< Markus 8 >
1 A kwanakin nan wani taro mai girma ya taru. Tun da yake ba su da abin da za su ci, sai Yesu ya kira almajiransa ya ce,
In those days again, when there was a great multitude, and had nothing to eat; calling his disciples together, he saith to them:
2 “Ina jin tausayin mutanen nan, kwanansu uku ke nan tare da ni, kuma ba su da abin da za su ci.
I have compassion on the multitude, for behold they have now been with me three days, and have nothing to eat.
3 In na sallame su gida da yunwa, za su kāsa a hanya, don waɗansu daga cikinsu sun zo daga nesa.”
And if I shall send them away fasting to their home, they will faint in the way; for some of them came from afar off.
4 Almajiransa suka amsa suka ce, “Amma a ina, a wannan wurin da ba kowa, wani zai iya samun isashen burodi, don a ciyar da su?”
And his disciples answered him: From whence can any one fill them here with bread in the wilderness?
5 Sai Yesu ya yi tambaya ya ce, “Burodi guda nawa kuke da su?” Suka ce, “Bakwai.”
And he asked them: How many loaves have ye? Who said: Seven.
6 Sai ya gaya wa taron su zazzauna a ƙasa. Bayan ya ɗauki burodin nan bakwai, ya yi godiya, sai ya kakkarya, ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutanen, suka kuwa yi haka.
And taking the seven loaves, giving thanks, he broke, and gave to his disciples for to set before them; and they set them before the people.
7 Suna kuma da ƙananan kifaye kaɗan, ya ba da godiya dominsu, ya kuma ce wa almajiran su rarraba musu.
And they had a few little fishes; and he blessed them, and commanded them to be set before them.
8 Mutanen suka ci, suka ƙoshi. Daga baya, almajiran suka tattara gutsattsarin da suka rage cike da kwanduna bakwai.
And they did eat and were filled; and they took up that which was left of the fragments, seven baskets.
9 Wajen maza dubu huɗu ne suka kasance. Da ya sallame su,
And they that had eaten were about four thousand; and he sent them away.
10 sai ya shiga jirgin ruwa tare da almajiransa, suka tafi yankin Dalmanuta.
And immediately going up into a ship with his disciples, he came into the parts of Dalmanutha.
11 Farisiyawa suka zo suka fara yin wa Yesu tambayoyi. Don su gwada shi, sai suka nemi yă nuna musu wata alama daga sama.
And the Pharisees came forth, and began to question with him, asking him a sign from heaven, tempting him.
12 Sai ya ja numfashi mai zurfi ya ce, “Don me wannan zamani yake neman ganin abin banmamaki? Gaskiya nake gaya muku, ba wata alamar da za a ba su.”
And sighing deeply in spirit, he saith: Why doth this generation seek a sign? Amen, I say to you, a sign shall not be given to this generation.
13 Sai ya bar su, ya koma cikin jirgin ruwan, suka ƙetare zuwa ɗaya hayin.
And leaving them, he went up again into the ship, and passed to the other side of the water.
14 Almajiran suka manta su riƙe burodi, sai dai guda ɗaya da suke da shi a cikin jirgin ruwan.
And they forgot to take bread; and they had but one loaf with them in the ship.
15 Yesu ya gargaɗe su ya ce, “Ku yi hankali, ku kuma lura da yistin Farisiyawa da na Hiridus.”
And he charged them, saying: Take heed and beware of the leaven of the Pharisees, and of the leaven of Herod.
16 Suka tattauna wannan da juna, suna cewa, “Don ba mu da burodi ne.”
And they reasoned among themselves, saying: Because we have no bread.
17 Da ya gane abin da suke tattaunawa, sai Yesu ya tambaye su ya ce, “Don me kuke zancen rashin burodi? Har yanzu ba ku gane ko fahimta ba? Zukatanku sun taurare ne?
Which Jesus knowing, saith to them: Why do you reason, because you have no bread? do you not yet know nor understand? have you still your heart blinded?
18 Kuna da idanu, amma kun kāsa gani, kuna da kunnuwa, amma kun kāsa ji? Ba ku tuna ba?
Having eyes, see you not? and having ears, hear you not? neither do you remember.
