< Mattiyu 1 >
1 Tarihin da aka rubuta game da asalin Yesu Kiristi ɗan Dawuda, ɗan Ibrahim.
Inyerte tisa kuwunun Yisa Kristi, usaun in Dauda, usaun Ibrahim.
2 Ibrahim ya haifi Ishaku, Ishaku ya haifi Yaƙub, Yaƙub ya haifi Yahuda da’yan’uwansa,
Ibrahim wadi uchifin Ishaku, a Ishaku uchifi Yakubu, a Yakubu uchifin Yahuda nin nuanamẹ.
3 Yahuda ya haifi Ferez da Zera, waɗanda Tamar ce mahaifiyarsu; Ferez ya haifi Hezron, Hezron ya haifi Ram,
uchifin Parez nin Zaraha unuzun kumantin Tamar, Parez uchifin Hasruna, Hasruna uchifin Arama.
4 Ram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon,
Arama wa maru Aminadaba ku, Aminadaba mara Nahashuna ku, Nahashuna mara.
5 Salmon ya haifi Bowaz, wanda Rahab ce mahaifiyarsa, Bowaz ya haifi Obed, wanda Rut ce mahaifiyarsa, Obed ya haifi Yesse,
Salmuna ku, Saalmuna mara Bu'az ku unuzu kumantin Rahab, Bu'az mara Ubida ku, unuzu kumantin Ruth, Ubida mara Jesẹ ku.
6 Yesse kuwa ya haifi Sarki Dawuda. Dawuda ya haifi Solomon, wanda matar Uriya ce mahaifiyarsa.
Jesẹ wadi uchif ngoh Dauda, Dauda mara Solomon ku, unuzun kitin wanin Uriya.
7 Solomon ya haifi Rehobowam, Rehobowam ya haifi Abiya, Abiya ya haifi Asa,
Solomon wadi uchifin Rehoboam, Rehoboam mara Abija ku, Abija mara Asa ku.
8 Asa ya haifi Yehoshafat, Yehoshafat ya haifi Yehoram, Yehoram ya haifi Azariya,
Asa mara Jehoshapat, Jehoshapat mara Joram ku, Joram wa maru Uzaya ku.
9 Azariya ya haifi Yotam, Yotam ya haifi Ahaz, Ahaz ya haifi Hezekiya,
Uzaya mara Jotham ku, Jotham wa di uchifin Ahaz, Ahaz mara Hizikiya ku.
10 Hezekiya ya haifi Manasse, Manasse ya haifi Amon, Amon ya haifi Yosiya,
Hizikiya mara Manasa ku, Manasa mara Amon ku, Amon mara Josaya ku.
11 Yosiya kuma ya haifi Yekoniya da’yan’uwansa a lokacin da aka kwashe su zuwa bauta a Babilon.
Josaya mara Jikoniya ku nin nuanẹ kubin kifuzun nonon Israila udumun u Babila.
12 Bayan an kwashe su zuwa bauta a Babilon. Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ya haifi Zerubbabel,
Kimalin kifuzu udu u Babilẹ, Jikoniya mara Shealtiel ku, Shealtiel mara Zarubabel ku.
13 Zerubbabel ya haifi Abiyud, Abiyud ya haifi Eliyakim, Eliyakim ya haifi Azor,
Zarubabel mara Abiud ku, Abiud mara ilayikum ku, Ilayakum mara Azor ku.
14 Azor ya haifi Zadok, Zadok ya haifi Akim, Akim kuma ya haifi Eliyud,
Azor mara Zadok ku, Zadok wadi uchifin Achim, Achim wadi uchifin Eliud.
15 Eliyud ya haifi Eleyazar, Eleyazar ya haifi Mattan, Mattan ya haifi Yaƙub,
Eliud wadi uchifin Ileza, Ileza mara Mattana ku, Mattana mara Yakub ku.
16 Yaƙub ya haifi Yusuf, mijin Maryamu, wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Kiristi.
Yakub mara Yusufu ku, ulessin Maremu ulenge na awa maru Yisa ku unuzu kitene, ulenge na idin yicighe Kristi.
17 Ta haka akwai zuriya goma sha huɗu ke nan duka-duka daga lokacin Ibrahim zuwa lokacin Dawuda, goma sha huɗu kuma daga Dawuda zuwa bauta a Babilon, goma sha huɗu kuma daga bauta a Babilon zuwa Kiristi.
Vat naji aji uyiru kitin Ibrahim udak kubin Dauda aji likure nin na nassari, uyiru kubin Dauda udu kubi ko na iwa yiru nani udu u Babila aji likure nin na nassari.
18 Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
Kumanti Yisa Kristi wadi nafo nengenari. Unene Maremu wa yiinnin aba su ilugma nin Yusufu, a na isa su ilugma ba iseghe nin liburin in Fip Kutellẹ.
19 Yusuf mijinta, da yake shi mai adalci ne, bai so yă ba ta kunya, yă tone mata asiri a fili ba, sai ya yi tunani yă sake ta a ɓoye.
Ulesse Yusufu wadi unan fiu Kutellẹ, na awa di nin su a nighe ncin nan nya nanit ba. Bara nani awa di nin su asughe likire.
20 Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne.
Na awa di kpilizu ni leli imone, unan kadura Kutellẹ da kitime nan nya namoro, aworo, YUsufu, uusaun Dauda, na uwa lanza fiu in woru uyiru Maremu ku a so uwanife ba, bara fisudu fo na fidi nanya liburi me unuzu kitin Ruhu ulauwari.
21 Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”
Ama maru gono, uma yichu lisame Yisa, bara amma tuchu anit me nanya nalapi mine.”
22 Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa,
Vat nilele wase bara inan kulo imon ile na Cikilari wa belli nnu nanan liru nin nu me, a woro.
23 “Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel” (wanda yake nufin “Allah tare da mu”).
“Yenen kubura ma ti liburi kumaru gono, ima yicu lisame immanuel, uninare Kutellẹ ligowe nan ghirik.”
24 Da Yusuf ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala’ikan Ubangiji, ya ɗauki Maryamu zuwa gida a matsayin matarsa.
Yusufu fita nanyan moro me asu nafo na unan kaduran Cikilare na bellinghe, ayira Maremmu ku aso uwanime.
25 Amma bai kwana da ita ba, sai bayan da ta haifi ɗan. Ya kuwa sa masa suna Yesu.
Nanya nani iwa so lisosin nless nin wanii, na izuro ba udu kubi kongo na awa maru. A na lisan gone Yisa.