< Mika 5 >

1 Ki tattara sojojinki, ya ke birnin mayaƙa, gama an kewaye mu da yaƙi. Za su bugi kumatun mai mulkin Isra’ila da sandar ƙarfe.
Yet now gather yourselves in troops, O people of troops! They lay siege against us; With a rod they smite the cheek of the judge of Israel.
2 “Amma ke, Betlehem ta Efrata, ko da yake ke ƙarama ce daga cikin zuriyarki a Yahuda, daga cikinki wani zai zo domina wanda zai yi mulkin Isra’ila, wanda asalinsa tun fil azal ne.”
But thou, Bethlehem Ephratah, Who art small to be among the thousands of Judah, Out of thee shall he come forth for me to be ruler in Israel, Whose origin is from the ancient age, from the days of old!
3 Saboda haka za a yashe Isra’ila har sai wadda take naƙuda ta haihu sauran’yan’uwansa kuma sun dawo su haɗu da Isra’ilawa.
But He [[Jehovah]] shall deliver them up, Until she that bringeth forth hath brought forth; Then shall the residue of his brethren return to the children of Israel.
4 Zai tsaya yă yi kiwon garkensa da ƙarfin Ubangiji, cikin girman sunan Ubangiji Allahnsa. Za su kuma zauna lafiya, gama girmansa za tă kai har ƙarshen duniya.
He shall stand and rule in the strength of Jehovah, In the majesty of Jehovah, his God; And they shall dwell in security, For he shall be great even to the ends of the earth.
5 Zai kuma zama salamarsu. Sa’ad da Assuriyawa suka kawo wa ƙasarmu hari suka tattake kagarunmu, za mu tā da makiyaya bakwai, har ma shugabannin mutane takwas su yi gāba da su.
And he shall be peace. When the Assyrian shall come into our land, To trample upon our palaces, Then shall we raise against him seven shepherds, And eight leaders of the people,
6 Za su yi mulkin ƙasar Assuriya da takobi, ƙasar Nimrod kuma da zaran takobi. Zai cece mu daga hannun Assuriyawa sa’ad da suka kawo wa ƙasarmu hari suka kuma tattake zuwa cikin iyakokinmu.
And they shall devour the land of Assyria with the sword, The land of Nimrod within her gates. Thus shall he deliver us from the Assyrian, when he cometh into our land, And treadeth in our borders.
7 Raguwar Yaƙub za tă kasance a tsakiyar mutane masu yawa kamar raɓa daga Ubangiji, kamar yayyafi a kan ciyawa, wanda ba ya jiran mutum ko kuma yă dakata wa ɗan adam.
The residue of Jacob shall be in the midst of many nations As the dew which cometh from Jehovah, As drops of rain upon the grass, Which tarrieth not for man, Nor waiteth for the sons of men.
8 Raguwar Yaƙub za tă kasance tare da al’ummai, a cikin mutane masu yawa, kamar zaki a cikin sauran namun jeji, kamar ɗan zaki cikin garken tumaki, wanda yake tattaka yă kuma yi kaca-kaca da su sa’ad da yake ratsa a cikinsu, ba kuwa wanda zai cece su.
The residue of Jacob shall be among the nations, In the midst of many kingdoms, As a lion among the beasts of the forest, As a young lion among flocks of sheep, Who, when he assaulteth, treadeth down and teareth, and none can deliver.
9 Za a ɗaga hannunka cikin nasara a kan abokan gābanka, za a hallaka maƙiyanka duka.
Thy hand shall be lifted up over thine adversaries, And all thine enemies shall be destroyed!
10 “A wannan rana,” in ji Ubangiji “Zan hallaka dawakanku daga cikinku, in kuma rurrushe kekunan yaƙinku.
It shall come to pass in that day, saith Jehovah, That I will destroy thy horses from the midst of thee, And I will consume thy chariots;
11 Zan hallaka biranen ƙasarku in yi rugu-rugu da dukan katangunku.
I will destroy the fortified cities of thy land, And throw down all thy strongholds;
12 Zan kawar da maitarku, ba za a ƙara yin sihiri ba.
I will destroy sorceries from thy borders, And soothsayers shall not be with thee.
13 Zan sassare dukan gumakan da kuka sassaƙa da keɓaɓɓun duwatsunku a cikinku, nan gaba ba za ku ƙara rusuna wa aikin hannuwanku ba.
I will destroy thy graven images and thy statues from the midst of thee, And thou shalt no more bow down to the work of thine hands;
14 Zan tumɓuke daga gare ku ginshiƙan Asheranku in kuma rurrushe biranenku.
I will root out thy Astartes from the midst of thee, And I will destroy thy fortified cities;
15 Zan yi ramuwa cikin fushi da hasala a kan al’umman da ba su yi mini biyayya ba.”
And I will execute vengeance in anger and in fury Upon the nations which have not hearkened to me.

< Mika 5 >