< Nehemiya 3 >
1 Eliyashib babban firist da’yan’uwansa firistoci suka tashi suka sāke gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa ƙofofinta a wurarensu, suka yi ginin har Hasumiyar Ɗari, wadda suka tsarkake, da kuma Hasumiyar Hananel.
2 Mutanen Yeriko kuwa suka kama ginin daga mahaɗin, Zakkur ɗan Imri kuma ya fara ginin biye da su.
3 ’Ya’yan Hassenaya ne suka gina Ƙofar Kifi. Suka kafa ginshiƙan, suka kuma sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu.
4 Kusa da su kuma, Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz ne ya yi gyare-gyaren. Biye da shi kuma sai Meshullam ɗan Berekiya, ɗan Meshezabel ya yi gyare-gyare. Kusa da shi Zadok ɗan Ba’ana shi ma ya yi gyare-gyare.
5 Mutanen Tekowa ne suka yi gyare-gyare biye da shi, amma manyan garinsu suka ƙi su sa hannu cikin aikin da shugabanninsu suka bayar.
6 Yohiyada ɗan Faseya, da Meshullam ɗan Besodehiya ne suka gyara Ƙofar Yeshana. Suka kafa katakanta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.
7 Biye da su, mutanen Gibeyon da Mizfa Melatiya na Gibeyon da Yadon Meronot waɗanda suke ƙarƙashin ikon gwamnan Kewayen Kogin Yuferites ne suka yi gyare-gyaren.
8 Uzziyel ɗan Harhahiya, ɗaya daga cikin masu ƙeran zinariya ne ya yi gyare-gyaren sashe na biye; sai Hananiya, ɗaya daga cikin masu yin turare, ya yi gyare-gyaren biye da wannan. Suka gyara Urushalima har zuwa Katanga Mai Faɗi.
9 Refahiya ɗan Hur, mai mulkin rabin yankin Urushalima, ya yi gyare-gyaren sashe na biye.
10 Kusa da Refahiya, Yedahiya ɗan Harumaf ya yi gyare-gyaren daga gaban gidansa, sai Hattush ɗan Hashabnehiya ya yi gyare-gyaren biye da shi.
11 Malkiya ɗan Harim, da Hasshub ɗan Fahat-Mowab ya yi gyare-gyaren wani sashe da kuma Hasumiyar Wurin Gashi.
12 Shallum ɗan Hallohesh, mai mulkin ɗayan rabin yankin Urushalima ya yi gyare-gyaren sashe na biye tare da taimakon’ya’yansa mata.
13 Hanun da mazaunan Zanowa ne suka gyara Ƙofar Kwari. Suka sāke gina ta suka sa ƙofofinta, da sakatunta, da sandunan ƙarfenta a wurarensu. Suka kuma gyara yadi ɗari biyar na katangar har zuwa Ƙofar Juji.
14 Malkiya ɗan Rekab mai mulkin yankin Bet-Hakkerem ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Juji. Ya sāke gina ta ya kuma sa sakatunta, da sanduna ƙarfenta a wurarensu.
15 Shallum ɗan Kol-Hoze mai mulkin Mizfa ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Maɓuɓɓuga. Ya sāke gina ta, ya yi mata jinƙa yana sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu. Ya kuma gyara katangar tafkin Silowam, ta Lambun Sarki, har zuwa matakalan da suka gangara daga Birnin Dawuda.
16 Gaba da shi, Nehemiya ɗan Azbuk, mai mulkin rabin yankin Bet-Zur ne ya yi gyare-gyaren har zuwa kusa da kaburburan Dawuda, har zuwa haƙaƙƙen tafki da kuma Gidan Jarumawa.
17 Biye da shi, Lawiyawa a ƙarƙashin Rehum ɗan Bani ne suka yi gyare-gyaren. Kusa da su, Hashabiya mai mulkin rabin yankin Keyila ne ya yi gyare-gyaren don yankinsa.
18 Biye da shi,’yan’uwansu Lawiyawa ne a ƙarƙashin Binnuyi ɗan Henadad, mai mulkin ɗayan rabin yankin Keyila suka yi gyare-gyaren.
19 Biye da su, Ezer ɗan Yeshuwa, mai mulkin Mizfa, ya yi gyara wani sashe, daga inda yake fuskantar hawan gidan makamai har zuwa kusurwa.
20 Biye da shi, Baruk ɗan Zakkai da ƙwazo ya gyara wani sashe, daga kusurwa zuwa mashigin gidan Eliyashib babban firist.
21 Biye da shi, Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz, ya yi gyaran wani sashe, daga mashigin gidan Eliyashib zuwa ƙarshensa.
22 Firistoci daga kewayen yankin ne suka yi gyare-gyaren biye da shi.
23 Can gaba da su, Benyamin da Hasshub ne suka yi gyare-gyaren a gaban gidansu, biye da su kuwa, Azariya ɗan Ma’asehiya, ɗan Ananiya ne ya yi gyare-gyaren kusa da gidansa.
24 Biye da shi, Binnuyi ɗan Henadad ya yi gyaran wani sashe, daga gidan Azariya zuwa kusurwa,
25 sai Falal ɗan Uzai ya yi aiki ɗaura da kusurwa da kuma doguwar hasumiya daga fadar da take bisa kusa da shirayin masu tsaro. Biye da shi, Fedahiya ɗan Farosh
26 da masu hidimar haikali da suke zama a tudun Ofel ne suka yi gyare-gyaren har zuwa wani wuri ɗaura da Ƙofar Ruwa wajen gabas da kuma doguwar hasumiya.
27 Biye da su, mutanen Tekowa suka yi gyaran wani sashe, daga babbar doguwar hasumiya zuwa katangar Ofel.
28 Daga Ƙofar Doki, firistoci ne suka yi gyare-gyaren, kowanne a gaban gidansa.
29 Biye da su, Zadok ɗan Immer ya yi gyare-gyaren ɗaura da gidansa. Biye da shi, Shemahiya ɗan Shekaniya, mai tsaron Ƙofar Gabas ya yi gyare-gyare.
30 Biye da shi, Hananiya ɗan Shelemiya, da Hanun, ɗa na shida na Zalaf, suka gyara wani sashe. Biye da su, Meshullam ɗan Berekiya ya yi gyare-gyaren ɗaura da wurin zamansa.
31 Biye da shi, Malkiya, ɗaya daga cikin masu ƙera zinariya ya yi gyare-gyaren har zuwa gidan masu hidimar haikali da kuma’yan kasuwa, ɗaura da Ƙofar Bincike, har zuwa ɗakin da yake bisa kusurwar.
32 Maƙeran zinariya da’yan kasuwa suka gyara wani sashi tsakanin ɗakin da yake bisa kusurwa da Ƙofar Tumaki.