< Mattiyu 10 >
1 Sai ya kira almajiransa goma sha biyu wurinsa ya kuma ba su iko su fitar aljanu, su kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
Llamó a sus 12 discípulos y les dio autoridad sobre los espíritus impuros para que los echaran fuera y sanaran toda enfermedad y toda dolencia.
2 Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu, da fari, Siman (wanda ake kira Bitrus) da ɗan’uwansa Andarawus; Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna;
Los nombres de los 12 apóstoles son: Primero, Simón Pedro, su hermano Andrés, Jacobo, hijo de Zebedeo, su hermano Juan,
3 Filibus da Bartolomeyu; Toma da Mattiyu mai karɓar haraji; Yaƙub ɗan Alfayus da Taddayus;
Felipe, Bartolomé, Tomás, Mateo el publicano, Jacobo, hijo de Alfeo, Tadeo,
4 Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu.
Simón el cananita, y Judas Iscariote, quien lo traicionó.
5 Waɗannan sha biyun ne Yesu ya aika da umarni cewa, “Kada ku je cikin Al’ummai, ko kuwa ku shiga wani garin Samariyawa.
Jesús envió a estos 12 y les ordenó: No vayan a los gentiles, ni entren en la región de Samaria,
6 A maimakon haka ku je wajen ɓatattun tumakin Isra’ila.
sino vayan antes a las ovejas perdidas de la casa de Israel.
7 Sa’ad da kuke tafiya, ku yi wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin sama ya kusato.’
Vayan y proclamen: El reino celestial se acercó.
8 Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.
Sanen enfermos, resuciten muertos, limpien leprosos y echen fuera demonios. Gratuitamente recibieron ustedes. Den del mismo modo.
9 “Kada ku riƙe wata zinariya ko azurfa ko jan ƙarfe a aljihunanku,
No se provean de oro, ni plata, ni cobre en sus cinturones,
10 kada ku ɗauki jaka don tafiya, ko ƙarin riga, ko takalma ko sanda; domin ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.
ni provisiones para el camino, ni dos túnicas, ni sandalias, ni bordón, porque el obrero es digno de su sustento.
11 Kowane gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a wurin, ku kuma zauna a gidansa har sai kun tashi.
En cualquier ciudad o aldea donde entren, infórmense quién es digno en ella, y posen allí hasta que salgan.
12 Da shigarku gidan, ku yi gaisuwa.
Al entrar en la casa, salúdenla.
13 In gidan na kirki ne, bari salamarku ta zauna a kansa; in kuwa ba mai kirki ba, salamarku ta komo muku.
Si en verdad la casa es digna, repose la paz de ustedes sobre ella, pero si no es digna, vuélvase su paz a ustedes.
14 Duk wanda ya ƙi marabtarku ko ya ƙi sauraron kalmominku, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita gidan ko garin.
Cualquiera que no los reciba, ni oiga sus palabras, al salir de aquella casa o ciudad, sacudan el polvo de sus pies.
15 Gaskiya nake gaya muku, za a fi jin tausayin Sodom da Gomorra a ranar shari’a fiye da wannan gari.
En verdad les digo que en el día del juicio, será más tolerable para la tierra de Sodoma y Gomorra que para aquella ciudad.
16 “Ina aikan ku kamar tumaki a cikin kyarketai. Saboda haka ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.
Recuerden, Yo los envío como a ovejas en medio de lobos. Por tanto sean prudentes como serpientes, y sencillos como palomas.
17 Ku yi hankali da mutane; za su miƙa ku ga majalisa su kuma yi muku bulala a majami’unsu.
Tengan cuidado de los hombres, porque los entregarán a los tribunales y los azotarán en las congregaciones judías.
18 Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Al’ummai.
Los llevarán aun ante gobernadores y reyes por causa de Mí para testimonio a ellos y a los gentiles.
19 Amma sa’ad da suka kama ku, kada ku damu game da abin da za ku faɗa ko kuwa yadda za ku faɗe shi. A lokacin za a ba ku abin da za ku faɗa,
Cuando los entreguen, no se preocupen en cuanto a cómo o qué dirán, porque en esa hora se les dará lo que deben decir.
20 gama ba ku ba ne kuke magana, amma Ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku.
Porque no son ustedes quienes hablan, sino el Espíritu de su Padre es Quien habla por ustedes.
21 “Ɗan’uwa zai ci amanar ɗan’uwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa;’ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.
