< Mattiyu 9 >

1 Yesu ya shiga jirgin ruwa, ya ƙetare ya zo garinsa.
I ušavši u lađu, preplovi i dođe u svoj grad.
2 Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Kada ka damu saurayi, an gafarta maka zunubanka.”
Kad gle, doniješe mu uzetoga koji je ležao na nosiljci. Vidjevši njihovu vjeru, reče Isus uzetomu: “Hrabro, sinko, otpuštaju ti se grijesi!”
3 Da jin wannan, waɗansu malaman dokoki suka ce wa juna, “Wannan mutum yana yin saɓo!”
A gle, neki od pismoznanaca rekoše u sebi: “Ovaj huli!”
4 Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, “Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku?
Prozrevši njihove misli, Isus reče: “Zašto snujete zlo u srcima?
5 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya?’
Ta što je lakše reći: 'Otpuštaju ti se grijesi' ili reći: 'Ustani i hodi'?
6 Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”
Ali da znate: vlastan je Sin Čovječji na zemlji otpuštati grijehe!” Tada reče uzetomu: “Ustani, uzmi nosiljku i pođi kući!”
7 Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida.
I on usta te ode kući.
8 Da taron suka ga haka, sai suka cika da tsoro, suka yabi Allah wanda ya ba wa mutane irin ikon nan.
Kad mnoštvo to vidje, zaprepasti se i poda slavu Bogu koji takvu vlast dade ljudima.
9 Da Yesu ya yi gaba daga wurin, sai ya ga wani mutum mai suna Mattiyu zaune a inda ake karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Mattiyu kuwa ya tashi ya bi shi.
Odlazeći odande, ugleda Isus čovjeka zvanog Matej gdje sjedi u carinarnici. I kaže mu: “Pođi za mnom!” On usta i pođe za njim.
10 Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Mattiyu, masu karɓar haraji da yawa da kuma masu zunubi suka zo suka kuwa ci tare da shi da kuma almajiransa.
Dok je Isus bio u kući za stolom, gle, mnogi carinici i grešnici dođoše za stol s njime i njegovim učenicima.
11 Sa’ad da Farisiyawa suka ga haka, sai suka tambayi almajiransa suka ce, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji, da masu zunubi?”
Vidjevši to, farizeji stanu govoriti: “Zašto vaš učitelj jede s carinicima i grešnicima?”
12 Da jin wannan, Yesu ya ce, “Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya.
A on, čuvši to, reče: “Ne treba zdravima liječnika, nego bolesnima.
13 Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”
Hajdete i proučite što znači: Milosrđe mi je milo, a ne žrtva. Ta ne dođoh zvati pravednike, nego grešnike.”
14 Sai almajiran Yohanna suka zo suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa mu da Farisiyawa muke azumi, amma almajiranka ba sa yi?”
Tada pristupe k njemu Ivanovi učenici govoreći: “Zašto mi i farizeji postimo, a učenici tvoji ne poste?”
15 Yesu ya amsa ya ce, “Yaya baƙin ango za su yi makoki yayinda yake tare da su? Lokaci yana zuwa da za a ɗauke ango daga gare su, sa’an nan za su yi azumi.
Nato im Isus reče: “Mogu li svatovi tugovati dok je s njima zaručnik? Doći će već dani kad će im se ugrabiti zaručnik, i tada će postiti!”
16 “Ba mai yin faci da sabon ƙyalle a kan tsohuwar riga, gama facin zai kece rigar yă sa kecewar ma ta fi ta dā muni.
“A nitko ne stavlja krpe od sirova sukna na staro odijelo, jer zakrpa vuče s odijela pa nastane još veća rupa.”
17 Mutane kuma ba sa zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In suka yi haka, salkunan za su farfashe, ruwan inabin kuwa yă zube salkunan kuma su lalace. A’a, ai, sukan zuba sabon ruwan inabi ne a cikin sababbin salkuna, don a kiyaye dukan biyun.”
“I ne ulijeva se novo vino u stare mješine. Inače se mješine proderu, vino prolije, a mješine propadnu. Nego, novo se vino ulijeva u nove mješine pa se oboje sačuva.”
18 Yayinda yake faɗin wannan, sai wani mai mulki ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Yanzu-yanzu diyata ta rasu. Amma ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, za tă kuwa rayu.”
Dok im on to govoraše, gle, pristupi neki glavar, pokloni mu se do zemlje i reče: “Kći mi, evo, umrije, ali dođi, stavi ruku na nju, i oživjet će.”
