< Mattiyu 2 >
1 Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima
Τοῦ δὲ Ἰησοῦ γεννηθέντος ἐν Βηθλεὲμ τῆς Ἰουδαίας ἐν ἡμέραις Ἡρώδου τοῦ βασιλέως, ἰδοὺ μάγοι ἀπὸ ἀνατολῶν παρεγένοντο εἰς Ἱεροσόλυμα
2 suka yi tambaya suka ce, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.”
λέγον τες, Ποῦ ἐστιν ὁ τεχθεὶς βασιλεὺς τῶν Ἰουδαίων; εἴδομεν γὰρ αὐτοῦ τὸν ἀστέρα ἐν τῇ ἀνατολῇ, καὶ ἤλθομεν προσκυνῆσαι αὐτῷ.
3 Da Sarki Hiridus ya ji wannan, sai hankalinsa ya tashi haka ma na dukan Urushalima.
ἀκούσας δὲ ὁ βασιλεὺς Ἡρώδης ἐταράχθη, καὶ πᾶσα Ἱεροσόλυμα μετ᾽ αὐτοῦ·
4 Bayan ya kira dukan manyan firistoci da malaman dokoki na mutane wuri ɗaya, sai ya tambaye su inda za a haifi Kiristi.
καὶ συναγαγὼν πάντας τοὺς ἀρχιερεῖς καὶ γραμματεῖς τοῦ λαοῦ, ἐπυνθάνετο παρ᾽ αὐτῶν, ποῦ ὁ χριστὸς γεννᾶται.
5 Suka amsa suka ce, “A Betlehem ne, cikin Yahudiya, gama haka annabin ya rubuta.
οἱ δὲ εἶπoν αὐτῷ, Ἐν Βηθλεὲμ τῆς Ἰουδαίας. οὕτως γὰρ γέγραπται διὰ τοῦ προφήτου,
6 “‘Amma ke Betlehem, a cikin ƙasar Yahuda, ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin masu mulki a Yahuda ba, gama daga cikinki mai mulki zai zo, wanda zai zama makiyayin mutanena Isra’ila.’”
Καὶ σύ, Βηθλεὲμ γῆ Ἰούδα, οὐδαμῶς ἐλαχίστη εἶ ἐν τοῖς ἡγεμόσιν Ἰούδα· ἐκ σοῦ γὰρ ἐξελεύσεται ἡγούμενος, ὅστις ποιμανεῖ τὸν λαόν μου τὸν Ἰσραήλ.
7 Sai Hiridus ya kira Masanan nan a ɓoye, yă gano daga wurinsu daidai lokacin da tauraron ya bayyana.
Τότε Ἡρώδης λάθρα καλέσας τοὺς μάγους ἠκρίβωσεν παρ᾽ αὐτῶν τὸν χρόνον τοῦ φαινομένου ἀστέρος,
8 Sai ya aike su Betlehem ya ce, “Ku je ku binciko a hankali game da yaron nan. Da kun same shi, sai ku kawo mini labari nan da nan, domin ni ma in je in yi masa sujada.”
καὶ πέμψας αὐτοὺς εἰς Βηθλεὲμ εἶπεν, Πορευθέντες ἐξετάσατε ἀκριβῶς περὶ τοῦ παιδίου· ἐπὰν δὲ εὕρητε, ἀπαγγείλατέ μοι, ὅπως κἀγὼ ἐλθὼν προσκυνήσω αὐτῷ.
9 Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake.
οἱ δὲ ἀκούσαντες τοῦ βασιλέως ἐπορεύθησαν· καὶ ἰδοὺ ὁ ἀστήρ, ὃν εἶδον ἐν τῇ ἀνατολῇ, προῆγεν αὐτοὺς ἕως ἐλθὼν ἐστάθη ἐπάνω οὗ ἦν τὸ παιδίον.
10 Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai.
ἰδόντες δὲ τὸν ἀστέρα ἐχάρησαν χαρὰν μεγάλην σφόδρα·
11 Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur.
καὶ ἐλθόντες εἰς τὴν οἰκίαν εἶδον τὸ παιδίον μετὰ Μαρίας τῆς μητρὸς αὐτοῦ, καὶ πεσόντες προσεκύνησαν αὐτῷ, καὶ ἀνοίξαντες τοὺς θησαυροὺς αὐτῶν προσήνεγκαν αὐτῷ δῶρα, χρυσὸν καὶ λίβανον καὶ σμύρναν.
12 Bayan an gargaɗe su cikin mafarki kada su koma wurin Hiridus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.
καὶ χρηματισθέντες κατ᾽ ὄναρ μὴ ἀνακάμψαι πρὸς Ἡρώδην, δι᾽ ἄλλης ὁδοῦ ἀνεχώρησαν εἰς τὴν χώραν αὐτῶν.
13 Bayan sun tafi, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku gudu zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yă kashe.”
