< Nehemiya 12 >
1 Waɗannan su ne firistoci da Lawiyawa waɗanda suka komo tare da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da kuma Yeshuwa. Serahiya, Irmiya, Ezra,
И сии суть священницы и левити, возшедшии с Зоровавелем сыном Салафиилевым и Иисусом: Сараиа, Иеремиа, Ездра,
2 Amariya, Malluk, Hattush
Амариа, Малух, Аттуй,
3 Shekaniya, Rehum, Meremot,
Сехениа, Реум, Маримоф,
5 Miyamin, Mowadiya, Bilga,
Миамин, Маадиа, Велга,
6 Shemahiya, Yohiyarib, Yedahiya,
Семиа, Иоиарив, Идиа,
7 Sallu, Amok, Hilkiya da Yedahiya. Waɗannan su ne shugabannin firistoci da’yan’uwansu a kwanakin Yeshuwa.
Салуй, Амук Хелкиа, Одуиа: сии началницы священников и братия их во дни Иисуса.
8 Lawiyawan su ne Yeshuwa, Binnuyi, Kadmiyel, Sherebiya, Yahuda, da kuma Mattaniya, wanda tare da’yan’uwansa yake lura da waƙoƙin godiya.
И левити: Иисус, Вануй, Кадмиил, Саравиа, Иодай и Матфаниа, при руках той, и братия их в чредныя служения:
9 Bakbukiya da Unni,’yan’uwansu sun tsaya ɗaura da su a hidimomi.
и Ваквакиа и Анай, братия их, прямо их во чреды дневныя.
10 Yeshuwa ne mahaifin Yohiyakim, Yohiyakim shi ne mahaifin Eliyashib, Eliyashib shi ne mahaifin Yohiyada,
Иисус же роди Иоакима, Иоаким роди Елиасива, Елиасив роди Иодаа,
11 Yohiyada shi ne mahaifin Yonatan, Yonatan kuma mahaifin Yadduwa.
Иодай же роди Ионафана, и Ионафан роди Адуа.
12 A kwanakin Yohiyakim, waɗannan su ne shugabannin iyalan firistoci, na iyalin Serahiya, Merahiya; na iyalin Irmiya, Hananiya;
Во дни же Иоакима беху братия его священницы и началницы отечеств: Сараии Амариа, Иеремии Ананиа,
13 na iyalin Ezra, Meshullam; na iyalin Amariya, Yehohanan;
Ездре Месуллам, Амарии Иоанан,
14 na iyalin Malluk, Yonatan; na iyalin Shebaniya, Yusuf;
Амалуху Ионафан, Сехении Иосиф,
15 na iyalin Harim, Adna; na iyalin Merahiyot, Helkai;
Аресу Еднас, Мариофу Елкей,
16 na iyalin Iddo, Zakariya; na iyalin Ginneton, Meshullam;
Аддаю Захариа, Ганафону Месуллам,
17 na iyalin Abiya, Zikri; na iyalin Miniyamin da na Mowadiya, Filtai;
Авии Зехрий, Миамину Маадай, Фелетию,
18 na iyalin Bilga, Shammuwa; na iyalin Shemahiya, Yehonatan;
Валгасу Самуей, Семии Ионафан,
19 na iyalin Yohiyarib, Mattenai; na iyalin Yedahiya, Uzzi;
Иоариву Матфанай, Едию Озий,
20 na iyalin Sallu, Kallai; na iyalin Amok, Eber;
Салаию Калаиа, Амеку Авед,
21 na iyalin Hilkiya, Hashabiya; na iyalin Yedahiya, Netanel.
Елкии Асавиа, Иедии Нафанаил.
22 Shugabannin iyalin Lawiyawa a kwanakin Eliyashib, Yohiyada, Yohanan da Yadduwa, da kuma na firistoci, an rubuta su a zamanin mulkin Dariyus mutumin Farisa.
Левити во дни Елиасива, Иоада и Иоа, и Иоанан и Идуа, написани началницы отечеств, и священницы в царство Дариа Персскаго.
23 Shugabannin iyali cikin zuriyar Lawi har zuwa lokacin Yohanan ɗan Eliyashib, an rubuta su a cikin littafin tarihi.
И сынове Левии началницы отечеств писани в книзе словес дний и даже до дний Иоанана сына Елисуева.
