< Mattiyu 12 >
1 A lokacin nan Yesu ya bi ta gonakin hatsi a ranar Asabbaci. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara kakkarya kan hatsi suna ci.
At that time Jesus went through the grainfields on the Sabbath. His disciples were hungry and began to pick the heads of grain and eat them.
2 Sa’ad da Farisiyawa suka ga wannan, sai suka ce masa, “Duba! Almajiranka suna yin abin da doka ta hana a yi a ranar Asabbaci.”
When the Pharisees saw this, they said to Him, “Look, Your disciples are doing what is unlawful on the Sabbath.”
3 Sai ya amsa ya ce, “Ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba ne sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa?
Jesus replied, “Have you not read what David did when he and his companions were hungry?
4 Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin, wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai.
He entered the house of God, and he and his companions ate the consecrated bread, which was not lawful for them to eat, but only for the priests.
5 Ko kuwa ba ku karanta a Doka cewa a ranar Asabbaci firistoci sukan karya dokar Asabbaci duk da haka ba da yin wani laifi ba?
Or haven’t you read in the Law that on the Sabbath the priests in the temple break the Sabbath and yet are innocent?
6 Ina faɗa muku cewa waniwanda ya fi haikali yana a nan.
But I tell you that something greater than the temple is here.
7 Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’da ba ku zargi marar laifi ba.
If only you had known the meaning of ‘I desire mercy, not sacrifice,’ you would not have condemned the innocent.
8 Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.”
For the Son of Man is Lord of the Sabbath.”
9 Da ya ci gaba daga wurin, sai ya shiga majami’arsu,
Moving on from there, Jesus entered their synagogue,
10 a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?”
and a man with a withered hand was there. In order to accuse Jesus, they asked Him, “Is it lawful to heal on the Sabbath?”
11 Ya ce musu, “In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba?
He replied, “If one of you has a sheep and it falls into a pit on the Sabbath, will he not take hold of it and lift it out?
12 Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja! Saboda haka ya dace a aikata alheri ran Asabbaci.”
How much more valuable is a man than a sheep! Therefore it is lawful to do good on the Sabbath.”
13 Sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙa hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye, kamar dai ɗayan.
Then Jesus said to the man, “Stretch out your hand.” So he stretched it out, and it was restored to full use, just like the other.
14 Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu.
But the Pharisees went out and plotted how they might kill Jesus.
15 Da ya gane wannan, sai Yesu ya janye daga wurin. Da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da dukan masu ciwonsu,
Aware of this, Jesus withdrew from that place. Large crowds followed Him, and He healed them all,
16 yana jan musu kunne kada su faɗa wa kowa akan ko shi wane ne.
warning them not to make Him known.
17 Wannan kuwa domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya ne cewa,
This was to fulfill what was spoken through the prophet Isaiah:
18 “Ga bawana da na zaɓa, ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi; zan sa Ruhuna a kansa, zai kuma yi shelar adalci ga al’ummai.
“Here is My Servant, whom I have chosen, My beloved, in whom My soul delights. I will put My Spirit on Him, and He will proclaim justice to the nations.
19 Ba zai yi faɗa ko yă ɗaga murya ba, ba kuwa wanda zai ji muryarsa a kan tituna.
He will not quarrel or cry out; no one will hear His voice in the streets.
20 Kyauron da ya tanƙwasa ba zai karye shi ba. Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba, sai ya jagoranci adalci zuwa ga nasara.
A bruised reed He will not break, and a smoldering wick He will not extinguish, till He leads justice to victory.
21 Cikin sunansa al’ummai za su dogara.”
In His name the nations will put their hope.”
22 Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari.
Then a demon-possessed man who was blind and mute was brought to Jesus, and He healed the man so that he could speak and see.
23 Dukan mutane suka yi mamaki, suka ce, “Wannan Ɗan Dawuda ne kuwa?”
The crowds were astounded and asked, “Could this be the Son of David?”
24 Amma da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce, “Ahab, da Be’elzebub sarkin aljanu ne kaɗai, wannan mutum yake fitar da aljanu.”
But when the Pharisees heard this, they said, “Only by Beelzebul, the prince of demons, does this man drive out demons.”
25 Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba.
Knowing their thoughts, Jesus said to them, “Every kingdom divided against itself will be laid waste, and every city or household divided against itself will not stand.
26 In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore?
If Satan drives out Satan, he is divided against himself. How then can his kingdom stand?
27 In kuwa ta wurin Be’elzebub nake fitar da aljanu, to, ta wa mutanenku suke fitar da su? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku.
And if I drive out demons by Beelzebul, by whom do your sons drive them out? So then, they will be your judges.
28 Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.
But if I drive out demons by the Spirit of God, then the kingdom of God has come upon you.
