< Nahum 1 >
1 Jawabi game da Ninebe a littafin wahayin Nahum, mutumin Elkosh.
A message about Nineveh, a vision which came to Nahum from Elkosh.
2 Ubangiji Allah mai kishi ne, mai sakayya kuma. Ubangiji Allah mai kishi ne, mai ɗaukar fansa kuma. Ubangiji yakan ɗauki fansa a kan maƙiyansa, yakan ci gaba da fushi a kan abokan gābansa.
The Lord tolerates no rivals. The Lord is vengeful and fierce in wrath. The Lord does not fail to punish his foes; the Lord is vengeful against his enemies.
3 Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai iko duka kuma. Ubangiji ba zai bar masu zunubi babu horo ba. Hanyarsa tana cikin guguwa da kuma hadari, gizagizai kuwa su ne ƙurar ƙafafunsa.
The Lord is slow to anger, great in power. The guilty will not escape his punishment. Storm tempest is his path and cloud is the dust of his feet.
4 Yakan tsawata wa teku yă kuma busar da shi; yakan sa dukan koguna su kafe. Bashan da Karmel sun yi yaushi tohon Lebanon kuma ya koɗe.
He rebukes the sea and dries it up and makes all the streams run dry. Bashan and Carmel are languishing and the bloom of Lebanon is withered.
5 Duwatsu suna rawan jiki a gabansa tuddai kuma sun narke. Duniya da dukan abin da yake cikinta suna rawan jiki a gabansa.
The mountains tremble before him and the hills dissolve. The earth heaves before him, the world and all who live in it.
6 Wa zai iya tsaya wa fushinsa? Wa yake da ikon jimre wa zafin hasalarsa? Ana zuba fushinsa kamar wuta; aka kuma ragargaza duwatsu a gabansa.
Who can stand before his wrath? Who can withstand the heat of his anger? His fierce fury pours forth like fire, he shatters rocks.
7 Ubangiji nagari ne, mafaka kuma a lokacin wahala. Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,
The Lord is good to those who hope in him, a place of refuge in the day of trouble.
8 amma da ambaliyar ruwa zai kawo Ninebe ga ƙarshe; zai fafari maƙiyansa zuwa cikin duhu.
With rushing flood an end he makes of those who rise against him, he drives his enemies into darkness.
9 Dukan abin da suke ƙullawa game da Ubangiji zai kawo ga ƙarshe; wahala ba za tă sāke komowa ƙaro na biyu ba.
Why do you plot against the Lord? He will end you. He only takes vengeance once.
10 Za su sarƙafe a ƙaya, za su kuma bugu da ruwan inabinsu; za a laƙume su kamar busasshiyar ciyawa.
Thorns, tangled and drenched, they are consumed like dry stubble.
11 Daga cikinki, ya Ninebe wani ya fito wanda ya ƙulla wa Ubangiji makirci yana ba da mugayen shawarwari.
Nineveh! From you has arisen one who plots evil against the Lord, a counsellor of wickedness.
12 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Ko da yake sun yi tarayya, suna kuma da yawa, za a yanke su, a kawar a su. Ko da yake na ba ki azaba, ya Yahuda, ba zan ƙara ba ki azaba ba.
The Lord says: “Though they are many and strong, they will pass away and be gone. Though I have afflicted you, I will afflict you no more,
13 Yanzu zan karya karkiyarsu daga wuyanki in kuma tsittsinke sarƙar da suka ɗaura ki.”
and now I will break his yoke from your necks and snap your chains.”
14 Ubangiji ya ba da umarni game da ke Ninebe, “Ba za ki sami zuriyar da za tă ci gaba da sunanki ba. Zan rurrushe siffofin da kuka sassaƙa da kuma gumakan da kuka ƙera gumakan da suke a cikin haikalin allolinku. Zan shirya kabarinki, domin ke muguwa ce.”
The Lord has given this command concerning you, Nineveh: “Your name will no longer be remembered. I will destroy every idol and image in the house of your God. I will destroy even your tomb, for you are worthless.”
15 Duba, can a bisa duwatsu, ga ƙafafu mai kawo labari mai daɗi, wanda yake shelar salama! Ki yi bukukkuwanki, ya Yahuda, ki kuma cika wa’adodinki. Mugaye ba za su ƙara mamaye ki ba; domin za a hallaka su ƙaƙaf.
Look! On the mountains a messenger bringing good news, announcing peace! “Celebrate the feasts, Judah, fulfill your vows. Never again will these enemies invade your land, they are destroyed!”