< Mika 1 >

1 Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce.
דבר יהוה אשר היה אל מיכה המרשתי בימי יותם אחז יחזקיה מלכי יהודה--אשר חזה על שמרון וירושלם
2 Ku ji, ya ku mutane duka, ki saurara, ya ke duniya da dukan mazauna cikinki, bari Ubangiji Mai Iko Duka yă zama shaida a kanku, daga haikalinsa mai tsarki.
שמעו עמים כלם הקשיבי ארץ ומלאה ויהי אדני יהוה בכם לעד אדני מהיכל קדשו
3 Duba! Ubangiji yana zuwa daga wurin zamansa; zai sauko yă taka maɗaukakan wuraren duniya.
כי הנה יהוה יצא ממקומו וירד ודרך על במותי (במתי) ארץ
4 Duwatsu za su narke a ƙarƙashin ƙafafunsa, kamar kaki a gaban wuta, kwaruruka kuma za su ɓace, kamar ruwan da yake gangarowa daga tsauni.
ונמסו ההרים תחתיו והעמקים יתבקעו כדונג מפני האש כמים מגרים במורד
5 Duk wannan zai faru saboda laifin Yaƙub, da kuma zunuban gidan Isra’ila ne. Mene ne laifin Yaƙub? Shin, ba Samariya ba ce? Ina ne maɗaukakan wuraren Yahuda? Shin, ba Urushalima ba ce?
בפשע יעקב כל זאת ובחטאות בית ישראל מי פשע יעקב הלוא שמרון ומי במות יהודה הלוא ירושלם
6 “Saboda haka zan mai da Samariya tarin juji, wurin noman inabi. Zan zubar da duwatsunta a cikin kwari in kuma bar harsashin gininta a bayyane.
ושמתי שמרון לעי השדה למטעי כרם והגרתי לגי אבניה ויסדיה אגלה
7 Za a ragargaje dukan allolinta; za a ƙone dukan baye-bayenta na haikali da wuta; zan lalatar da dukan gumakanta. Tun da ta wurin karuwanci ne ta tattara su, ga karuwanci kuma za su koma.”
וכל פסיליה יכתו וכל אתנניה ישרפו באש וכל עצביה אשים שממה כי מאתנן זונה קבצה ועד אתנן זונה ישובו
8 Saboda wannan zan yi baƙin ciki, in yi kuka; zan yi tafiya ba takalmi, zan tuɓe, in kuma yi tafiya tsirara. Zan yi kuka kamar dila, in yi baƙin ciki kamar mujiya.
על זאת אספדה ואילילה אילכה שילל (שולל) וערום אעשה מספד כתנים ואבל כבנות יענה
9 Gama raunin Samariya ba mai warkewa ba ne; ya bazu har Yahuda. Ya ma kai bakin ƙofar mutanena, har ma Urushalima da kanta.
כי אנושה מכותיה כי באה עד יהודה--נגע עד שער עמי עד ירושלם
10 Kada a faɗe shi a Gat; kada ma a yi kuka. A maimako haka, a yi birgima a cikin ƙura a Bet-Leyafra.
בגת אל תגידו--בכו אל תבכו בבית לעפרה עפר התפלשתי (התפלשי)
11 Ku wuce tsirara da kuma kunya, ku mazaunan Shafir. Bet-Ezel tana makoki domin babu wani daga Za’anan da ya fito don yă taimaka.
עברי לכם יושבת שפיר עריה בשת לא יצאה יושבת צאנן--מספד בית האצל יקח מכם עמדתו
12 Mazaunan Marot sun ƙosa su ga alheri, amma Ubangiji ya sauko da azaba, har zuwa ƙofar Urushalima.
כי חלה לטוב יושבת מרות כי ירד רע מאת יהוה לשער ירושלם
13 Ku da kuke zama a Lakish, ku ɗaura wa dawakai kekunan yaƙi. Gama ku kuka fara yin zunubi a Sihiyona, gama an sami laifofin Isra’ila a cikinku.
רתם המרכבה לרכש יושבת לכיש ראשית חטאת היא לבת ציון כי בך נמצאו פשעי ישראל
14 Saboda haka za ku ba da kyautan bankwana ga Moreshet Gat. Garin Akzib zai zama abin yaudara ga sarakunan Isra’ila.
לכן תתני שלוחים על מורשת גת בתי אכזיב לאכזב למלכי ישראל
15 Ku mazaunan Maresha Ubangiji zai kawo wanda zai ci ku da yaƙi. Sarakunan Isra’ila za su gudu zuwa Adullam.
עד הירש אבי לך יושבת מרשה עד עדלם יבוא כבוד ישראל
16 Ku aske kanku ƙwal don makoki, ku yi wa kanku ƙwalƙwal kamar ungulu. Gama za a ja’ya’yan da kuke farin ciki a kai su bauta.
קרחי וגזי על בני תענוגיך הרחבי קרחתך כנשר כי גלו ממך

< Mika 1 >