< Mattiyu 17 >

1 Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai.
Seis días después, Jesús tomó a Pedro, Jacobo y Juan, y los llevó aparte a una montaña alta.
2 A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, tufafinsa kuwa suka zama fari fat suna walƙiya.
Y se transfiguró delante de ellos. Su rostro resplandeció como el sol y sus vestiduras se transformaron como la luz.
3 Nan take sai ga Musa da Iliya suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.
Aparecieron Moisés y Elías quienes hablaban con Él.
4 Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. In kana so, sai in kafa bukkoki uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”
Entonces Pedro dijo a Jesús: ¡Señor, es bueno que nos quedemos aquí! Si quieres, haré tres enramadas: una para Ti, una para Moisés y una para Elías.
5 Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”
Mientras hablaba, una nube radiante los cubrió, y de la nube salió una voz que decía: Éste es mi Hijo amado, en Quien me complací. Escúchenlo a Él.
6 Sa’ad da almajiran suka ji haka, sai suka fāɗi ƙasa rubda ciki, a firgice.
Los discípulos, al oír [esto], cayeron sobre sus rostros y se atemorizaron muchísimo.
7 Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”
Pero Jesús se acercó, los tocó y dijo: Levántense. No teman.
8 Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai.
Al levantar sus ojos, solo vieron a Jesús.
9 Suna cikin gangarowa daga dutsen ke nan, sai Yesu ya umarce su cewa, “Kada ku faɗa wa kowa abin da kuka gani, sai bayan an tā da Ɗan Mutum daga matattu.”
Mientras ellos descendían de la montaña, Jesús les ordenó: A nadie digan la visión hasta que el Hijo del Hombre sea levantado de entre [los] muertos.
10 Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, me ya sa malaman dokoki suke cewa, dole sai Iliya ya fara zuwa?”
Los discípulos le preguntaron: ¿Por qué dicen los escribas que Elías debe venir primero?
11 Yesu ya amsa ya ce, “Tabbatacce, Iliya zai zo, zai kuma gyara dukan abubuwa.
Él respondió: En verdad Elías vendría y restauraría todas las cosas.
12 Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa gane shi ba, amma suka yi masa duk abin da suka ga dama. Haka ma Ɗan Mutum zai sha wahala a hannunsu.”
Pero les digo que Elías ya vino y no lo reconocieron, sino hicieron con él todo lo que quisieron. Así también el Hijo del Hombre padecerá pronto en manos de ellos.
13 Sa’an nan almajiran suka gane cewa yana musu zancen Yohanna Mai Baftisma ne.
Entonces los discípulos comprendieron que les hablaba de Juan el Bautista.
14 Da suka isa wajen taron, sai wani mutum ya zo ya durƙusa a gabansa.
Cuando llegó al gentío, un hombre se [le] acercó, se arrodilló ante Él
15 Ya ce, “Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa.
y le dijo: Señor, ten compasión de mi hijo, pues es lunático y padece severamente. Porque muchas veces cae en el fuego y en el agua.
16 Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.”
Lo traje a tus discípulos, pero no fueron capaces de sanarlo.
17 Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.”
Jesús respondió: ¡Oh generación incrédula y perversa! ¿Hasta cuándo estaré con ustedes? ¿Hasta cuándo los soportaré? ¡Tráiganlo acá!
18 Yesu ya tsawata wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.
Jesús lo reprendió y el demonio salió de él. El muchacho fue sanado desde aquel momento.
19 Sa’an nan almajiran suka zo wurin Yesu a ɓoye suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da aljanin ba?”
Entonces, los discípulos se acercaron a Jesús en privado y le preguntaron: ¿Por qué nosotros no pudimos echarlo?
20 Ya amsa ya ce, “Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.”
Les respondió: Por su poca fe, porque en verdad les digo que si tuvieran fe como un grano de mostaza, dirían a esta montaña: ¡Pásate de aquí allá! Y se pasaría, y nada les sería imposible.
22 Da suka taru a Galili, sai ya ce musu, “Za a bashe Ɗan Mutum, a hannun mutane.
Cuando estaban en Galilea Jesús les dijo: El Hijo del Hombre va a ser entregado en manos de unos hombres
23 Za su kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Almajiran kuwa suka cika da baƙin ciki.
y lo matarán, pero al tercer día será resucitado. Y ellos se entristecieron muchísimo.
24 Bayan Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan harajin rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku ba ya biyan harajin haikali ne?”
Al llegar ellos a Cafarnaúm, los que cobraban las dos dracmas se acercaron a Pedro y dijeron: ¿Su Maestro no paga didracma?
25 Ya amsa ya ce “I, yana biya.” Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, “Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji, daga wurin’ya’yansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?”
Contestó: Sí. Y al llegar a la casa, Jesús se le adelantó y preguntó: ¿Qué opinas, Simón? ¿De quiénes cobran impuestos o tributo los reyes de la tierra? ¿De sus hijos o de los extraños?
26 Bitrus ya amsa ya ce, “Daga wurin waɗansu.” Yesu ya ce masa, “Wato, an ɗauke wa’ya’yan ke nan.
Y respondió: De los extraños. Jesús le dijo: Entonces los hijos están exentos.
27 Amma don kada mu ɓata musu rai, ka je tafki ka jefa ƙugiyarka. Ka ɗauki kifin da ka fara kama; ka buɗe bakinsa, za ka sami shekel guda. Ka kawo ka ba su, harajina da naka ke nan.”
Sin embargo, para que no los ofendamos, vé al mar, lanza un anzuelo y toma el primer pez que salga. Al abrir su boca, hallarás un didracma. Tómalo, vé, dáselo por Mí y por ti.

< Mattiyu 17 >