< Mattiyu 8 >

1 Da ya sauko daga dutsen, sai taron mutane mai yawan gaske suka bi shi.
Сшедшу же Ему с горы, вслед Его идяху народи мнози.
2 Wani mutum mai kuturta ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Ubangiji, in kana so, kana iya tsabtacce ni.”
И се, прокажен пришед кланяшеся Ему, глаголя: Господи, аще хощеши, можеши мя очистити.
3 Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtacce!” Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa.
И простер руку Иисус, коснуся ему, глаголя: хощу, очистися. И абие очистися ему проказа.
4 Sai Yesu ya ce masa, “Ka lura kada ka gaya wa kowa. Sai dai ka tafi, ka nuna kanka ga firist ka kuma yi bayarwar da Musa ya umarta, a matsayin shaida gare su.”
И глагола ему Иисус: виждь, ни комуже повеждь: но шед покажися иереови и принеси дар, егоже повеле (в законе) Моисей, во свидетелство им.
5 Da Yesu ya shiga Kafarnahum, sai wani jarumi ya zo wurinsa, yana neman taimako.
Вшедшу же Ему в Капернаум, приступи к Нему сотник, моля Его
6 Ya ce, “Ubangiji, bawana yana kwance a gida shanyayye, yana kuma shan azaba ƙwarai.”
и глаголя: Господи, отрок мой лежит в дому разслаблен, люте стражда.
7 Yesu ya ce masa, “Zan je in warkar da shi.”
И глагола ему Иисус: Аз пришед изцелю его.
8 Jarumin ya amsa, “Ubangiji, ban cancanci in sa ka zo gidana ba, ka dai yi magana kawai, bawana zai warke.
И отвещав сотник, рече (Ему): Господи, несмь достоин, да под кров мой внидеши: но токмо рцы слово, и изцелеет отрок мой:
9 Gama ni kaina mutum ne a ƙarƙashin iko, da kuma sojoji a ƙarƙashina. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi; wancan kuma, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan ce wa bawana, ‘Yi wannan,’ sai kuwa yă yi.”
ибо аз человек есмь под властию, имый под собою воины: и глаголю сему: иди, и идет: и другому: прииди, и приходит: и рабу моему: сотвори сие, и сотворит.
10 Da Yesu ya ji wannan, sai ya yi mamaki ya kuma ce wa waɗanda suke binsa, “Gaskiya nake gaya muku, ban taɓa samun wani a Isra’ila da bangaskiya mai girma haka ba.
Слышав же Иисус, удивися, и рече грядущым по Нем: аминь глаголю вам: ни во Израили толики веры обретох.
11 Ina kuma gaya muku da yawa za su zo daga gabas da kuma yamma, su ɗauki wuraren zamansu a biki tare da Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub a cikin mulkin sama.
Глаголю же вам, яко мнози от восток и запад приидут и возлягут со Авраамом и Исааком и Иаковом во Царствии Небеснем:
12 Amma za a jefar da’ya’yan mulki waje, zuwa cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”
сынове же царствия изгнани будут во тму кромешнюю: ту будет плачь и скрежет зубом.
13 Sa’an nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.
И рече Иисус сотнику: иди, и якоже веровал еси, буди тебе. И изцеле отрок его в той час.
14 Da Yesu ya zo cikin gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance a gado tana da zazzaɓi.
И пришед Иисус в дом Петров, виде тещу его лежащу и огнем жегому,
15 Ya taɓa hannunta sai zazzaɓin ya sake ta, ta kuwa tashi ta fara yin masa hidima.
и прикоснуся руце ея, и остави ю огнь: и воста и служаше ему.
16 Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.
Позде же бывшу, приведоша к Нему бесны многи: и изгна духи словом и вся болящыя изцели:
17 Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa, “Ya ɗebi rashin lafiyarmu, ya kuma ɗauki cututtukanmu.”
да сбудется реченное Исаием пророком, глаголющим: Той недуги нашя прият и болезни понесе.
18 Da Yesu ya ga taron mutane kewaye da shi, sai ya ba da umarni a ƙetare zuwa ɗayan hayin tafkin.
Видев же Иисус многи народы окрест Себе, повеле (учеником) ити на он пол.
19 Sai wani malamin dokoki ya zo wurinsa ya ce, “Malam, zan bi ka duk inda za ka.”
И приступль един книжник, рече Ему: Учителю, иду по Тебе, аможе аще идеши.
20 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”
Глагола ему Иисус: лиси язвины имут, и птицы небесныя гнезда: Сын же Человеческий не имать где главы подклонити.
21 Sai wani almajiri ya ce masa, “Ubangiji, da farko bari in je in binne mahaifina.”
Другий же от ученик Его рече Ему: Господи, повели ми прежде ити и погребсти отца моего.
22 Amma Yesu ya ce masa, “Ka bi ni, ka bar matattu su binne matattunsu.”
Иисус же рече ему: гряди по Мне и остави мертвых погребсти своя мертвецы.
23 Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi.
И влезшу Ему в корабль, по Нем идоша ученицы Его.
24 Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci.
И се, трус велик бысть в мори, якоже кораблю покрыватися волнами: Той же спаше.
25 Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”
И пришедше ученицы Его возбудиша Его, глаголюще: Господи, спаси ны, погибаем.
26 Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.
И глагола им: что страшливи есте, маловери? Тогда востав запрети ветром и морю, и бысть тишина велия.
27 Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”
Человецы же чудишася, глаголюще: кто есть Сей, яко и ветри и море послушают Его?
28 Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa (ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya.
И пришедшу Ему на он пол, в страну Гергесинскую, сретоста Его два бесна от гроб исходяща, люта зело, яко не мощи ни кому минути путем тем.
29 Suka yi ihu suka ce, “Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?” Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yă yi?
И се, возописта глаголюща: что нама и Тебе, Иисусе Сыне Божий? Пришел еси семо прежде времене мучити нас.
30 Nesa kaɗan da su kuwa akwai babban garken aladu da yake kiwo.
Бяше же далече от нею стадо свиний много пасомо.
31 Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.”
Беси же моляху Его, глаголюще: аще изгониши ны, повели нам ити в стадо свиное.
32 Ya ce musu, “Ku tafi!” Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa.
И рече им: идите. Они же изшедше идоша в стадо свиное: и се, (абие) устремися стадо все по брегу в море, и утопоша в водах.
33 Masu kiwon aladun suka ruga, suka je cikin gari suka ba da labarin dukan wannan, haɗe da abin da ya faru da mutanen nan masu aljanu.
Пасущии же бежаша, и шедше во град, возвестиша вся, и о бесною.
34 Sai dukan garin suka fito don su taryi Yesu. Da suka kuwa gan shi, sai suka roƙe shi yă bar musu yanki.
И се, весь град изыде в сретение Иисусови: и видевше Его, молиша, яко дабы прешел от предел их.

< Mattiyu 8 >