< Nahum 2 >
1 Mai hari yana matsowa a kanki, Ninebe. Ki tsare mafaka, ki yi gadin hanya ki sha ɗamara ki tattaro dukan ƙarfinki!
尼尼微啊,那打碎邦國的上來攻擊你。 你要看守保障,謹防道路, 使腰強壯,大大勉力。 (
2 Ubangiji zai maido da darajar Yaƙub, kamar ta Isra’ila, ko da yake masu washewa sun washe su suka kuma lalatar da inabinsu.
耶和華復興雅各的榮華, 好像以色列的榮華一樣; 因為使地空虛的, 已經使雅各和以色列空虛, 將他們的葡萄枝毀壞了。)
3 Garkuwoyin sojojinsa ja wur ne; jarumawansa suna sanye da kaya masu ruwan jan garura. Ƙarafan kekunan yaƙi suna walƙiya a ranar da aka shirya su; ana kaɗa māsu da bantsoro.
他勇士的盾牌是紅的, 精兵都穿朱紅衣服。 在他預備爭戰的日子, 戰車上的鋼鐵閃爍如火, 柏木把的槍也掄起來了。
4 Kekunan yaƙi sun zabura a tituna, suna kai da kawowa a dandali. Suna walƙiya kamar tocila suna sheƙawa a guje kamar walƙiya.
車輛在街上急行, 在寬闊處奔來奔去, 形狀如火把, 飛跑如閃電。
5 Ninebe ta tattara rundunarta, duk da haka sun yi ta tuntuɓe a kan hanyarsu. Sun ruga zuwa katangan birnin, sun sanya garkuwar kāriya a inda ya kamata.
尼尼微王招聚他的貴冑; 他們步行絆跌, 速上城牆,預備擋牌。
6 An buɗe ƙofofin rafuffukan sai wurin ya rurrushe.
河閘開放,宮殿沖沒。
7 An umarta cewa birnin za tă tafi bauta, za a kuma yi gaba da su. Bayi’yan mata suna kuka kamar tattabaru suna buga ƙirjinsu.
王后蒙羞,被人擄去; 宮女搥胸,哀鳴如鴿。 此乃命定之事。
8 Ninebe tana kama da tafki, wanda ruwanta yana yoyo. Suna kuka suna cewa, “Ku tsaya! Ku tsaya,” amma ba wanda ya waiga.
尼尼微自古以來充滿人民, 如同聚水的池子; 現在居民卻都逃跑。 雖有人呼喊說:站住!站住! 卻無人回顧。
9 A washe azurfa; a washe zinariya; dukiyarsu ba ta da iyaka, arzikinsu kuma ba ya ƙarewa.
你們搶掠金銀吧! 因為所積蓄的無窮, 華美的寶器無數。
10 Ta zama wofi, an washe ta, an tuɓe ta! Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa, jikuna suna rawa, fuskoki duk sun kwantsare!
尼尼微現在空虛荒涼, 人心消化,雙膝相碰, 腰都疼痛,臉都變色。
11 Ina kogon zakokin nan yake yanzu, inda suka ciyar da’ya’yansu, inda zaki da zakanya sukan shiga, da’ya’yansu, ba mai damunsu
獅子的洞和少壯獅子餵養之處在哪裏呢? 公獅母獅小獅遊行、無人驚嚇之地在哪裏呢?
12 Zaki ya kashe abin da ya ishe’ya’yansa ya kuma murɗe wuyan dabbobi ya cika wurin zamansa da abin da ya kama ya cika kogwanninsa da abin da ya kashe.
公獅為小獅撕碎許多食物, 為母獅掐死活物, 把撕碎的、掐死的充滿牠的洞穴。
13 “Ina gāba da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan ƙone kekunan yaƙinki, takobi kuma zai fafare’ya’yan zakokinki. Ba kuma zan bar miki namun jejin da za ki kashe a duniya ba. Ba kuwa za a ƙara jin muryar’yan saƙonki ba.”
萬軍之耶和華說:「我與你為敵,必將你的車輛焚燒成煙,刀劍也必吞滅你的少壯獅子。我必從地上除滅你所撕碎的,你使者的聲音必不再聽見。」