< Mika 4 >
1 A kwanakin ƙarshe za a kafa dutsen haikalin Ubangiji yă zama babba a cikin duwatsu. Za a ɗaga shi sama da tuddai, mutane kuma za su riƙa ɗunguma zuwa gare shi.
2 Al’ummai da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, don mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Doka za tă fita daga Sihiyona, maganar Ubangiji kuma daga Urushalima.
3 Zai shari’anta tsakanin mutane yă kuma sulhunta tsakanin manyan al’ummai nesa da kuma kusa. Har su mai da takubansu su zama garemani, māsunsu kuma su zama wuƙaƙen askin itace. Al’umma ba za tă ɗauki takobi gāba da wata al’umma ba, ko a yi horarwa don yaƙi.
4 Kowa zai zauna a tushen kuringar inabinsa da tushen ɓaurensa, kuma ba wanda zai tsoratar da su, gama Ubangiji Maɗaukaki ne ya faɗa.
5 Dukan al’ummai za su iya tafiya a cikin sunan allolinsu; mu dai za mu yi tafiya a cikin sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin.
6 “A wannan rana,” in ji Ubangiji, “zan tattara guragu; zan kuma tara masu zaman bauta, da waɗanda na sa suka damu.
7 Zan mai da guragu su zama raguwa, waɗanda aka kora, su zama al’umma mai ƙarfi. Ubangiji zai yi mulkinsu a Dutsen Sihiyona daga wannan rana da kuma har abada.
8 Game da ke, ya hasumiyar tsaron garke, Ya mafaka Diyar Sihiyona, za a maido miki da mulkinki na dā, sarauta kuma za tă zo wa Diyar Urushalima.”
9 Don me yanzu kike kuka da ƙarfi, ba ki da sarki ne? Masu shawararki sun hallaka ne, da zafi ya cika ki kamar mace mai naƙuda?
10 Ki yi birgima cikin zafin azaba, ya Diyar Sihiyona, kamar macen da take naƙuda, don yanzu dole ki bar birni ki kafa sansani a filin Allah. Za ki tafi Babilon; a can za a kuɓutar da ki. A can ne Ubangiji zai fanshe ki daga hannun maƙiyanki.
11 Amma yanzu al’ummai da yawa suna gāba da ke. Suna cewa, “Bari a ƙazantar da ita, bari mu zuba wa Sihiyona ido.”
12 Amma ba su san tunanin Ubangiji ba; ba su fahimci shirinsa ba, shi da ya tattara su kamar dammuna a masussuka.
13 “Ki tashi ki yi sussuka, ya Diyar Sihiyona, gama zan ba ki ƙahonin ƙarfe; zan ba ki kofatan tagulla domin ki ragargaje al’ummai masu yawa.” Za ki ba Ubangiji dukan dukiyarsu da suka tara ta hanyar zamba, wadatarsu kuma ga Ubangiji dukan duniya.