El hermano entregará a su hermano a muerte, y el padre al hijo. Los hijos se rebelarán contra los padres y los matarán.
22 Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto.
Ustedes serán aborrecidos por todos a causa de mi Nombre, pero el que persevere hasta el fin será salvo.
23 Sa’ad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo.
Cuando los persigan en esta ciudad huyan a la otra. Porque en verdad les digo: No terminarán ustedes de recorrer las ciudades de Israel, hasta cuando venga el Hijo del Hombre.
24 “Ɗalibi ba ya fin malaminsa, haka ma, bawa ba ya fin maigidansa.
Un discípulo no está por encima del maestro, ni un esclavo por encima de su amo.
25 Ya isa wa ɗalibi yă zama kamar malaminsa, haka ma bawa kamar maigidansa. In har an kira wanda yake kan gida Be’elzebub, me za su ce game da mutanen gidansa?
Basta al discípulo que sea como su maestro, y al esclavo como su señor. Si al amo de la casa [lo] llamaron Beelzebul, ¡cuánto más a los de su casa!
26 “Saboda haka kada ku ji tsoronsu. Ba abin da yake a rufe da ba za a tone ba, ko kuwa a ɓoye da ba za a bayyana ba.
Así que, no les teman, porque nada hay encubierto que no se manifieste, ni oculto que no se sepa.
27 Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki.
Lo que les digo en la oscuridad díganlo en la luz, y lo que oyen al oído proclámenlo desde las azoteas.
28 Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta. (Geenna )
No teman a los que matan el cuerpo pero no pueden matar el alma. Teman más bien al que puede destruir el alma y el cuerpo en el infierno. (Geenna )
29 Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku.
¿No se venden dos pajarillos por un centavo? A pesar de eso, ni uno de ellos cae a tierra sin [que lo permita ]el Padre de ustedes.
30 Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su.
En cuanto a ustedes, aun todos los cabellos de la cabeza están contados.
31 Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.
Así que, no teman, más valen ustedes que muchos pajarillos.
32 “Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama.
Cualquiera, pues, que me confiese delante de los hombres, Yo también lo confesaré delante de mi Padre celestial.
33 Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama.
Pero cualquiera que me niegue delante de los hombres, Yo también lo negaré delante de mi Padre celestial.
34 “Kada fa ku ɗauka na zo ne don in kawo salama a duniya. A’a, ban zo don in kawo salama ba, sai dai takobi.
No piensen que vine a traer paz a la tierra. No vine a traer paz, sino espada.
35 Gama na zo ne in sa, “‘gāba tsakanin mutum da mahaifinsa,’ya da mahaifiyarta, matar ɗa da surukarta,
Porque vine para poner en enemistad al hombre contra su padre, a la hija contra su madre, y a la nuera contra su suegra.
36 abokan gāban mutum, za su zama mutanen gidansa ne.’
Los enemigos del hombre serán los de su casa.
37 “Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba;
El que ama a padre o madre más que a Mí, no es digno de Mí. El que ama a hijo o hija más que a Mí, no es digno de Mí.
38 duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba.
El que no toma su cruz y sigue tras Mí, no es digno de Mí.
39 Duk mai son adana ransa zai rasa shi, duk wanda kuwa ya rasa ransa saboda ni zai same shi.
El que halla su vida la perderá, y el que pierde su vida por causa de Mí, la hallará.
40 “Wanda ya karɓe ku, ya karɓe ni ne, wanda kuma ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.
El que los recibe a ustedes, me recibe a Mí, y el que me recibe, recibe al que me envió.
41 Duk wanda ya karɓi annabi don shi annabi ne, zai sami ladar annabi, duk kuwa wanda ya karɓi mutum mai adalci don shi mai adalci ne, zai sami ladar mai adalci.
El que recibe a un profeta por el nombre de profeta, recibirá recompensa de profeta, y el que recibe a un justo por el nombre de justo, recibirá recompensa de justo.
42 In kuma wani ya ba wa ɗaya daga cikin ƙananan nan ko da kwaf ruwan sanyi ne kan shi almajirina ne, gaskiya nake gaya muku, ba shakka ba zai rasa ladarsa ba.”
Cualquiera que dé a beber tan solo un vaso de agua fría a uno de estos pequeños por cuanto es discípulo, en verdad les digo que de ningún modo perderá su recompensa.