< Mattiyu 14 >
1 A lokacin nan sarki Hiridus ya ji labarin Yesu,
in illo tempore audiit Herodes tetrarcha famam Iesu
2 sai ya ce wa fadawansa, “Wannan Yohanna Mai Baftisma ne; ya tashi daga matattu! Shi ya sa abubuwan banmamakin nan suke faruwa ta wurinsa.”
et ait pueris suis hic est Iohannes Baptista ipse surrexit a mortuis et ideo virtutes inoperantur in eo
3 To, dā Hiridus ya kama Yohanna ya daure, ya kuma sa shi cikin kurkuku saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus,
Herodes enim tenuit Iohannem et alligavit eum et posuit in carcere propter Herodiadem uxorem fratris sui
4 gama Yohanna ya dinga ce masa, “Ba daidai ba ne ka aure ta.”
dicebat enim illi Iohannes non licet tibi habere eam
5 Hiridus ya so yă kashe Yohanna, amma yana jin tsoron mutane, don sun ɗauka shi annabi ne.
et volens illum occidere timuit populum quia sicut prophetam eum habebant
6 A bikin tuna da ranar haihuwar Hiridus, diyar Hiridiyas ta yi musu rawa ta kuma gamsar da Hiridus ƙwarai,
die autem natalis Herodis saltavit filia Herodiadis in medio et placuit Herodi
7 har ya yi alkawari da rantsuwa cewa zai ba ta duk abin da ta roƙa.
unde cum iuramento pollicitus est ei dare quodcumque postulasset ab eo
8 Da mahaifiyarta ta zuga ta, sai ta ce, “Ba ni a cikin kwanon nan, kan Yohanna Mai Baftisma.”
at illa praemonita a matre sua da mihi inquit hic in disco caput Iohannis Baptistae
9 Sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwarsa da kuma baƙinsa, sai ya ba da umarni a ba ta abin da ta roƙa
et contristatus est rex propter iuramentum autem et eos qui pariter recumbebant iussit dari
10 ya kuma sa aka yanke kan Yohanna a kurkuku.
misitque et decollavit Iohannem in carcere
11 Aka kawo kansa cikin kwano aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa mahaifiyarta.
et adlatum est caput eius in disco et datum est puellae et tulit matri suae
12 Almajiran Yohanna suka zo suka ɗauki gawarsa suka binne. Sa’an nan suka je suka gaya wa Yesu.
et accedentes discipuli eius tulerunt corpus et sepelierunt illud et venientes nuntiaverunt Iesu
13 Sa’ad da Yesu ya ji abin da ya faru, sai ya shiga jirgin ruwa ya janye shi kaɗai zuwa wani wuri inda ba kowa. Da jin haka, taron mutane suka bi shi da ƙafa daga garuruwa.
quod cum audisset Iesus secessit inde in navicula in locum desertum seorsum et cum audissent turbae secutae sunt eum pedestres de civitatibus
14 Da Yesu ya sauka ya kuma ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu ya kuma warkar da marasa lafiyarsu.
et exiens vidit turbam multam et misertus est eius et curavit languidos eorum
15 Da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuma rana ta kusa fāɗuwa. Ka sallami taron don su shiga ƙauyuka su nemi wa kansu abinci.”
vespere autem facto accesserunt ad eum discipuli eius dicentes desertus est locus et hora iam praeteriit dimitte turbas ut euntes in castella emant sibi escas
16 Yesu ya amsa, “Ba su bukata su tafi. Ku ku ba su wani abu su ci.”
Iesus autem dixit eis non habent necesse ire date illis vos manducare
17 Suka ce, “Burodi biyar da kifi biyu ne kawai muke da su a nan.”
responderunt ei non habemus hic nisi quinque panes et duos pisces
18 Ya ce, “Ku kawo mini su a nan.”
qui ait eis adferte illos mihi huc
19 Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane.
et cum iussisset turbam discumbere supra faenum acceptis quinque panibus et duobus piscibus aspiciens in caelum benedixit et fregit et dedit discipulis panes discipuli autem turbis
20 Duk suka ci suka ƙoshi, almajiran kuwa suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu.
et manducaverunt omnes et saturati sunt et tulerunt reliquias duodecim cofinos fragmentorum plenos
21 Yawan waɗanda suka ci, sun yi wajen maza dubu biyar, ban da mata da yara.
manducantium autem fuit numerus quinque milia virorum exceptis mulieribus et parvulis
22 Nan da nan Yesu ya sa almajiran su shiga jirgin ruwa su sha gabansa, su haye zuwa ɗayan hayin, yayinda shi kuma yă sallami taron.
et statim iussit discipulos ascendere in navicula et praecedere eum trans fretum donec dimitteret turbas
23 Bayan ya sallame su, sai ya haura bisan gefen dutse shi kaɗai don yă yi addu’a. Da yamma ta yi, yana can shi kaɗai,
et dimissa turba ascendit in montem solus orare vespere autem facto solus erat ibi
24 jirgin ruwan kuwa ya riga ya yi nesa da gaci, yana fama da raƙuman ruwa domin iska tana gāba da shi.
navicula autem in medio mari iactabatur fluctibus erat enim contrarius ventus
25 Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin.
quarta autem vigilia noctis venit ad eos ambulans supra mare
26 Sa’ad da almajiran suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai tsoro ya kama su. Suka yi ihu don tsoro suka ce, “Fatalwa ce.”
et videntes eum supra mare ambulantem turbati sunt dicentes quia fantasma est et prae timore clamaverunt
27 Amma nan da nan Yesu ya ce musu, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”
statimque Iesus locutus est eis dicens habete fiduciam ego sum nolite timere
28 Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji in kai ne ka ce mini in zo wurinka a kan ruwan.”
respondens autem Petrus dixit Domine si tu es iube me venire ad te super aquas
29 Ya ce, “Zo.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwan, ya taka a kan ruwan ya nufe wajen Yesu.
at ipse ait veni et descendens Petrus de navicula ambulabat super aquam ut veniret ad Iesum
30 Amma da ya ga haukar iskar, sai ya ji tsoro, ya kuma fara nutsewa, sai ya yi ihu ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”
videns vero ventum validum timuit et cum coepisset mergi clamavit dicens Domine salvum me fac
31 Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, “Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”
et continuo Iesus extendens manum adprehendit eum et ait illi modicae fidei quare dubitasti
32 Da suka hau jirgin ruwan, sai iskar ta kwanta.
et cum ascendissent in naviculam cessavit ventus
33 Waɗanda suke cikin jirgin ruwan kuwa suka yi masa sujada, suna cewa, “Gaskiya kai Ɗan Allah ne.”
qui autem in navicula erant venerunt et adoraverunt eum dicentes vere Filius Dei es
34 Sa’ad da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret.
et cum transfretassent venerunt in terram Gennesar
35 Da mutanen wurin suka gane da Yesu, sai suka kai labari a ko’ina a ƙauyukan da suke kewaye. Mutane suka kawo masa dukan marasa lafiyarsu
et cum cognovissent eum viri loci illius miserunt in universam regionem illam et obtulerunt ei omnes male habentes
36 suka kuwa roƙe shi yă bar marasa lafiya su taɓa ko da gefen rigarsa kawai, duk waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.
et rogabant eum ut vel fimbriam vestimenti eius tangerent et quicumque tetigerunt salvi facti sunt