga, su shaƙe maganar, har su mai da ita marar amfani. (aiōn g165)
(parallel missing)
In hannunka yana sa ka yin zunubi, yanke shi. Ai, gwamma ka shiga rai da hannu ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta, inda ba a iya kashe wutar ba, da hannuwanka biyu. (Geenna g1067)
(parallel missing)
In kuma ƙafarka tana sa ka yin zunubi, yanke ta. Ai, gwamma ka shiga rai da ƙafa ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da ƙafafunka biyu. (Geenna g1067)
(parallel missing)
In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu, (Geenna g1067)
(parallel missing)
Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?” (aiōnios g166)
(parallel missing)
sa’an nan yă kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da’yan’uwa mata, da’yan’uwa maza, da uwaye, da’ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma yă sami rai madawwami. (aiōn g165, aiōnios g166)
(parallel missing)
Sai ya ce wa itacen, “Kada kowa yă ƙara cin’ya’yanka.” Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka. (aiōn g165)
(parallel missing)
zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba.” (aiōn g165)
(parallel missing)
ga Ibrahim da zuriyarsa har abada, kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.” (aiōn g165)
(parallel missing)
(yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki), (aiōn g165)
(parallel missing)
Suka yi ta roƙonsa kada yă umarce su su shiga ramin Abis. (Abyssos g12)
(parallel missing)
Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani za ki sami ɗaukaka ne? A’a, za a hallaka ki. (Hadēs g86)
(parallel missing)
Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don yă gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, “Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?” (aiōnios g166)
(parallel missing)
Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa. (Geenna g1067)
(parallel missing)
“Maigidan kuwa ya yabi manajan nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama’yan duniyan nan suna da wayon yin hulɗa da junansu fiye da’yan haske. (aiōn g165)
(parallel missing)
Ina gaya muku, ku yi amfani da dukiya na wannan duniya, domin ku sami wa kanku abokai. Saboda bayan dukiyar ta ƙare, za a karɓe ku a wuraren zama da sun dawwama. (aiōnios g166)
(parallel missing)
A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa. (Hadēs g86)
(parallel missing)
Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?” (aiōnios g166)
(parallel missing)
da zai kāsa samun riɓi mai yawa, a wannan zamani, ya kuma sami rai madawwami a zamani mai zuwa.” (aiōn g165, aiōnios g166)
(parallel missing)
Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure, (aiōn g165)
(parallel missing)
amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba. (aiōn g165)
(parallel missing)
don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.” (aiōnios g166)
(parallel missing)
Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.” (aiōnios g166)
(parallel missing)
amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Tabbatacce, ruwan da zan ba shi, zai zama masa maɓuɓɓugan ruwa da yake ɓuɓɓugowa har yă zuwa rai madawwami.” (aiōn g165, aiōnios g166)
(parallel missing)
Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare. (aiōnios g166)
(parallel missing)
“Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Kuna ta nazarin Nassosi da himma don kuna tsammani ta wurinsu ne kuna samun rai madawwami. Nassosin nan ne suke ba da shaida a kaina, (aiōnios g166)
(parallel missing)
Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yă zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.” (aiōnios g166)
(parallel missing)
Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.” (aiōnios g166)
(parallel missing)
Gaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.” (aiōn g165)
(parallel missing)
Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Wannan shi ne burodin da ya sauko daga sama. Kakannin-kakanninku sun ci Manna suka kuma mutu, amma duk wanda yake cin wannan burodi zai rayu har abada.” (aiōn g165)
(parallel missing)
Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Bawa dai ba shi da wurin zama na ɗinɗinɗin a cikin iyali, amma ɗa na gida ne har abada. (aiōn g165)
(parallel missing)
Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya kiyaye maganata, ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.” (aiōn g165)
