< Mattiyu 3 >

1 A waɗancan kwanaki, Yohanna Mai Baftisma ya zo, yana wa’azi a Hamadan Yahudiya
In those days John the Baptist came, preaching in the wilderness of Judea
2 yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”
and saying, “Repent, for the kingdom of heaven is near.”
3 Wannan shi ne wanda aka yi maganarsa ta wurin annabi Ishaya cewa, “Ga murya mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’”
This is he who was spoken of through the prophet Isaiah: “A voice of one calling in the wilderness, ‘Prepare the way for the Lord, make straight paths for Him.’”
4 Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma daure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da zumar jeji.
John wore a garment of camel’s hair, with a leather belt around his waist. His food was locusts and wild honey.
5 Mutane suka zo wurinsa daga Urushalima da dukan Yahudiya da kuma dukan yankin Urdun.
People went out to him from Jerusalem and all Judea and the whole region around the Jordan.
6 Suna furta zunubansu, ya kuma yi musu baftisma a Kogin Urdun.
Confessing their sins, they were baptized by him in the Jordan River.
7 Amma da Yohanna ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa inda yake yin baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?
But when John saw many of the Pharisees and Sadducees coming to his place of baptism, he said to them, “You brood of vipers, who warned you to flee from the coming wrath?
8 Ku yi ayyukan da suka dace da tuba.
Produce fruit, then, in keeping with repentance.
9 Kada ma ku yi tunani a ranku cewa, ‘Ai, Ibrahim ne mahaifinmu.’ Ina gaya muku cewa Allah zai iya tā da’ya’ya wa Ibrahim daga cikin duwatsun nan.
And do not presume to say to yourselves, ‘We have Abraham as our father.’ For I tell you that out of these stones God can raise up children for Abraham.
10 An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.
The axe lies ready at the root of the trees, and every tree that does not produce good fruit will be cut down and thrown into the fire.
11 “Ina muku baftisma da ruwa domin tuba. Amma wani yana zuwa a bayana wanda ya fi ni iko, wanda ko takalmansa ma ban isa in ɗauka ba. Zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta.
I baptize you with water for repentance, but after me will come One more powerful than I, whose sandals I am not worthy to carry. He will baptize you with the Holy Spirit and with fire.
12 Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, yă kuma tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”
His winnowing fork is in His hand to clear His threshing floor and to gather His wheat into the barn; but He will burn up the chaff with unquenchable fire.”
13 Sai Yesu ya zo daga Galili, ya je Urdun don Yohanna yă yi masa baftisma.
At that time Jesus came from Galilee to the Jordan to be baptized by John.
14 Amma Yohanna ya so yă hana shi, yana cewa, “Ina bukata ka yi mini baftisma, yaya kake zuwa wurina?”
But John tried to prevent Him, saying, “I need to be baptized by You, and do You come to me?”
15 Yesu ya amsa ya ce, “Bari yă zama haka yanzu; ya dace mu yi haka don mu cika dukan adalci.” Sa’an nan Yohanna ya yarda.
“Let it be so now,” Jesus replied. “It is fitting for us to fulfill all righteousness in this way.” Then John permitted Him.
16 Nan da nan da aka yi wa Yesu baftisma, sai ya fito daga ruwa. A wannan lokaci sama ya buɗe, sai ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya ya kuwa sauka a kansa.
As soon as Jesus was baptized, He went up out of the water. Suddenly the heavens were opened, and He saw the Spirit of God descending like a dove and resting on Him.
17 Sai murya daga sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai.”
And a voice from heaven said, “This is My beloved Son, in whom I am well pleased!”

< Mattiyu 3 >