< Mika 2 >
1 Taku ta ƙare, ku da kuke shirya makirci, ku da kuke ƙulle-ƙullen mugunta a kan gadonku! Da gari ya waye sai ku fita ku aikata mugunta domin ikon aikatawa yana hannunku.
2 Kukan yi ƙyashin gonaki ku kuma ƙwace su, ku yi ƙyashin gidaje ku kuma ƙwace. Kukan zalunci mutum, ku ƙwace masa gidansa, har ku ƙwace masa gādonsa.
3 Saboda haka, Ubangiji ya ce, “Ina shirya wa waɗannan mutane bala’i, yadda ba za ku iya ceton kanku ba. Ba za ku ƙara tafiya kuna taƙama ba, gama zai zama lokacin bala’i ne.
4 A wannan rana mutane za su yi muku ba’a za su yi muku gwalo da wannan waƙar makoki, ‘An lalatar da mu sarai; an rarraba mallakar mutanena. Ya ɗauke shi daga gare ni! Ya miƙa filayenmu ga maciyan amanarmu.’”
5 Saboda haka ba za ku kasance da wani a taron jama’ar Ubangiji da zai raba ƙasar ta wurin jefa ƙuri’a ba.
6 “Kada ku yi annabci” in ji annabawansu. “Kada ku yi annabci game da waɗannan abubuwa; abin kunya ba zai same mu ba.”
7 Daidai ne a ce, ya gidan Yaƙub, “Ruhun Ubangiji yana fushi ne? Yana yin irin waɗannan abubuwa?” “Ashe, maganata ba tă amfane wanda ayyukansa suke daidai ba?
8 Ba da daɗewa ba mutanena sun tashi kamar magabci. Kun tuɓe riga mai tsada daga waɗanda suke wucewa ba tare da kun damu ba, sai ka ce mutanen da suke komowa daga yaƙi.
9 Kun kori matan mutanena daga gidajensu masu daɗi. Kuka kawar da albarkata har abada daga wurin’ya’yansu.
10 Ku tafi, ku ba ni wuri! Gama wannan ba wurin hutunku ba ne, gama ya ƙazantu, ya zama kangon da ya wuce gyara.
11 In maƙaryaci da mazambaci ya zo ya ce, ‘Zan yi muku annabci ku sami wadataccen ruwan inabi da barasa,’ zai dai zama annabin da ya dace da wannan mutane ne!
12 “Tabbatacce zan tattara ku duka, ya gidan Yaƙub; zan tattara ku raguwar Isra’ila. Zan kawo su wuri ɗaya kamar tumaki a cikin garke, kamar garke a wajen kiwonsa; wurin zai cika da mutane.
13 Wanda ya fasa ƙofa ya buɗe, shi zai haura yă yi musu jagora, za su fashe bangon su fita. Sarkinsu zai wuce gabansu, Ubangiji kuma zai kasance a gaba.”