(parallel missing)
Da jin haka Yahudawa suka ce, “Tabɗi, yanzu kam mun san kana da aljani! Ibrahim ya mutu haka ma annabawa, ga shi kana cewa duk wanda ya kiyaye maganarka ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam. (aiōn g165)
(parallel missing)
Ba wanda ya taɓa ji cewa an buɗe idanun wanda aka haifa makaho. (aiōn g165)
(parallel missing)
Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. (aiōn g165, aiōnios g166)
(parallel missing)
kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?” (aiōn g165)
(parallel missing)
Duk mai ƙaunar ransa, zai rasa shi, duk mai ƙin ransa a wannan duniya, zai kiyaye shi har yă zuwa rai madawwami. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Sai taron suka ce, “Ahab, Dokarmu ta gaya mana cewa, Kiristi zai kasance har abada, to, yaya za ka ce, ‘Dole ne a ɗaga Ɗan Mutum?’ Wane ne wannan ‘Ɗan Mutum’?” (aiōn g165)
(parallel missing)
Na san cewa umarninsa yana kai ga rai madawwami. Saboda haka duk abin da na faɗa na faɗe shi ne kamar dai yadda Uba ya ce in faɗa.” (aiōnios g166)
(parallel missing)
Sai Bitrus ya ce, “Faufau, ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba.” Yesu ya amsa ya ce, “Sai na wanke ka, in ba haka ba, ba ka da rabo a gare ni.” (aiōn g165)
(parallel missing)
Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada, (aiōn g165)
(parallel missing)
Gama ka ba shi iko bisa dukan mutane domin yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Rai madawwami kuwa shi ne, su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko. (aiōnios g166)
(parallel missing)
gama ba za ka bar ni cikin kabari ba, ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yă ruɓa ba. (Hadēs g86)
(parallel missing)
Ganin abin da yake gaba, ya yi magana a kan tashin Kiristi daga matattu cewa, ba a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma bai ruɓa ba. (Hadēs g86)
(parallel missing)
Dole yă kasance a sama, sai lokaci ya yi da Allah zai mai da kome sabo, yadda ya yi alkawari tun dā ta wurin annabawansa masu tsarki. (aiōn g165)
(parallel missing)
Sai Bulus da Barnabas suka amsa musu gabagadi, suka ce, “Ya zama mana dole mu yi muku maganar Allah da farko. Da yake kun ƙi ta ba ku kuma ga kun cancanci rai madawwami ba, to, za mu juya ga Al’ummai. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Sa’ad da Al’ummai suka ji haka, sai suka yi farin ciki suka ɗaukaka maganar Ubangiji; kuma duk waɗanda aka zaɓa don samun rai madawwami, suka gaskata. (aiōnios g166)
(parallel missing)
da aka sani tun zamanai. (aiōn g165)
(parallel missing)
Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja. (aïdios g126)
(parallel missing)
Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami. (aiōnios g166)
(parallel missing)
domin, kamar yadda zunubi ya yi mulki cikin mutuwa, haka ma alheri yă yi mulki ta wurin adalci yă kuwa kawo rai madawwami ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Amma a yanzu da aka’yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Kakannin-kakannin nan kuma nasu ne, Kiristi kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
“ko kuwa ‘Wa zai gangara can zurfin ƙasa?’” (wato, don yă hauro da Kiristi daga matattu). (Abyssos g12)
(parallel missing)
Gama Allah ya daure dukan mutane ga rashin biyayya don yă nuna jinƙai ga kowa. (eleēsē g1653)
(parallel missing)
Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance. Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke. (aiōn g165)
(parallel missing)
Ɗaukaka ta tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa’azin Yesu Kiristi, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil azal, (aiōnios g166)
(parallel missing)
amma yanzu kuwa aka bayyana, aka kuma sanar ta wurin rubuce-rubucen annabawa bisa ga umarnin Allah madawwami, domin dukan al’ummai su gaskata su kuma yi masa biyayya (aiōnios g166)
(parallel missing)
ɗaukaka ta tabbata har abada ga Allah, wanda shi ne kaɗai mai hikima ta wurin Yesu Kiristi! Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba? (aiōn g165)
(parallel missing)
Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba. (aiōn g165)
(parallel missing)
A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai. (aiōn g165)
(parallel missing)
Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba. (aiōn g165)
(parallel missing)
Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima. (aiōn g165)
(parallel missing)
Saboda haka, in abin da nake ci zai sa ɗan’uwana yă yi zunubi, ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa shi yă yi tuntuɓe. (aiōn g165)
(parallel missing)
Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana. (aiōn g165)
(parallel missing)
“Ya ke mutuwa, ina nasararki? Ya ke mutuwa, ina dafinki?” (Hadēs g86)
(parallel missing)
Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah. (aiōn g165)
(parallel missing)
Don wannan’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Yanzu mun san cewa in an hallaka tentin duniyan nan da muke ciki, muna da wani gini daga Allah, madawwamin gida a sama, wanda ba da hannuwan mutum ne suka gina shi ba. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ya ba gajiyayyu hannu sake, ayyukansa na alheri madawwama ne.” (aiōn g165)
(parallel missing)
Allah Uban Ubangiji Yesu Kiristi, wanda yabo ta tabbata a gare shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba. (aiōn g165)
(parallel missing)
Shi wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu don yă cece mu daga wannan mugun zamani na yanzu, bisa ga nufin Allah wanda yake kuma Ubanmu, (aiōn g165)
(parallel missing)
a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa. (aiōn g165)
(parallel missing)
Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah. (aiōn g165)
(parallel missing)
Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu. (aiōn g165)
(parallel missing)
An zaɓe ni in bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda Allah, mahaliccin kome, ya ɓoye shekara da shekaru. (aiōn g165)
(parallel missing)
Wannan shi ne madawwamin shirinsa, kuma an aikata shi ta wurin Kiristi Yesu Ubangijinmu. (aiōn g165)
(parallel missing)
Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikkilisiya da kuma a cikin Kiristi Yesu, har yă zuwa dukan zamanai, har abada abadin! Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. (aiōn g165)
(parallel missing)
Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu da Ubanmu har abada abadin. Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
Wannan magana da nake gaya muku asiri ne da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, wanda yanzu aka bayyana ga tsarkaka. (aiōn g165)
(parallel missing)
Za a hukunta su da madawwamiyar hallaka a kuma kau da su daga gaban Ubangiji da kuma daga ɗaukakar ikonsa (aiōnios g166)
(parallel missing)
Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege, (aiōnios g166)
(parallel missing)
Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa. (aiōnios g166)
(parallel missing)
wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. (aiōn g165)
(parallel missing)
wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun fil azal, (aiōnios g166)
(parallel missing)
Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka. (aiōnios g166)
(parallel missing)
gama Demas, saboda ƙaunar wannan duniya, ya yashe ni ya tafi Tessalonika. Kirssens ya tafi Galatiya, Titus kuwa ya tafi Dalmatiya. (aiōn g165)
(parallel missing)
Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi, (aiōnios g166)
(parallel missing)
Yana koya mana mu ce, “A’a” ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani, (aiōn g165)
(parallel missing)
wannan fa domin an kuɓutar da mu ne ta wurin alherinsa, don mu zama magāda masu begen ga rai madawwami. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Wataƙila abin da ya sa aka raba ka da shi na ɗan lokaci ƙanƙani shi ne don ka same shi da amfani (aiōnios g166)
(parallel missing)
amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya. (aiōn g165)
(parallel missing)
Amma game da Ɗan ya ce, “Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin, adalci kuma zai zama sandan mulkinka. (aiōn g165)
(parallel missing)
Ya kuma ya ce a wani wuri, “Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.” (aiōn g165)
(parallel missing)
kuma da aka mai da shi cikakke, sai ya zama hanyar samun madawwamin ceto ga dukan waɗanda suke masa biyayya. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Kuma bai kamata mu ci gaba da koyar da umarnai game da baftisma, ɗibiya hannuwa, tashin matattu, da kuma madawwamin hukunci ba. (aiōnios g166)
(parallel missing)
waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa, (aiōn g165)
(parallel missing)
