< Mattiyu 28 >

1 Bayan ranar Asabbaci, da sassafe, a ranar farko ta mako, Maryamu Magdalin tare da ɗaya Maryamun, suka je don su ga kabarin.
Now after the sabbath, in the dawning towards the first day of the week, came Mary Magdalene, and the other Mary, to look at the sepulchre:
2 Sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa. Don wani mala’ikan Ubangiji ya sauka daga sama, ya je kabarin, ya gungurar da dutsen, ya kuma zauna a kai.
and behold, there had been a great earthquake; for an angel of the Lord descending from heaven, had come and rolled away the stone from the door, and was sitting upon it:
3 Kamanninsa yana kama da walƙiya, tufafinsa kuma fari fat kamar dusan ƙanƙara.
(and his countenance was like lightning, and his raiment white as snow:
4 Masu gadin kabarin kuma suka ji tsoro ƙwarai, suka yi rawan jiki, suka zama kamar matattu.
and the guards shook for fear of him, and became like dead men: )
5 Mala’ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na san cewa kuna neman Yesu wanda aka gicciye ne.
and the angel said to the women, Be not ye afraid: for I know that ye seek Jesus who was crucified.
6 Ai, ba ya nan, ya tashi kamar yadda ya faɗa. Ku zo ku ga inda ya kwanta.
He is not here, for He is risen, as He said. Come, see the place where the Lord lay:
7 Sai ku tafi da sauri ku gaya wa almajiransa cewa, ‘Ya tashi daga matattu, ya kuma ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi.’ Ga shi na faɗa muku.”
and go quickly, and tell his disciples that He is risen from the dead; and behold, He is going before you into Galilee; there ye shall see Him; lo, I have told you.
8 Sai matan suka bar kabarin da hanzari, da tsoro, sai dai cike da farin ciki, suka tafi a guje don su gaya wa almajiransa.
And they went immediately from the sepulchre, with fear, and great joy, and ran to tell his disciples.
9 Kwaram, sai ga Yesu ya gamu da su ya ce, “Gaisuwa.” Sai suka zo kusa da shi, suka rungumi ƙafafunsa, suka yi masa sujada.
And as they were going to tell his disciples, behold, Jesus met them and said, God save you. And they drew near and embraced his feet, and worshipped Him.
10 Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku tafi ku gaya wa’yan’uwana, su tafi Galili. A can za su gan ni.”
Then saith Jesus unto them, Be not afraid, go tell my brethren to repair into Galilee, and there they shall see me.
11 Yayinda matan nan suna cikin tafiya, sai waɗansu daga cikin masu gadin suka shiga gari, suka ba wa manyan firistoci labarin duk abin da ya faru.
Now while they were going, behold some of the guard came into the city, and told the chief priests all that had happened:
12 Da manyan firistoci da dattawa suka taru, sai suka ƙulla wata dabara, suka ba wa sojojin kuɗi mai yawa.
and they assembled with the elders, and taking counsel together gave the soldiers a large sum of money,
13 Suka ce musu, “Ku, za ku ce, ‘Almajiransa ne sun zo da dare suka sace shi, lokacin da muke barci.’
saying, Do you say, that his disciples came by night, and stole Him away, while we were asleep.
14 In wannan labari ya kai kunnen gwamna, za mu lallashe shi, mu kuma kāre ku daga duk wata wahala.”
And if this should come to a hearing before the governor, we will satisfy him, and indemnify you.
15 Sai sojojin suka karɓi kuɗin, suka kuma yi kamar yadda aka umarce su. Wannan labarin kuwa shi ne ake bazawa ko’ina a cikin Yahudawa, har yă zuwa yau.
So they took the money, and did as they were instructed: and this is commonly reported among the Jews to this day.
16 Sa’an nan almajiransa goma sha ɗaya, suka tafi Galili, suka je dutsen da Yesu ya gaya musu.
And the eleven disciples went into Galilee, to the mountain where Jesus had appointed them.
17 Da suka gan shi, sai suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka.
And when they saw Him, they worshipped Him: but some doubted.
18 Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa.
And Jesus came and spake unto them, saying, All power is given unto me both in heaven and on earth.
19 Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikinsunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki,
Go ye therefore and instruct all nations, baptizing them in the name of the Father, and of the Son,
20 kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.” (aiōn g165)
and of the holy Ghost, and teaching them to observe all things whatsoever I have commanded you: and lo, I am with you always, even to the end of the world. Amen. (aiōn g165)

< Mattiyu 28 >