< Mika 7 >

1 Tawa ta ƙare! Ina kama da wanda yake tattara’ya’yan itatuwa a lokacin kalar’ya’yan inabi; babu sauran nonon inabin da za a tsinka a ci, babu kuma’ya’yan ɓaure na farko-farkon da raina yake marmari.
我有禍了! 因為我變成了一個夏季搜摘果實,採集殘餘葡萄的人,卻沒有一粒葡萄可吃,也沒有我心思所想望的早熟的無花果。
2 An kawar da masu tsoron Allah daga ƙasar; babu sauran mai adalcin da ya rage. Dukan mutane suna kwanto don su zub da jini; kowa yana farautar ɗan’uwansa da tarko.
虔敬人從地上消逝了,人間竟沒有一個正直人;人人都潛伏著要流人血,各以羅網獵取自己的弟兄。
3 Dukan hannuwansu sun gwaninta wajen yin mugunta; shugabanni suna nema a ba su kyautai, alƙalai suna nema a ba su cin hanci, masu iko suna faɗar son zuciyarsu, duk suna ƙulla makirci tare.
他們的手善於作惡,官員貪求賄賂,法官勒索酬金,權貴只隨自己的心願發言,他們顛倒了一切。
4 Mafi kyau a cikinsu yana kama da ƙaya, mafi gaskiyarsu ya fi shingen ƙaya muni. Ranar da Allah zai ziyarce ku ta zo, ranar da masu gadinku za su hura ƙaho. Yanzu ne lokacin ruɗewarku.
他們中最好的人也不過相似荊棘,最正直的人也不過相似有刺的籬笆。你的守望者所宣佈的懲罰之日已經到了;現在他們必要驚惶。
5 Kada ka yarda da maƙwabci; kada ka sa begenka ga abokai. Ko ma wadda take kwance a ƙirjinka, ka yi hankali da kalmominka.
你們不要信賴鄰里;不要倚靠朋友,連對躺在你懷中的妻子,也也要堅守口舌,
6 Gama ɗa yakan ce wannan ba mahaifinsa ba ne, diya kuma takan tayar wa mahaifiyarta, matar ɗa takan yi gāba da uwar mijinta, abokan gāban mutum su ne iyalin cikin gidansa.
因為兒子要侮辱自己的父親,女兒要反抗自己的母親,兒媳要違抗自己的婆母:人的仇敵就是自己的家人。
7 Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji, ina sauraron Allah Mai Cetona; Allahna kuwa zai ji ni.
至於我,我要仰望上主,寄望於拯救我的天主;天主必要俯聽我。
8 Kada ku yi farin ciki, ku maƙiyana! Ko da yake na fāɗi, zan tashi. Ko da yake na zauna a cikin duhu, Ubangiji zai zama haskena.
我的仇敵! 你不要因我遭難而高興;我雖然跌倒,必再起來;我雖坐在黑暗中,但上主是我的光明。
9 Domin na yi masa zunubi, zan fuskanci fushin Ubangiji, har sai ya dubi batuna ya kuma tabbatar da’yancina. Zai kawo ni zuwa wurin haske; zan ga adalcinsa.
因為我得罪了上主,我必須承擔上主的義怒,直到衪審判我的案件,為我主持公道,衪必領 進入光明,我必能目睹衪的正義。
10 Sa’an nan maƙiyina zai gani yă kuma sha kunya, shi da yake ce da ni “Ina Ubangiji Allahnka?” Zai gani, yă kuma ji kunya. Ko yanzu ma za a tattake shi kamar taɓo a tituna.
我的仇敵見了,必要蒙受羞辱,因為他曾對我說:「上主你的天主在哪裏﹖」我的眼必要看見他,有如街上的污泥被人踐踏。
11 Ranar gina katangarka tana zuwa, a ranar za a fadada iyakokinka.
必有一天,要重建你的城垣;那一天,你的地界必要擴展;
12 A wannan rana mutane za su zo gare ka daga Assuriya da kuma biranen Masar, daga Masar ma har zuwa Yuferites daga teku zuwa teku, kuma daga dutse zuwa dutse.
那一天,從亞述到埃及,從提洛到幼發的河,從這海到那海,從這山到那山的人民,都要向你歸來;
13 Duniya za tă zama kufai saboda mazaunanta, saboda ayyukansu.
其餘的地域,必因其中居民行為的惡果,變為一片荒涼。
14 Ka yi kiwon mutanenka da sandarka, garken gādonka, wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi, a ƙasa mai kyau ta kiwo, bari su yi kiwo a Bashan da Gileyad kamar a kwanakin dā.
上主,求你拿你的牧杖牧放你的人民──獨留在草莽中,在田園間,作你基業的羊群;讓他們在巴商和基肋阿得獲得豢養,一如昔日。
15 “Kamar a kwanakin da kuka fito daga Masar, zan nuna musu al’ajabaina.”
上主一如讓我們在你出離埃及的時日內,見到奇蹟;
16 Al’ummai za su gani su kuma ji kunya, za a kuma ƙwace musu dukan ikonsu. Za su kama bakinsu kunnuwansu kuma za su zama kurame.
讓異民見了,感到自己一籌莫展,棎自慚愧,用手掩口,雙耳變聾。
17 Za su lashi ƙura kamar maciji, kamar dabbobi masu rarrafe a ƙasa. Za su fito daga maɓuyarsu da rawan jiki, za su juya cikin tsoro ga Ubangiji Allahnmu su kuma ji tsoronku.
他們將舔土如蛇,像上爬行的爬蟲,戰戰兢兢地從他們洞穴裏爬出來,向你,上主我們的天主,表示尊敬敬畏。
18 Wane ne Allah kamar ka, wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu? Ba ka zama mai fushi har abada amma kana marmari ka nuna jinƙai.
哪裏有神相似你,赦免罪惡,寬宥他的基業──遺民的過錯,不堅時憤怒於永遠,反而喜愛仁慈﹖
19 Za ka sāke jin tausayinmu; za ka tattake zunubanmu a ƙarƙashin sawunka ka kuma tura dukan kurakuranmu zuwa cikin zurfafan teku.
你必再憐憫我們,將我們的邪惡踏於足下,將我們的一切罪過投入海底。
20 Za ka yi wa Yaƙub aminci, ka kuma nuna jinƙai ga Ibrahim, kamar yadda ka yi alkawari da rantsuwa ga kakanninmu tun a kwanankin dā.
你必按照你昔日向我們祖先所發了的誓,對雅各伯表示忠信,對亞巴郎施行仁慈。

< Mika 7 >