< Nehemiya 10 >

1 Waɗanda suka buga hatimin su ne, Nehemiya ɗan Hakaliya, wanda yake gwamna. Zedekiya
ועל החתומים נחמיה התרשתא בן חכליה וצדקיה׃
2 da Serahiya, da Azariya, da Irmiya,
שריה עזריה ירמיה׃
3 da Fashhur, da Amariya, da Malkiya,
פשחור אמריה מלכיה׃
4 da Hattush, da Shebaniya, da Malluk,
חטוש שבניה מלוך׃
5 da Harim, da Meremot, da Obadiya,
חרם מרמות עבדיה׃
6 da Daniyel, da Ginneton, da Baruk,
דניאל גנתון ברוך׃
7 da Meshullam, da Abiya, da Miyamin,
משלם אביה מימן׃
8 da Ma’aziya, da Bilgai, da kuma Shemahiya. Waɗannan su ne Firistocin.
מעזיה בלגי שמעיה אלה הכהנים׃
9 Lawiyawan kuwa su ne, Yeshuwa ɗan Azaniya, da Binnuyi ɗan Henadad, da Kadmiyel,
והלוים וישוע בן אזניה בנוי מבני חנדד קדמיאל׃
10 ’yan’uwansu kuwa su ne, Shebaniya, da Hodiya, da Kelita, da Felahiya, da Hanan,
ואחיהם שבניה הודיה קליטא פלאיה חנן׃
11 da Mika, da Rehob, da Hashabiya,
מיכא רחוב חשביה׃
12 da Zakkur, da Sherebiya, da Shebaniya,
זכור שרביה שבניה׃
13 da Hodiya, da Bani da kuma Beninu.
הודיה בני בנינו׃
14 Shugabannin mutane su ne, Farosh, da Fahat-Mowab, da Elam, da Zattu, da Bani,
ראשי העם פרעש פחת מואב עילם זתוא בני׃
15 da Bunni, da Azgad, da Bebai,
בני עזגד בבי׃
16 da Adoniya, da Bigwai, da Adin,
אדניה בגוי עדין׃
17 da Ater, da Hezekiya, da Azzur,
אטר חזקיה עזור׃
18 da Hodiya, da Hashum, da Bezai,
הודיה חשם בצי׃
19 da Harif, da Anatot, da Nebai,
חריף ענתות נובי׃
20 da Magfiyash, da Meshullam, da Hezir,
מגפיעש משלם חזיר׃
21 da Meshezabel, da Zadok, da Yadduwa
משיזבאל צדוק ידוע׃
22 da Felatiya, da Hanan, da Anahiya,
פלטיה חנן עניה׃
23 da Hosheya, da Hananiya, da Hasshub,
הושע חנניה חשוב׃
24 da Hallohesh, da Filha, da Shobek,
הלוחש פלחא שובק׃
25 da Rehum, da Hashabna, da Ma’asehiya
רחום חשבנה מעשיה׃
26 da Ahiya, da Hanan, da Anan,
ואחיה חנן ענן׃
27 da Malluk, da Harim da kuma Ba’ana.
מלוך חרם בענה׃
28 “Sauran mutane, wato, firistoci, Lawiyawa, matsaran ƙofofi, mawaƙa, ma’aikatan haikali da dukan waɗanda suka ware kansu daga maƙwabta saboda Dokar Allah, tare da matansu da dukan’ya’yansu maza da mata waɗanda za su iya fahimta,
ושאר העם הכהנים הלוים השוערים המשררים הנתינים וכל הנבדל מעמי הארצות אל תורת האלהים נשיהם בניהם ובנתיהם כל יודע מבין׃
29 dukan waɗannan yanzu suka sadu da manyan gari’yan’uwansu, suka rantse, cewa la’ana ta same su idan ba su kiyaye Dokar Allah da aka bayar ta wurin Musa bawan Allah su kuma mai da hankali ga yin biyayya da dukan umarnai, ƙa’idodi da farillan Ubangiji shugabanmu ba.
מחזיקים על אחיהם אדיריהם ובאים באלה ובשבועה ללכת בתורת האלהים אשר נתנה ביד משה עבד האלהים ולשמור ולעשות את כל מצות יהוה אדנינו ומשפטיו וחקיו׃
30 “Mun yi alkawari ba za mu ba da’ya’yanmu mata aure ga mutanen da suke kewaye da mu ba, ba kuwa za mu auri’ya’yansu mata wa’ya’yanmu maza ba.
