< Mattiyu 22 >
1 Yesu ya sāke yin musu magana da misalai, yana cewa,
And Jesus answered and spoke to them again by parables, and said,
2 “Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya bikin auren ɗansa.
The kingdom of heaven is like a certain king, who made a marriage for his son,
3 Sai ya aiki bayinsa su kira waɗanda aka gayyata zuwa bikin, amma waɗanda aka ce su zo bikin, suka ƙi zuwa.
And sent his servants to call them that were invited to the wedding: and they would not come.
4 “Sai ya sāke aiken waɗansu bayi ya ce, ‘Ku ce wa waɗanda aka gayyata cewa na shirya abinci. An yanka bijimai da shanun da aka yi kiwo, kome a shirye yake. Ku zo bikin auren mana.’
Again, he sent other servants, saying, Tell them who are invited, Behold, I have prepared my dinner: my oxen and my fatlings are killed, and all things are ready: come to the marriage.
5 “Amma ba su kula ba, suka kama gabansu, ɗaya ya tafi gonarsa, ɗaya kuma ya tafi kasuwancinsa.
But they made light of it, and went their ways, one to his farm, another to his merchandise:
6 Sauran suka kama bayinsa suka wulaƙanta su, suka kuma kashe su.
And the remnant took his servants, and treated them spitefully, and slew them.
7 Sai sarkin ya yi fushi. Ya aiki mayaƙansa suka karkashe masu kisankan nan, aka kuma ƙone birninsu.
But when the king heard of it, he was angry: and he sent his armies, and destroyed those murderers, and burned up their city.
8 “Sa’an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin aure fa ya shiryu, sai dai mutanen da na gayyata ba su dace ba.
Then he saith to his servants, The wedding is ready, but they who were invited were not worthy.
9 Ku bi titi-titi ku gayyato duk waɗanda kuka gani, su zo bikin.’
Go ye therefore into the highways, and as many as ye shall find, invite to the marriage.
10 Saboda haka bayin suka bi titi-titi, suka tattaro duk mutanen da suka samu, masu kirki da marasa kirki, zauren bikin ya cika makil da baƙi.
So those servants went out into the highways, and gathered together all as many as they found, both bad and good: and the wedding was furnished with guests.
11 “Amma da sarkin ya shigo don yă ga baƙin, sai ya ga wani can da ba ya sanye da kayan auren.
And when the king came in to see the guests, he saw there a man who had not a wedding garment:
12 Ya yi tambaya ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa.
And he saith to him, Friend, how camest thou in here not having a wedding garment? And he was speechless.
13 “Sai sarkin ya ce wa fadawa, ‘Ku daure shi hannu da ƙafa, ku jefar da shi waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’
Then said the king to the servants, Bind him hand and foot, and take him away, and cast him into outer darkness; there shall be weeping and gnashing of teeth.
14 “Gama kirayayu da yawa, amma zaɓaɓɓu kaɗan ne zaɓaɓɓu.”
For many are called, but few are chosen.
15 Sai Farisiyawa suka yi waje, suka ƙulla yadda za su yi masa tarko cikin maganarsa.
Then went the Pharisees, and took counsel how they might entangle him in his talk.
16 Suka aiki almajiransu tare da mutanen Hiridus wurinsa. Suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci, kuma kana koyar da maganar Allah bisa gaskiya. Mutane ba sa ɗaukan hankalinka, domin ba ka kula ko su wane ne ba.
And they sent out to him their disciples with the Herodians, saying, Master, we know that thou art true, and teachest the way of God in truth, neither carest thou for any man: for thou regardest not the person of men.
17 To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?”
Tell us therefore, What thinkest thou? Is it lawful to give tribute to Caesar, or not?
18 Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, “Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko?
But Jesus perceived their wickedness, and said, Why tempt ye me, ye hypocrites?
19 Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.” Sai suka kawo masa dinari,
Show me the tribute money. And they brought to him a penny.
20 sai ya tambaye su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?”
And he saith to them, Whose is this image and superscription?
21 Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”
They say to him, Caesar’s. Then saith he to them, Render therefore to Caesar the things which are Caesar’s; and to God the things that are God’s.
