< Nehemiya 5 >

1 To, sai maza da matansu suka tā da fara gunaguni mai tsanani a kan’yan’uwansu Yahudawa.
茲に民その妻とともにその兄弟なるユダヤ人にむかひて大に叫べり
2 Waɗansu suka ce, “Mu da’ya’yanmu maza da mata muna da yawa, muna bukatar hatsi domin mu ci mu rayu.”
或人言ふ我儕および我らの男子女子は多し我ら穀物を得食ふて生ざるべからず
3 Waɗansu kuwa suka ce, “Saboda yunwa mun jinginar da gonakinmu, da gonakin inabinmu, da gidajenmu don mu sami hatsi.”
或人は言ふ我らは我らの田畑葡萄園および家をも質となすなり既に飢に迫れば我らに穀物を獲させよ
4 Har illa yau waɗansu suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu.
或は言ふ我らは我らの田畝および葡萄園をもて金を貸て王の租税を納む
5 Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne,’ya’yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duk da haka an tilasta mu mu sa’ya’yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma an riga an bautar waɗansu daga cikin’ya’yanmu mata, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.”
然ど我らの肉も我らの兄弟の肉と同じく我らの子女も彼らの子女と同じ視よ我らは男子女子を人に伏從はせて奴隷となす我らの女子の中すでに人に伏從せし者もあり如何とも爲ん方法なし其は我らの田畝および葡萄園は別の人の有となりたればなりと
6 Sa’ad da na ji kukansu da waɗannan koke-koke, na husata ƙwarai.
我は彼らの叫および是等の言を聞て大に怒れり
7 Na yi tunaninsu a zuciyata sa’an nan na zargi manyan gari da shugabanni. Na ce musu, “Kuna musguna wa’yan’uwanku ta wurin ba su rance da ruwa!” Saboda haka na kira babban taro gaba ɗaya don a magance wannan.
是において我心に思ひ計り貴き人々および牧伯等を責てこれに言けるは汝らは各々その兄弟より利息を取るなりと而して我かれらの事につきて大會を開き
8 Na ce, “Da dukan iyakar ƙoƙarinmu, mun fanshi’yan’uwanmu Yahudawan da aka sayar wa Al’ummai. Amma ga shi kuna sayar da’yan’uwanku ga Al’ummai, don kawai a sāke sayar mana da su!”
彼らに言けるは我らは異邦人の手に売れたる我らの兄弟ユダヤ人を我らの力にしたがひて贖へり然るにまた汝等は己の兄弟を売んとするやいかで之をわれらの手に売るべけんやと彼らは黙して言なかりき
9 Saboda haka na ci gaba na ce, “Abin da kuke yi a yanzu ba daidai ba ne. Bai kamata ku yi tafiya cikin tsoron Allahnmu don mu guji ba’ar Al’ummai abokan gābanmu ba?
我また言けるは汝らの爲すところ善らず汝らは我らの敵たる異邦人の誹膀をおもひて我儕の神を畏れつつ事をなすべきに非ずや
10 Ni ma da’yan’uwana da kuma mutanena muna ba wa mutane bashin kuɗi da kuma hatsi. Sai mu daina sha’anin ba da rance da ruwa!
我もわが兄弟および僕等も同じく金と穀物とを貸て利息を取ことをなす願くは我らこの利息を廃ん
11 Yau sai ku mayar musu da gonakinsu, da gonakin inabinsu, da na zaitunsu, da gidajensu, da kashi ɗaya bisa ɗari na kuɗi, da na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, waɗanda kuka karɓa a wurinsu.”
請ふ汝ら今日にも彼らの田畝葡萄園橄欖園および家を彼らに還しまた彼らに貸あたへて金穀物および酒油などの百分の一を取ることを廃よと
12 Suka ce, “Za mu mayar musu, kuma ba za mu bukaci wani abu daga gare su ba. Za mu yi yadda ka faɗa.” Sai na tattara firistoci na kuma sa manyan gari da shugabanni su yi rantsuwa don su yi abin da suka yi alkawari.
彼ら即ち言けるは我ら之を還すべし彼らに何をも要めざらん汝の言るごとく我ら然なすべしと是に於て我祭司を呼び彼らをして此言のごとく行なふといふ誓を立しめたり
13 Na kuma kakkaɓe hannuna, na ce, “Duk wanda ya karya wannan alkawari, haka Allah zai kakkaɓe shi daga gidansa da aikinsa. Allah zai kakkaɓe shi, yă wofintar da shi!” Da jin wannan, sai dukan taron suka ce, “Amin,” suka kuma yabi Ubangiji. Mutane kuwa suka yi kamar yadda suka yi alkawari.
而して我わが胸懐を打拂ひて言ふ是言を行はざる者をば臨くは神是のごとく凡て打拂ひてその家およびその業を離れさせたまへ即ちその人は斯打拂はれて空しくなれかしと時に會衆みなアーメンと言てヱホバを讃美せり而して民はこの言のごとくに行へり
14 Ban da haka ma, daga shekara ta ashirin ta Sarki Artazerzes, sa’ad da aka naɗa ni in zama gwamnansu a ƙasar Yahuda, har zuwa shekara ta talatin da biyu na mulkinsa, shekara sha biyu ke nan, ko ni, ko’yan’uwana, ba wanda ya ci abincin da akan ba wa gwamna.
且また我がユダの地の総督に任ぜられし時より即ちアルタシヤユタ王の二十年より三十二年まで十二年の間は我もわが兄弟も総督の受べき禄を食ざりき
15 Amma gwamnonin farko, waɗanda suka riga ni, sun ɗaura wa mutane kaya mai nauyi suka karɓi shekel arba’in na azurfa daga gare su haɗe da abinci da kuma ruwan inabi. Har bayin masu mulki ma sun nawaya wa mutane. Amma ni ban yi haka ba, saboda ina tsoron Allah.
わが以前にありし旧の総督等は民に重荷を負せてパンと酒とを是より取り其外にまた銀四十シケルを取れり然のみならずその僕等も亦民を圧せり然ども我は神を畏るるに因て然せざりき
16 A maimakon haka, na miƙa kaina ga aiki a kan wannan katanga. Na tattara dukan mutanena a can don aikin; ba mu samar wa kanmu wata gona ba.
我は反てこの石垣の工事に身を委ね我儕は何の田地をも買しこと無し我僕は皆かしこに集りて工事をなせり
17 Bugu da ƙari, Yahudawa da shugabanni ɗari da hamsin suna ci daga teburina, haka ma waɗanda suka zo wurinmu daga ƙasashen da suke kewaye.
且また我席にはユダヤ人および牧伯等百五十人あり其外にまた我らの周圍の異邦人の中より我らに來れる者等もありき
18 Kowace rana akan shirya mini saniya ɗaya, zaɓaɓɓun tumaki shida da waɗansu kaji, kuma kowace kwana goma akan tanadar da ruwan inabi na kowane iri a yalwace. Duk da haka, ban taɓa nemi a ba ni abincin da akan ba wa gwamna ba, domin wahala ta yi wa jama’a yawa.
是をもて一日に牛一匹肥たる羊六匹を備へ亦鶏をも許多備へ十日に一回種々の酒を多く備へたり是ありしかどもこの民の役おもきに因て我は総督の受くべき禄を要めざりき
19 Ka tuna da ni, ka yi mini alheri, ya Allah, saboda dukan abubuwan da na yi saboda waɗannan mutane.
わが神よ我が此民のために爲る一切の事を憶ひ仁慈をもて我をあしらひ給へ

< Nehemiya 5 >