24 Shugabannin Lawiyawa kuwa su ne Hashabiya, Sherebiya, Yeshuwa ɗan Kadmiyel, da’yan’uwansu, waɗanda suka tsaya ɗaura da su don su yi yabo da kuma godiya, sashe ɗaya kan ba da amsa ga ɗaya sashen, kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.
И началницы левитом Асавиа и Саравиа и Иисус, и сынове Кадмииловы и братия их пред ними в песнех хвалити и исповедовати, по заповеди Давида человека Божия, по чредам от дне до дне.
25 Mattaniya, Bakbukiya, Obadiya, Meshullam, Talmon da Akkub su ne matsaran ƙofofi waɗanda suka yi tsaron ɗaukan ajiya a ƙofofi.
Матфаниа и Ваквакиа, Авдиа, Месуллам, Телмон, Акув, стрегущии дверницы стражу, внегда собрати ми дверники.
26 Sun yi hidima a kwanakin Yohiyakim ɗan Yeshuwa, ɗan Yozadak, kuma a kwanakin Nehemiya gwamna da kuma na Ezra firist da kuma marubuci.
Во дни Иоакима сына Иисусова, сына Иоседекова, и во дни Неемии и Ездры священника и книгочии,
27 A keɓewar katangar Urushalima, an nemi Lawiyawa daga inda suke zama aka kawo su Urushalima don su yi bikin miƙawa da farin ciki da waƙoƙin godiya da kuma kiɗin kuge, garaya da molo.
и во обновлении стены Иерусалимския, взыскаша левитов в местех их да возведут их во Иерусалим сотворити обновление и веселие во хвалении и песнех, в кимвалех и псалтирех и гуслех.
28 Aka kuma tattara mawaƙa su ma daga yankin kewayen Urushalima, daga ƙauyukan Netofawa,
И собрашася сынове поющих и от страны окрестныя во Иерусалим, и от сел Нетофатиевых,
29 daga Bet-Gilgal, da kuma daga wuraren Geba da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima.
и от Дому (Галгал) и от стран (Гева и Азмавет), яко села создаша себе певцы окрест Иерусалима:
30 Sa’ad da firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu da tsarki, sai suka tsarkake mutane, ƙofofi da kuma katanga.
и очистишася священницы и левити, и очистиша людий и врата и стену.
31 Sai na sa shugabannin Yahuda suka haura zuwa bisan katangar. Na kuma sa manyan ƙungiyoyi biyu na mawaƙa su miƙa godiya. Ɗaya ya haura zuwa bisan katangar zuwa dama, wajen Ƙofar Juji.
И возведох началников Иудиных на стену, и поставих два клироса велика, хвалы ради, и проидоша от десныя страны на стену ко вратом Гнойным.
32 Hoshahiya da rabin shugabannin Yahuda kuwa suka bi su,
И идоша за ними Осаиа и половина началников Иудиных,
33 tare da Azariya, Ezra, Meshullam,
и Азариа и Ездра и Месуллам,
34 Yahuda, Benyamin, Shemahiya, Irmiya,
Иуда и Вениамин, и Самаиа и Иеремиа:
35 da waɗansu firistoci kuma da ƙahoni, da kuma Zakariya ɗan Yonatan, ɗan Shemahiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mikahiya, ɗan Zakkur, ɗan Asaf,
и от сынов священничих с трубами Захариа сын Ионафанов, сын Самаии, сын Мафаниин, сын Михаин, сын Закхуров, сын Асафов,
36 da’yan’uwansa, Shemahiya, Azarel, Milalai, Gilalai, Ma’ai, Netanel, Yahuda da Hanani, tare da kayan kiɗi da Dawuda mutumin Allah ya umarta. Ezra malamin Doka ya jagoranci jerin gwanon.
и братия его Самаиа и Озиил, Гелол, Маиа, Нафанаил и Иуда и Ананий, еже хвалити в песнех Давида человека Божия:
37 A Ƙofar Maɓuɓɓuga suka ci gaba kai tsaye suka haura matakalan Birnin Dawuda a kan hawa zuwa katangar suka wuce a bisa gidan Dawuda zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas.