ואשר לא נתן בנתינו לעמי הארץ ואת בנתיהם לא נקח לבנינו׃
31 “Sa’ad da maƙwabta suka kawo kayayyaki ko hatsi don su sayar a ranar Asabbaci, ba za mu saya daga gare su a ranar Asabbaci ko a rana mai tsarki ba. Kowace shekarar Asabbaci ba za mu nome ƙasa ba kuma za mu yafe kowane irin bashi.
ועמי הארץ המביאים את המקחות וכל שבר ביום השבת למכור לא נקח מהם בשבת וביום קדש ונטש את השנה השביעית ומשא כל יד׃
32 “Mun ɗauka hakkin bin umarnai na ba da kashi ɗaya bisa uku na shekel kowace shekara don hidimar gidan Allahnmu.
והעמדנו עלינו מצות לתת עלינו שלשית השקל בשנה לעבדת בית אלהינו׃
33 Za mu tanada burodin da ake ajiye a kan tebur; za mu ba da hadayun hatsi da hadayun ƙonawa na kullum; za mu ba da hadayun Asabbatai, da na bukukkuwan Sabon Wata da na bukukkuwan da aka ƙayyade; za mu ba da hadayu masu tsarki; za mu ba da hadayun zunubi don a yi kafara domin Isra’ila; mu kuma ba da abubuwan da ake bukata dukan domin ayyukan gidan Allahnmu.
ללחם המערכת ומנחת התמיד ולעולת התמיד השבתות החדשים למועדים ולקדשים ולחטאות לכפר על ישראל וכל מלאכת בית אלהינו׃
34 “Mu, firistoci, da Lawiyawa da kuma mutane, mun jefa ƙuri’a don a san lokacin da kowane iyalinmu zai kawo sadakar itace don ƙonewa a gidan Allahnmu a ƙayyadaddun lokuta a bagaden Ubangiji Allahnmu, kamar yadda yake a rubuce a cikin Doka.
והגורלות הפלנו על קרבן העצים הכהנים הלוים והעם להביא לבית אלהינו לבית אבתינו לעתים מזמנים שנה בשנה לבער על מזבח יהוה אלהינו ככתוב בתורה׃
35 “Mun kuma ɗauka hakkin kawo nunan fari na hatsinmu da kuma na kowane itace mai ba da’ya’ya a gidan Ubangiji kowace shekara.
ולהביא את בכורי אדמתנו ובכורי כל פרי כל עץ שנה בשנה לבית יהוה׃
36 “Kamar yadda yake a rubuce a cikin Doka, za mu kawo ɗan fari na’ya’yanmu maza da na garken shanunmu, da na tumakinmu, da kuma na awakinmu a gidan Allahnmu, don firistocin da suke aikin a can.
ואת בכרות בנינו ובהמתינו ככתוב בתורה ואת בכורי בקרינו וצאנינו להביא לבית אלהינו לכהנים המשרתים בבית אלהינו׃
37 “Ban da haka ma, za mu kawo wa ɗakunan ajiyar gidan Allahnmu, abincinmu na farko daga ƙasa, na hadayun hatsinmu, na’ya’yan dukan itatuwanmu da kuma na sabon ruwan inabinmu da mai namu wa firistoci. Za mu kuma kawo zakkar hatsinmu wa Lawiyawa, gama Lawiyawa ne ke karɓan Zakka cikin dukan garuruwan da muke noma.
ואת ראשית עריסתינו ותרומתינו ופרי כל עץ תירוש ויצהר נביא לכהנים אל לשכות בית אלהינו ומעשר אדמתנו ללוים והם הלוים המעשרים בכל ערי עבדתנו׃
38 Firist wanda yake daga zuriyar Haruna zai raka Lawiyawa sa’ad da suke karɓan zakka, Lawiyawan kuma za su kawo kashi ɗaya bisa goma na zakka zuwa gidan Allahnmu, su kawo a ɗakunan ajiya na baitulmali.
והיה הכהן בן אהרן עם הלוים בעשר הלוים והלוים יעלו את מעשר המעשר לבית אלהינו אל הלשכות לבית האוצר׃
39 Mutanen Isra’ila haɗe da Lawiyawa, za su kawo sadakokinsu na hatsi, sabon ruwan inabi da mai a ɗakunan ajiya inda ake ajiyar kayayyakin wuri mai tsarki da kuma inda firistoci, matsaran ƙofofi da kuma mawaƙa suke zama. “Ba za mu ƙyale gidan Allahnmu ba.”
כי אל הלשכות יביאו בני ישראל ובני הלוי את תרומת הדגן התירוש והיצהר ושם כלי המקדש והכהנים המשרתים והשוערים והמשררים ולא נעזב את בית אלהינו׃

< Nehemiya 10 >