19 Yesu ya tashi ya tafi tare da shi, haka ma almajiransa.
Isus usta te s učenicima pođe za njim.
20 A daidai wannan lokaci sai ga wata mace wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini ta raɓo ta bayansa ta taɓa gefen rigarsa.
I gle, neka žena koja bolovaše dvanaest godina od krvarenja priđe odostraga i dotaknu se skuta njegove haljine.
21 Ta ce a ranta, “Ko da rigarsa ce kawai na taɓo, zan warke.”
Mislila je: “Dotaknem li se samo njegove haljine, spasit ću se.”
22 Yesu ya juya ya gan ta. Sai ya ce, “Kada ki damu diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take macen ta warke.
A Isus se okrenu i vidjevši je reče: “Hrabro, kćeri, vjera te tvoja spasila.” I žena bi spašena od toga časa.
23 Da Yesu ya shiga gidan mai mulkin ya ga masu busan sarewa da taro mai hayaniya,
I uđe Isus u kuću glavarovu. Ugleda svirače i bučno mnoštvo pa
24 sai ya ce, “Ku ba da wuri. Ai, yarinyar ba tă mutu ba, tana barci ne.” Amma suka yi masa dariya.
reče: “Odstupite! Djevojka nije umrla, nego spava.” Oni mu se podsmjehivahu.
25 Bayan an fitar da taron waje, sai ya shiga ciki ya kama yarinyar a hannu, ta kuwa tashi.
A kad je svijet bio izbačen, uđe on, primi djevojku za ruku i ona bi uskrišena.
26 Labarin wannan kuwa ya bazu ko’ina a yankin.
I razglasi se to po svem onom kraju.
27 Da Yesu ya fita daga can, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna kira, suna cewa, “Ka yi mana jinƙai, Ɗan Dawuda!”
Kad je Isus odlazio odande, pođu za njim dva slijepca vičući: “Smiluj nam se, Sine Davidov!”
28 Da ya shiga cikin gida, sai makafin nan suka zo wurinsa, ya kuma tambaye su, “Kun gaskata cewa ina iya yin wannan?” Suka amsa suka ce, “I, Ubangiji.”
A kad uđe u kuću, pristupe mu slijepci. Isus im kaže: “Vjerujete li da mogu to učiniti?” Kažu mu: “Da, Gospodine!”
29 Sa’an nan ya taɓa idanunsu ya ce, “Bisa ga bangaskiyarku a yi muku haka”;
Tada se dotače njihovih očiju govoreći: “Neka vam bude po vašoj vjeri.”
30 sai idanunsu suka buɗe. Yesu ya gargaɗe su sosai ya ce, “Ku lura kada wani yă san wani abu game da wannan.”
I otvoriše im se oči. A Isus im poprijeti: “Pazite da nitko ne dozna!”
31 Amma suka fita suka yi ta baza labari game da shi ko’ina a wannan yankin.
Ali oni, izišavši, razniješe glas o njemu po svem onom kraju.
32 Yayinda suke fitowa, sai aka kawo wa Yesu wani mutum mai aljani, da ba ya iya magana.
Tek što oni iziđoše, gle, doniješe mu njemaka opsjednuta.
33 Sa’ad da aka fitar da aljanin kuwa, sai beben ya yi magana. Taron suka yi mamaki suka ce, “Ba a taɓa ganin irin wannan abu a Isra’ila ba.”
Pošto izagna đavla, progovori njemak. Mnoštvo se čudom čudilo i govorilo: “Nikada se takvo što ne vidje u Izraelu!”
34 Amma Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”
A farizeji govorahu: “Po poglavici đavolskome izgoni đavle.”
35 Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
I obilazio je Isus sve gradove i sela učeći po njihovim sinagogama, propovijedajući Evanđelje o Kraljevstvu i liječeći svaku bolest i svaku nemoć.
36 Da ya ga taron mutane, sai ya ji tausayinsu, domin an wulaƙanta su ba su kuma da mai taimako, kamar tumaki marasa makiyayi.
Vidjevši mnoštvo, sažali mu se nad njim jer bijahu izmučeni i ophrvani kao ovce bez pastira.
37 Sai ya ce wa almajiransa, “Girbi yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne.
Tada reče svojim učenicima: “Žetve je mnogo, a radnika malo.
38 Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi, yă aiko da ma’aikata cikin gonarsa na girbi.”
Molite dakle gospodara žetve da pošalje radnike u žetvu svoju.”

< Mattiyu 9 >