< Markus 9 >
1 Ya kuma ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”
耶稣又对他们说:“告诉你们实话,站在这里的有些人,在死前必定会看见上帝的天国带着力量降临人间。”
2 Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna tare da shi, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, suka kasance su kaɗai a wurin. A can aka sāke kamanninsa a gabansu.
六天后,耶稣带着彼得、雅各和约翰爬上高山,然后在他们面前改变了形象。
3 Tufafinsa suka zama fari suna ƙyalli, fiye da yadda wani a duniya zai iya yi su.
他的衣服闪耀着洁白的光芒,人间任何漂白的布料都比不上这样的白色。
4 Iliya da Musa suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.
然后以利亚和摩西现身在他们面前,跟耶稣谈话。
5 Bitrus ya ce wa Yesu, “Rabbi, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”
彼得对耶稣说:“拉比,我们在这里太好了!我们可以搭三个庇护所,一个为你,一个为摩西,一个为以利亚。”
6 (Bai san abin da zai faɗa ba ne, gama sun tsorata ƙwarai.)
(彼得其实不知道该说什么,因为他们都非常害怕!)
7 Sai wani girgije ya bayyana, ya rufe su, wata murya kuma ta fito daga girgijen, ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna, ku saurare shi!”
有一片云朵飘到他们头顶,云中传来一个声音:“这是吾子,我之所爱,你们要听他。”
8 Farat ɗaya, da suka waiwaya, ba su ƙara ganin kowa tare da su ba, sai dai Yesu.
门徒们正在张望之际,忽然就看不见别的人了,只有耶稣和他们在一起。
9 Da suna saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu.
他们下山的时候,耶稣吩咐他们,人子死而复生之前,不要将所见告诉其他人。
10 Suka riƙe wannan zance a ɓoye tsakaninsu, suna tattaunawa ko mece ce ma’anar “tashi daga matattu.”
门徒把这句话记在心里,但她们彼此争论死而复生是什么意思。
11 Suka tambaye shi, suka ce, “Don me malaman dokoki suke cewa, sai Iliya ya fara zuwa?”
他们就问耶稣:“宗教老师为什么说以利亚必须先来呢?”
12 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya ne, Iliya zai zo da fari, yă kuma mayar da dukan abubuwa. Don me kuma aka rubuta cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahala sosai, kuma a ƙi shi?
耶稣说:“的确,以利亚要先来做好准备,但为什么经书中又说人子要受许多苦,被人侮辱呢?
13 Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, kuma suka yi duk abin da suka ga dama da shi, kamar yadda aka rubuta game da shi.”
但我告诉你们,以利亚已降临,他们任意地虐待他,就像经书中记载的那样。”
14 Da suka dawo wurin sauran almajiran, sai suka ga babban taro kewaye da su, malaman dokoki suna gardama da su.
他们回到其他门徒那里,看见一大群人围着他们,还有宗教老师在和他们辩论。
15 Nan take da dukan mutanen suka ga Yesu, sai suka cika da mamaki, suka ruga da gudu don su gai da shi.
众人看见了耶稣都很惊奇,就跑上前去向他问候。
16 Ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi da su?”
他问他们:“你们和他们辩论什么?”
17 Wani mutum a cikin taron ya amsa ya ce, “Malam, na kawo maka ɗana mai wani ruhun da yake hana shi magana.
民众当中有一人回答他:“老师,我把我的儿子带到你这里来,他被恶灵附体,无法说话。
18 Duk lokacin da mugun ruhun ya kama shi, yakan jefa shi a ƙasa. Bakinsa yakan yi kumfa, yă cije haƙorarsa, yakan sa jikinsa ya sandare, yă zama da ƙarfi. Na roƙi almajiranka su fitar da ruhun, amma ba su iya ba.”
无论在哪里,恶灵都会抓住他,把他摔倒,让他口吐白沫、咬牙切齿、浑身僵硬。我请你的门徒把恶灵赶出去,他们却办不到。”
19 Yesu ya ce, “Ya ku zamani marar bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron.”
耶稣回答他们:“唉!这些没有信心的人啊!我在这里必须待到什么时候?我还要忍受你们多久?把他带到我这里来吧。”
20 Sai suka kawo shi. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan sai ya buge yaron da farfaɗiya. Ya fāɗi a ƙasa, yana birgima, bakinsa yana kumfa.
他们把孩子带到他跟前。那恶灵一见耶稣,就立刻让孩子倒在地上抽搐,口吐白沫打滚。
21 Yesu ya tambayi mahaifin yaron ya ce, “Tun yaushe yake haka?” Ya ce, “Tun yana ƙarami.
耶稣问他父亲:“他这样多久了?” 他说:“从小就是这样。
22 Ya sha jefa shi cikin wuta, ko ruwa don yă kashe shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.”
恶灵经常把他扔在火中想要烧死他,把他扔在水中想要淹死他。如果你能,求你可怜我们,帮助我们。”
23 Yesu ya ce, “‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata.”
耶稣说:“为什么你要说‘如果你能?’有信心者必有力量!”
24 Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, “Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!”
孩子的父亲立刻喊着说:“我真的信你!但我的信心不够,求你帮助我。”
25 Da Yesu ya ga taron suna zuwa can a guje, sai ya tsawata wa mugun ruhun ya ce, “Kai ruhun kurma, da na bebe, na umarce ka, ka fita daga cikinsa, kada kuma ka ƙara shigarsa.”
