< Mattiyu 4 >

1 Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi.
Then Jesus was led up into the wilderness by the Spirit to be tempted by the devil.
2 Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa.
And, after he had fasted for forty days and forty nights, he became hungry.
3 Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi.”
The Tempter came to him, and said: ‘If you are God’s Son, tell these stones to become loaves of bread.’
4 Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’”
But Jesus answered, ‘Scripture says – “It is not on bread alone that a person is to live, but on every word that comes from the mouth of God.”’
5 Sai Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya kai shi can wuri mafi tsayi duka na haikali.
Then the devil took him to the Holy City, and, placing him on the parapet of the temple, said to him,
6 Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake, “‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’”
‘If you are God’s Son, throw yourself down, for scripture says – “He will give his angels commands about you, and on their hands they will lift you up, so you do not even strike your foot against a stone.”’
7 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’”
‘Scripture also says,’ answered Jesus, ‘“You must not tempt the Lord your God.”’
8 Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo sosai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu.
The third time, the devil took Jesus to a very high mountain, and, showing him all the kingdoms of the world and their splendour, said to him:
9 Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in za ka durƙusa ka yi mini sujada.”
‘All these I will give you, if you will fall at my feet and worship me.’
10 Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’”
Then Jesus said to him, ‘Go away, Satan! For scripture says – “You must worship the Lord your God, and worship him only.”’
11 Sa’an nan Iblis ya bar shi, mala’iku kuwa suka zo suka yi masa hidima.
Then the devil left him alone, and angels came and helped him.
12 Da Yesu ya ji labari cewa an kulle Yohanna a kurkuku, sai ya koma zuwa Galili.
When Jesus heard that John had been arrested, he returned to Galilee.
13 Ya bar Nazaret, ya je ya zauna a Kafarnahum, wadda take a bakin tafki wajen Zebulun da Naftali
Afterwards, leaving Nazareth, he went and settled at Capernaum, which is by the side of the sea, within the borders of Zebulun and Naphtali;
14 don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa,
in fulfilment of these words in the prophet Isaiah –
15 “Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali, da kuke a hanyar zuwa tekun Galili, a ƙetaren Urdun, wannan yankin Galili ta Al’ummai,
“The land of Zebulun and the land of Naphtali, the land of the Road by the sea, and beyond the Jordan, with Galilee of the Gentiles –
16 mutanen da suke zama cikin duhu sun ga babban haske; haske kuma ya haskaka a kan waɗanda suke zama a inuwar mutuwa.”
The people who were living in darkness have seen a great light, and, for those who were living in the shadow-land of death, a light has dawned!”
17 Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”
At that time Jesus began to proclaim – ‘Repent, for the kingdom of heaven is at hand.’
18 Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne.
As Jesus was walking along the shore of the Sea of Galilee, he saw two brothers – Simon, also known as Peter, and his brother Andrew – casting a net into the sea; for they were fishermen.
19 Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masu jan mutane zuwa wurina.”
‘Come and follow me,’ Jesus said, ‘and I will teach you to fish for people.’
20 Nan da nan suka bar abin kamun kifinsu suka bi shi.
The two men left their nets at once and followed him.
21 Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu’yan’uwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya abin kamun kifinsu. Yesu ya kira su,
Going further on, he saw two other men who were also brothers, James, Zebedee’s son, and his brother John, in their boat with their father, mending their nets. Jesus called them,
22 nan take suka bar jirgin ruwan da mahaifinsu suka kuwa bi Yesu.
and they at once left their boat and their father, and followed him.
23 Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane.
Jesus went all through Galilee, teaching in their synagogues, proclaiming the good news of the kingdom, and curing every kind of disease and every kind of sickness among the people;
24 Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.
and his fame spread all through Syria. They brought to him all who were ill with any form of disease, or who were suffering pain – any who were either possessed by demons, or were lunatic, or paralysed; and he cured them.
25 Taron mutane mai yawa daga Galili, Dekafolis, Urushalima, Yahudiya da kuma yankin hayin Urdun suka bi shi.
He was followed by large crowds from Galilee, the district of the Ten Towns, Jerusalem, Judea, and from beyond the Jordan.

< Mattiyu 4 >