и Ездра книгочий пред ними при вратех Источника, хвалити прямо их. И взыдоша на лествицы града Давидова, на восход стены выше дому Давидова и даже до врат Водных к востоку.
38 Ƙungiyar mawaƙa ta biyu suka yi jerin gwano a ɗaya gefen. Na bi su a bisan katangar, tare da rabin mutanen, muka wuce Hasumiya Tanderu zuwa Katanga Mai Faɗi,
И клирос вторый хвалу воздающих идяше сопротив их, и аз по нем, и половина людий по стене, верху столпа Фануримля и даже до стены пространнейшия,
39 bisa Ƙofar Efraim, Ƙofar Yeshana, Ƙofar Kifi, Hasumiyar Hananel da kuma Hasumiya ɗari, har zuwa Ƙofar Tumaki. A Ƙofar Matsara suka tsaya.
и на врата Ефраима, и на врата старая, и на врата Рыбная, и на столп Анамеиль, и на столп Емаф, и даже до врат Овчих.
40 Ƙungiyoyin mawaƙa biyu da suka yi godiya suka ɗauki wurarensu a gidan Allah, haka ma ni, tare da rabin shugabanni,
И сташа на вратех Стражи, сташа же два клироса хваляща в дому Божии, и аз и половина воевод со мною,
41 da kuma firistoci, Eliyakim, Ma’asehiya, Miniyamin, Mikahiya, Eliyohenai, Zakariya da Hananiya tare da ƙahoninsu,
и священницы Елиаким, Маасиа, Миамин, Михеа, Елиона, Захариа, Ананиа с трубами,
42 haka ma Ma’asehiya, Shemahiya, Eleyazar, Uzzi, Yehohanan, Malkiya, Elam da Ezer. Mawaƙan suka rera waƙoƙi a ƙarƙashin kulawar Yezrahiya.
и Маасиа и Семеиа, и Елеазар и Озиа, и Иоанан и Мелхиа, и Елеамий и Иезур. И слышани быша певцы и Иезриа, и соглядани, и восхвалиша.
43 A rana ta uku kuma suka miƙa manyan hadayu, suna farin ciki domin Allah ya ba su farin ciki mai girma. Mata da yara suka yi farin ciki su ma. An ji ƙarar farin ciki da ake yi a Urushalima daga nesa.
И пожроша в день той жертвы великия и возвеселишася, яко Бог возвесели их вельми: и жены их и чада их радовахуся, и слышано бысть веселие то во Иерусалиме издалеча.
44 A lokacin an naɗa mutane su lura da ɗakunan ajiya don sadakoki, nunan fari da kuma zakka. Daga gonakin garuruwan da suke kewaye za su kawo sassan da Dokar ta umarta zuwa ɗakunan ajiya domin firistoci da Lawiyawa, gama Yahuda ya ji daɗin aikin firistoci da Lawiyawa.
И поставиша в день той мужей над сокровищными хранилищи, на начатки и десятины, и да собирают сими началниками от градов части священником и левитом, яко веселие бе во Иудеи, во священницех и в левитех предстоящих,
45 Sun yi hidimar Allahnsu da kuma hidimar tsarkakewa, kamar yadda mawaƙa da matsaran ƙofofi suka yi, bisa ga umarnin Dawuda da ɗansa Solomon.
и стрежаху стражу Бога своего, и хранение очищения, и певцев и дверников, по повелению Давида и Соломона сына его.
46 Gama tun dā, a kwanakin Dawuda da Asaf, akwai masu bi da mawaƙa da kuma na waƙoƙin yabo da na godiya ga Allah.
Яко во дни Давидовы Асаф от начала первый в певцех и в песнех и хвалении Богу,
47 Saboda haka a kwanakin Zerubbabel da Nehemiya, dukan Isra’ila suka ba da sashe na kowace rana domin mawaƙa da matsaran ƙofofi. Suka kuma keɓe sashe don sauran Lawiyawa, Lawiyawan kuma suka keɓe sashe don zuriyar Haruna.
и весь Израиль во дни Зоровавеля и во дни Неемии даяху оброк певцем и дверником от дне до дне и освящаху левитом, левити же освящаху сыновом Аароним.