耶稣见民众围拢了来,开始斥责那恶灵说:“让人聋哑的恶灵,我命令你从他身上出来,不要再回去。”
26 Sai ruhun ya yi ihu, ya buge shi da ƙarfi da farfaɗiya, ya fita. Yaron ya kwanta kamar matacce, har mutane da yawa suka ce, “Ai, ya mutu.”
那恶灵喊叫着,让这孩子陷入剧烈的抽搐,然后就从他身体里被驱赶出来。孩子仿佛已经死了,许多人都说:“他死了!”
27 Amma Yesu ya kama shi a hannu ya ɗaga, ya kuwa tashi tsaye.
但耶稣拉着男孩的手,扶他起来,他就站起来了。
28 Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da shi ba?”
然后耶稣走进屋子,门徒私下问他说:“为什么我们就无法驱赶那恶灵呢?”
29 Ya amsa ya ce, “Sai da addu’akaɗai irin wannan yakan fita.”
耶稣对他们说:“如果不祈祷,这种恶灵无法驱赶。”
30 Suka bar wurin suka bi ta Galili. Yesu bai so wani yă san inda suke ba,
他们离开了,途经加利利。耶稣不想让任何人知道他们的行踪,
31 gama yana koya wa almajiransa. Ya ce musu, “Za a ci amanar Ɗan Mutum, a ba da shi ga hannun mutane. Za su kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi.”
因为他正在教导门徒。他对他们说:“人子将遭到背叛,送到人类的官府,他们会杀害他,但他在死后三天就会复活。”
32 Amma ba su fahimci abin da yake nufi ba, suka kuma ji tsoro su tambaye shi game da wannan.
门徒不明白这话,又不敢询问。
33 Suka iso Kafarnahum. Da yana cikin gida, sai ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi a hanya?”
他们来到迦百农的一个房间内住下。耶稣问他们:“你们在路上讨论什么呢?”
34 Amma suka yi shiru, don a hanya suna gardama ne, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma?
门徒不说话,因为他们在路上争论谁最重要。
35 Da Yesu ya zauna, sai ya kira Sha Biyun ya ce, “In wani yana so yă zama na fari, dole yă zama na ƙarshe duka, da kuma bawan kowa.”
耶稣坐下,唤来十二门徒,对他们说:“一个人如果想为首,就必在众人中成为最后,做众人的仆人。”
36 Ya ɗauki wani ƙaramin yaro ya sa yă tsaya a tsakiyarsu. Ya ɗauke shi a hannunsa, ya ce musu,
耶稣拉过一个小孩子来,叫他站在门徒中间,然后把孩子抱起来拥抱着他,对门徒说:
37 “Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”
“凡因我之名迎接这样的小孩子,就是迎接我,这样的人并非在迎接我,而是迎接那派我过来的人。”
38 Yohanna ya ce, “Malam mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, sai muka ce yă daina, domin shi ba ɗaya daga cikinmu ba ne.”
约翰对耶稣说:“老师,我们看见有人以你之名驱鬼,我们想要制止他,因为他不是我们中的一员。”
39 Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ba wanda yake yin ayyukan banmamaki a cikin sunana, nan take yă faɗi wani abu mummuna game da ni.
耶稣说:“不要制止他,因为没有人能在以我之名行神迹的同时又诅咒我。
40 Gama duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne.
不反对我们,就是支持我们。
41 Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ba ku ruwan sha a sunana, saboda ku na Kiristi ne, lalle, ba zai rasa ladarsa ba.
无论是谁,若以我之名给你一杯水,他这样做只因你属于基督,就不会失掉赏赐,相信我。
42 “Idan kuma wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan’yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyarsa, a jefa shi cikin teku.
但如果有人让这些信我的小孩子犯罪,最好就是在他的脖子上拴一块大磨石,让其淹没在海里。
43 In hannunka yana sa ka yin zunubi, yanke shi. Ai, gwamma ka shiga rai da hannu ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta, inda ba a iya kashe wutar ba, da hannuwanka biyu. (Geenna )
如果你的一只手让你犯罪,把它砍下来。残疾却能进永生,总好过双手下哥和拿,堕入不灭的哥和拿之火。 (Geenna )
45 In kuma ƙafarka tana sa ka yin zunubi, yanke ta. Ai, gwamma ka shiga rai da ƙafa ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da ƙafafunka biyu. (Geenna )
如果你的一只脚让你犯罪,把它砍下来。瘸腿却能获得永生,总好过两脚齐全却被丢在哥和拿。 (Geenna )
47 In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu, (Geenna )
如果你的一只眼睛让你犯罪,把它挖出来。一只眼睛进入上帝之国,总好过两眼齐全被丢进哥和拿, (Geenna )
48 inda “‘tsutsotsinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a iya kashewa.’
哥和拿里的虫不死,火永不灭。
49 Za a tsarkake kowa da wuta.
每个人会像被‘盐腌’一样,被火灼烧。
50 “Gishiri yana da daɗi, amma in ya rabu da ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da ɗanɗanonsa? Ku kasance da gishiri a cikinku, ku kuma yi zauna lafiya da juna.”
盐是好东西,但如果失去了它的味道,怎样才能让它恢复咸味呢?你们需要像盐一样,彼此和睦地生活。”