29 “Ko kuwa, yaya wani zai iya shiga gidan mai ƙarfi yă ƙwace masa kaya ba tare da ya fara daure mai ƙarfin nan tukuna ba? Sa’an nan zai iya washe gidansa.
Or again, how can anyone enter a strong man’s house and steal his possessions, unless he first ties up the strong man? Then he can plunder his house.
30 “Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ne, kuma wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.
He who is not with Me is against Me, and he who does not gather with Me scatters.
31 Saboda haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane zunubi da kuma saɓo, amma saɓo game da Ruhu, ba za a gafarta ba.
Therefore I tell you, every sin and blasphemy will be forgiven men, but the blasphemy against the Spirit will not be forgiven.
32 Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa. (aiōn )
Whoever speaks a word against the Son of Man will be forgiven, but whoever speaks against the Holy Spirit will not be forgiven, either in this age or in the one to come. (aiōn )
33 “Itace mai kyau, yakan ba da’ya’ya masu kyau. Itace marar kyau kuma, yakan ba da’ya’ya marasa kyau. Itace dai, da irin’ya’yansa ne ake gane shi.
Make a tree good and its fruit will be good, or make a tree bad and its fruit will be bad; for a tree is known by its fruit.
34 Ku macizai, ta yaya ku da kuke mugaye za ku iya magana kirki? Gama daga baki, mutum yakan faɗi abin da yake cikin zuciya.
You brood of vipers, how can you who are evil say anything good? For out of the overflow of the heart, the mouth speaks.
35 Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa.
The good man brings good things out of his good store of treasure, and the evil man brings evil things out of his evil store of treasure.
36 Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa.
But I tell you that men will give an account on the day of judgment for every careless word they have spoken.
37 Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.”
For by your words you will be acquitted, and by your words you will be condemned.”
38 Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka ce masa, “Malam, muna so mu ga wata alama mai banmamaki daga gare ka.”
Then some of the scribes and Pharisees said to Him, “Teacher, we want to see a sign from You.”
39 Sai ya amsa ya ce, “Mugaye da masu zinan zamanin nan suna neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana.
Jesus replied, “A wicked and adulterous generation demands a sign, but none will be given it except the sign of the prophet Jonah.
40 Gama kamar yadda Yunana ya yi yini uku da kuma dare uku a cikin wani babban kifi, haka Ɗan Mutum zai yi yini uku da kuma dare uku a cikin ƙasa.
For as Jonah was three days and three nights in the belly of the great fish, so the Son of Man will be three days and three nights in the heart of the earth.
41 Mutanen Ninebe za su tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, su kuwa hukunta shi; don sun tuba saboda wa’azin Yunana, yanzu kuwa ga wanda ya fi Yunana girma a nan.
The men of Nineveh will stand at the judgment with this generation and condemn it; for they repented at the preaching of Jonah, and now One greater than Jonah is here.
42 Sarauniyar Sheba za tă tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, tă kuwa hukunta shi; don ta zo daga ƙarshen duniya, ta saurari hikimar Solomon, yanzu kuwa ga wanda ya fi Solomon girma a nan.
The Queen of the South will rise at the judgment with this generation and condemn it; for she came from the ends of the earth to hear the wisdom of Solomon, and now One greater than Solomon is here.
43 “Sa’ad da mugun ruhu ya fita daga mutum, yakan bi wuraren da ba ruwa yana neman hutu, ba ya kuwa samu.
When an unclean spirit comes out of a man, it passes through arid places seeking rest and does not find it.
44 Sa’an nan yakan ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ Sa’ad da ya iso, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, kuma a kintse.
Then it says, ‘I will return to the house I left.’ On its return, it finds the house vacant, swept clean, and put in order.
45 Sai yă je yă ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, su kuwa zo su shiga su zauna a can. Ƙarshen mutumin nan fa zai fi farkonsa muni. Haka zai zama ga wannan mugun zamani.”
Then it goes and brings with it seven other spirits more wicked than itself, and they go in and dwell there; and the final plight of that man is worse than the first. So will it be with this wicked generation.”
46 Yayinda Yesu yake cikin magana da taron, sai ga mahaifiyarsa da’yan’uwansa tsaye a waje, suna so su yi magana da shi.
While Jesus was still speaking to the crowds, His mother and brothers stood outside, wanting to speak to Him.
47 Wani ya ce masa, “Mahaifiyarka da’yan’uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.”
Someone told Him, “Look, Your mother and brothers are standing outside, wanting to speak to You.”
48 Ya amsa masa ya ce, “Wace ce mahaifiyata, su wane ne kuma’yan’uwana?”
But Jesus replied, “Who is My mother, and who are My brothers?”
49 Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa ya ce, “Ga mahaifiyata da kuma’yan’uwana.
Pointing to His disciples, He said, “Here are My mother and My brothers.
50 Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗan’uwana da’yar’uwata da kuma mahaifiyata.”
For whoever does the will of My Father in heaven is My brother and sister and mother.”