inda Yesu, wanda ya sha gabanmu, ya shiga a madadinmu. Ya zama babban firist na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek. (aiōn g165)
(parallel missing)
Gama nassi ya ce, “Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.” (aiōn g165)
(parallel missing)
shi wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi da ya ce masa, “Ubangiji ya rantse, ba kuwa zai canja zuciyarsa ba, ‘Kai firist ne na har abada.’” (aiōn g165)
(parallel missing)
amma Yesu ba zai mutu ba, don haka zai zama firist har abada. (aiōn g165)
(parallel missing)
Gama doka takan naɗa babban firist a cikin mutane masu kāsawa; amma rantsuwar da ta zo bayan dokar, ta naɗa Ɗan, wanda aka mai da shi cikakke har abada. (aiōn g165)
(parallel missing)
Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa. (aiōnios g166)
(parallel missing)
balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai! (aiōnios g166)
(parallel missing)
Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Da a ce haka ne, ai, da Kiristi ya sha wahala sau da yawa tun halittar duniya. Amma yanzu ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamanai domin yă kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya. (aiōn g165)
(parallel missing)
Ta wurin bangaskiya ne muka fahimci cewa an halicci duniya bisa ga umarnin Allah, saboda an halicce abin da ake gani daga abin da ba a gani. (aiōn g165)
(parallel missing)
Yesu Kiristi ba ya sākewa, shi ne a jiya, shi ne a yau, shi ne kuma har abada. (aiōn g165)
(parallel missing)
Bari Allah na salama, wanda ta wurin jinin madawwamin alkawari ya tā da Ubangijinmu Yesu daga matattu, wannan Makiyayin tumaki mai girma, (aiōnios g166)
(parallel missing)
yă kintsa ku da kowane abu mai kyau domin aikata nufinsa, bari kuma yă aikata abin da zai gamshe shi cikinmu, ta wurin Yesu Kiristi, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada. Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
Harshe ma wuta ne! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata mutum gaba ɗaya, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa jahannama ce take zuga shi. (Geenna g1067)
(parallel missing)
Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah. (aiōn g165)
(parallel missing)
amma maganar Ubangiji tana nan har abada.” Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi. (aiōn g165)
(parallel missing)
In wani ya yi magana, ya kamata yă yi ta a matsayin wanda yake magana ainihin kalmomin Allah. In wani yana yin hidima, ya kamata yă yi ta da ƙarfin da Allah ya tanadar, domin a cikin kome a yabi Allah ta wurin Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin. Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, yă kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Gare shi bari iko yă tabbata har abada abadin. Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
za ku sami kyakkyawar marabta cikin madawwamin mulkin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Gama in har Allah bai ƙyale mala’iku sa’ad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci; (Tartaroō g5020)
(parallel missing)
Sai dai ku yi girma cikin alheri da sanin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka ta tabbata yanzu da har abada! Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
Wannan Rai ya bayyana, muka kuwa gan shi, muka kuma shaida shi, muna kuwa yin muku shelar wannan rai madawwami, wanda dā yake tare da Uba, ya kuma bayyana a gare mu. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada. (aiōn g165)
(parallel missing)
Wannan shi ne abin da ya yi mana alkawari, wato, rai madawwami. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Duk mai ƙin ɗan’uwansa mai kisankai ne, kun kuma san cewa ba mai kisankan da yake da rai madawwami a cikinsa. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Wannan kuwa ita ce shaidar; cewa Allah ya ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Ina rubuta waɗannan abubuwa gare ku, ku da kuka gaskata sunan Ɗan Allah domin ku san kuna da rai madawwami. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Mun san cewa Ɗan Allah ya zo duniya, ya kuma ba mu ganewa domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna cikinsa, shi da yake Allah na gaskiya wato, cikin Ɗansa Yesu Kiristi. Shi ne Allah na gaskiya da kuma rai na har abada. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Muna ƙaunarku saboda gaskiyan nan, wadda take cikinmu za tă kuma kasance tare da mu har abada. (aiōn g165)