Ἀναχωρησάντων δὲ αὐτῶν, ἰδοὺ ἄγγελος κυρίου κατ᾽ ὄναρ φαίνεται τῷ Ἰωσὴφ λέγων, Ἐγερθεὶς παράλαβε τὸ παιδίον καὶ τὴν μητέρα αὐτοῦ, καὶ φεῦγε εἰς Αἴγυπτον, καὶ ἴσθι ἐκεῖ ἕως ἂν εἴπω σοί· μέλλει γὰρ Ἡρώδης ζητεῖν τὸ παιδίον, τοῦ ἀπολέσαι αὐτό.
14 Sai Yusuf ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa da dad dare suka tafi Masar,
ὁ δὲ ἐγερθεὶς παρέλαβεν τὸ παιδίον καὶ τὴν μητέρα αὐτοῦ νυκτὸς καὶ ἀνεχώρησεν εἰς Αἴγυπτον,
15 inda ya zauna har sai da Hiridus ya mutu. Ta haka kuwa aka cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kira ɗana.”
καὶ ἦν ἐκεῖ ἕως τῆς τελευτῆς Ἡρώδου· ἵνα πληρωθῇ τὸ ῥηθὲν ὑπὸ κυρίου διὰ τοῦ προφήτου λέγοντος, Ἐξ Αἰγύπτου ἐκάλεσα τὸν υἱόν μου.
16 Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan’yan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan.
Τότε Ἡρώδης ἰδὼν ὅτι ἐνεπαίχθη ὑπὸ τῶν μάγων, ἐθυμώθη λίαν, καὶ ἀποστείλας ἀνεῖλεν πάντας τοὺς παῖδας τοὺς ἐν Βηθλεὲμ καὶ ἐν πᾶσιν τοῖς ὁρίοις αὐτῆς, ἀπὸ διετοῦς καὶ κατωτέρω, κατὰ τὸν χρόνον ὃν ἠκρίβωσεν παρὰ τῶν μάγων.
17 Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa,
τότε ἐπληρώθη τὸ ῥηθὲν διὰ Ἱερεμίου τοῦ προφήτου λέγοντος,
18 “An ji murya a Rama, tana kuka da makoki mai tsanani, Rahila ce take kuka domin’ya’yanta, an kāsa ta’azantar da ita, don ba su.”
Φωνὴ ἐν Ῥαμᾶ ἠκούσθη, κλαυθμὸς καὶ ὀδυρμὸς πολύς, Ῥαχὴλ κλαίουσα τὰ τέκνα αὐτῆς, καὶ οὐκ ἤθελεν παρακληθῆναι, ὅτι οὐκ εἰσίν.
19 Bayan Hiridus ya mutu, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki a Masar,
Τελευτήσαντος δὲ τοῦ Ἡρώδου, ἰδοὺ ἄγγελος κυρίου φαίνεται κατ᾽ ὄναρ τῷ Ἰωσὴφ ἐν Αἰγύπτῳ,
20 ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa ku tafi ƙasar Isra’ila, domin waɗanda suke neman ran yaron sun mutu.”
λέγων, Ἐγερθεὶς παράλαβε τὸ παιδίον καὶ τὴν μητέρα αὐτοῦ, καὶ πορεύου εἰς γῆν Ἰσραήλ· τεθνήκασιν γὰρ οἱ ζητοῦντες τὴν ψυχὴν τοῦ παιδίου.
21 Sai ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa suka tafi ƙasar Isra’ila.
ὁ δὲ ἐγερθεὶς παρέλαβεν τὸ παιδίον καὶ τὴν μητέρα αὐτοῦ καὶ εἰσῆλθεν εἰς γῆν Ἰσραήλ.
22 Amma da ya ji Arkelawus ne yake mulki a Yahudiya a matsayin wanda ya gāji mahaifinsa Hiridus, sai ya ji tsoron zuwa can. Bayan an gargaɗe shi a mafarki, sai ya ratse zuwa gundumar Galili,
ἀκούσας δὲ ὅτι Ἀρχέλαος βασιλεύει [ἐπὶ] τῆς Ἰουδαίας ἀντὶ τοῦ πατρὸς αὐτοῦ Ἡρώδου ἐφοβήθη ἐκεῖ ἀπελθεῖν· χρηματισθεὶς δὲ κατ᾽ ὄναρ ἀνεχώρησεν εἰς τὰ μέρη τῆς Γαλιλαίας,
23 ya je ya zauna a wani garin da ake kira Nazaret. Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta bakin annabawa cewa, “Za a ce da shi Banazare.”
καὶ ἐλθὼν κατῴκησεν εἰς πόλιν λεγομένην Ναζαρέθ, ὅπως πληρωθῇ τὸ ῥηθὲν διὰ τῶν προφητῶν ὅτι Ναζωραῖος κληθήσεται.