22 Da suka ji haka, sai suka yi mamaki. Saboda haka suka ƙyale shi, suka yi tafiyarsu.
When they had heard these words, they marvelled, and left him, and departed.
23 A ranan nan Sadukiyawa, waɗanda suke cewa babu tashin matattu, suka zo wurinsa da tambaya.
The same day came to him the Sadducees, who say that there is no resurrection, and asked him,
24 Suka ce “Malam, Musa ya faɗa mana cewa in mutum ya mutu ba shi da’ya’ya, dole ɗan’uwansa yă auri gwauruwar yă kuma haifar wa ɗan’uwan’ya’ya.
Saying, Master, Moses said, If a man dies, having no children, his brother shall marry his wife, and raise up seed to his brother.
25 A cikinmu an yi’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu, da yake bai sami’ya’ya ba, sai ya bar matarsa wa ɗan’uwansa.
Now there were with us seven brothers: and the first, when he had married a wife, died, and, having no issue, left his wife to his brother:
26 Haka ya faru da ɗan’uwa na biyu da na uku, har zuwa na bakwai.
Likewise the second also, and the third, to the seventh.
27 A ƙarshe, macen ta mutu.
And last of all the woman died also.
28 To, a tashin matattu, matar wa a cikinsu bakwai ɗin nan za tă zama, da yake dukansu sun aure ta?”
Therefore in the resurrection whose wife shall she be of the seven? for they all had her.
29 Yesu ya amsa ya ce, “Kun ɓata, domin ba ku san Nassi ko ikon Allah ba.
Jesus answered and said to them, Ye do err, not knowing the scriptures, nor the power of God.
30 Ai, a tashin matattu, mutane ba za su yi aure ko su ba da aure ba; za su zama kamar mala’iku a sama.
For in the resurrection they neither marry, nor are given in marriage, but are as the angels of God in heaven.
31 Amma game da tashi daga matattu na waɗanda suka mutu ba ku karanta abin da Allah ya ce muku ba ne,
But as concerning the resurrection of the dead, have ye not read that which was spoken to you by God, saying,
32 ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’? Ai, shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne.”
I am the God of Abraham, and the God of Isaac, and the God of Jacob? God is not the God of the dead, but of the living.
33 Da taro suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.
And when the multitude heard this, they were astonished at his doctrine.
34 Da jin Yesu ya ƙure Sadukiyawa, sai Farisiyawa suka tattaru.
But when the Pharisees had heard that he had put the Sadducees to silence, they were gathered together about him.
35 Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Doka, ya gwada shi da wannan tambaya.
Then one of them, who was a lawyer, asked him a question, tempting him, and saying,
36 “Malam, wace doka ce mafi girma a cikin dokoki?”
Master, which is the great commandment in the law?
37 Yesu ya amsa ya ce, “‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’
Jesus said to him, Thou shalt love the Lord thy God with all thy heart, and with all thy soul, and with all thy mind.
38 Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma.
This is the first and great commandment.
39 Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’
And the second is like it, Thou shalt love thy neighbour as thyself.
40 Dukan Doka da Annabawa suna rataya ne a kan waɗannan dokoki biyu.”
On these two commandments hang all the law and the prophets.
41 Yayinda Farisiyawa suke a tattare wuri ɗaya, sai Yesu ya tambaye su,
While the Pharisees were gathered together, Jesus asked them,
42 “Me kuke tsammani game da Kiristi? Ɗan wane ne shi?” Suka amsa suka ce, “Ɗan Dawuda.”
Saying, What think ye of Christ? whose son is he? They say to him, The Son of David.
43 Ya ce musu, “To, ta yaya Dawuda ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya kira shi ‘Ubangiji’? Gama ya ce,
He saith to them, How then doth David in spirit call him Lord, saying,
44 “‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.”’
The LORD said to my Lord, Sit thou on my right hand, till I make thy enemies thy footstool?
45 To, in Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji,’ yaya zai zama ɗansa?”
If David then calleth him Lord, how is he his son?
46 Ba wanda ya iya tanka masa, daga wannan rana kuwa ba wanda ya sāke yin karambanin yin masa wata tambaya.
And no man was able to answer him a word, neither dared any man from that day forth ask him any more questions.