(parallel missing)
Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan. (aïdios g126)
(parallel missing)
Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada. (aiōn g165)
(parallel missing)
Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yă kawo ku ga rai madawwami. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
ya kuma mai da mu masarauta da firistoci don mu yi wa Allahnsa da Ubansa hidima, a gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin! Amin. (aiōn g165)
(parallel missing)
Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades. (aiōn g165, Hadēs g86)
(parallel missing)
Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, (aiōn g165)
(parallel missing)
sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa, (aiōn g165)
(parallel missing)
Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa, “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon yabo da girma da ɗaukaka da iko, (aiōn g165)
(parallel missing)
Na duba, can a gabana kuwa ga ƙodaɗɗen doki! An ba wa mai hawansa suna Mutuwa, Hades kuwa yana biye da shi. Aka ba su iko a kan kashi ɗaya bisa huɗu na duniya don su yi kisa da takobi, yunwa da annoba, har ma da namomin jeji na duniya. (Hadēs g86)
(parallel missing)
suna cewa, “Amin! Yabo da ɗaukaka, da hikima da godiya da girma da iko da ƙarfi sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin. Amin!” (aiōn g165)
(parallel missing)
Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis. (Abyssos g12)
(parallel missing)
Da ya buɗe Abis ɗin, sai hayaƙi ya taso daga cikin kamar hayaƙin matoya mai girma. Hayaƙin nan daga Abis ya duhunta rana da sararin sama. (Abyssos g12)
(parallel missing)
Suna da sarkin da yake mulki a bisansu wanda yake mala’ikan Abis, wanda sunansa a harshen Yahudawa shi ne Abaddon, da harshen Hellenawa kuwa shi ne, Afolliyon. (Abyssos g12)
(parallel missing)
Ya kuma yi rantsuwa da wannan wanda yake raye har abada abadin, wanda ya halicci sammai da dukan abin da yake cikinsu, duniya da dukan abin da yake cikinta, da kuma teku da dukan abin da yake cikinsa, ya kuma ce, “Babu sauran jinkiri! (aiōn g165)
(parallel missing)
To, da suka gama shaidarsu, dabbar da takan fito daga Abis za tă kai musu hari, tă kuwa sha ƙarfinsu tă kuma kashe su. (Abyssos g12)
(parallel missing)
Mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji muryoyi masu ƙarfi a sama da suka ce, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Kiristinsa, zai kuwa yi mulki har abada abadin.” (aiōn g165)
(parallel missing)
Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a. (aiōnios g166)
(parallel missing)
Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.” (aiōn g165)
(parallel missing)
Sai ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai, ya ba wa mala’iku bakwai nan kwanonin zinariya bakwai cike da fushin Allah, wanda yake raye har abada abadin. (aiōn g165)
(parallel missing)
Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za tă kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za tă dawo. (Abyssos g12)
(parallel missing)
Suka sāke tā da murya suka ce, “Halleluya! Hayaƙin yake fitowa daga wurinta ya yi ta tashi sama har abada abadin.” (aiōn g165)
(parallel missing)
Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci. (Limnē Pyr g3041 g4442)
(parallel missing)
Na kuma ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da mabuɗin Abis yana kuma riƙe da ƙaton sarƙa a hannunsa. (Abyssos g12)
(parallel missing)
Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci. (Abyssos g12)
(parallel missing)
Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin. (aiōn g165, Limnē Pyr g3041 g4442)
(parallel missing)
Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. (Hadēs g86)
(parallel missing)
Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. (Hadēs g86, Limnē Pyr g3041 g4442)
(parallel missing)
Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan. (Limnē Pyr g3041 g4442)
(parallel missing)
Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.” (Limnē Pyr g3041 g4442)
(parallel missing)
Ba za a ƙara yin dare ba. Ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su kuwa yi mulki har abada abadin. (aiōn g165)
(parallel missing)

HSA > Aionian Verses: 264
BLF > Aionian Verses: 22