19 Da na kakkarya burodi guda biyar wa mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?” Suka amsa, “Sha biyu.”
When I broke the five loaves among five thousand, how many baskets full of fragments took you up? They say to him, Twelve.
20 “Da na kuma kakkarya burodin nan bakwai wa mutum dubu huɗu, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?” Suka ce, “Bakwai.”
When also the seven loaves among four thousand, how many baskets of fragments took you up? And they say to him, Seven.
21 Ya ce musu, “Har yanzu ba ku fahimta ba?”
And he said to them: How do you not yet understand?
22 Suka iso Betsaida, sai waɗansu mutane suka kawo wani makaho, suka roƙi Yesu yă taɓa shi.
And they came to Bethsaida; and they bring to him a blind man, and they besought him that he would touch him.
23 Yesu ya kama hannun makahon ya kai shi bayan ƙauyen. Bayan ya tofa miyau a idanun mutumin, ya kuma ɗibiya masa hannuwansa, sai ya tambaye shi ya ce, “Kana iya ganin wani abu?”
And taking the blind man by the hand, he led him out of the town; and spitting upon his eyes, laying his hands on him, he asked him if he saw any thing.
24 Sai ya ɗaga kai ya ce, “Ina ganin mutane, suna kama da itatuwa da suke tafiya.”
And looking up, he said: I see men as it were trees, walking.
25 Yesu ya sāke ɗibiya hannuwansa a idanun mutumin, sai idanunsa suka buɗe, ya sami gani, ya kuma ga kome sarai.
After that again he laid his hands upon his eyes, and he began to see, and was restored, so that he saw all things clearly.
26 Yesu ya sallame shi gida ya ce, “Kada ka shiga cikin ƙauyen.”
And he sent him into his house, saying: Go into thy house, and if thou enter into the town, tell nobody.
27 Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan da suke kewaye da Kaisariya Filibbi. A hanya ya tambaye su ya ce, “Wa, mutane suke ce da ni?”
And Jesus went out, and his disciples, into the towns of Caesarea Philippi. And in the way, he asked his disciples, saying to them: Whom do men say that I am?
28 Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu Iliya, waɗansu kuma har wa yau sun ce, ɗaya daga cikin annabawa.”
Who answered him, saying: John the Baptist; but some Elias, and others as one of the prophets.
29 Sai ya yi tambaya ya ce, “Amma ku fa, wa kuke ce da ni?” Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi.”
Then he saith to them: But whom do you say that I am? Peter answering said to him: Thou art the Christ.
30 Yesu ya gargaɗe su kada su gaya wa kowa kome a kansa.
And he strictly charged them that they should not tell any man of him.
31 Sai ya fara koya musu cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahaloli da yawa, dattawa, manyan firistoci da malaman dokoki kuma su ƙi shi. Dole kuma a kashe shi, bayan kwana uku kuma, yă tashi.
And he began to teach them, that the Son of man must suffer many things, and be rejected by the ancients and by the high priests, and the scribes, and be killed: and after three days rise again.
32 Ya yi wannan zance a sarari. Sai Bitrus ya jawo shi gefe, ya fara tsawata masa.
And he spoke the word openly. And Peter taking him, began to rebuke him.
33 Amma da Yesu ya juya ya dubi almajiransa, sai ya tsawata wa Bitrus ya ce, “Tashi daga nan Shaiɗan! Ba ka da al’amuran Allah a zuciyarka, sai na mutane.”
Who turning about and seeing his disciples, threatened Peter, saying: Go behind me, Satan, because thou savorest not the things that are of God, but that are of men.
34 Sai ya kira taron wurinsa tare da almajiransa ya ce, “Duk wanda zai bi ni, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa yă bi ni.
And calling the multitude together with his disciples, he said to them: If any man will follow me, let him deny himself, and take up his cross, and follow me.
35 Domin duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma bishara, zai same shi.
For whosoever will save his life, shall lose it: and whosoever shall lose his life for my sake and the gospel, shall save it.
36 Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa?
For what shall it profit a man, if he gain the whole world, and suffer the loss of his soul?
37 Ko kuma, me mutum zai bayar a musayar ransa?
Or what shall a man give in exchange for his soul?
38 Duk wanda ya ji kunyata, da na kalmomina a wannan zamani na fasikanci da zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da ya shiga cikin ɗaukakar Ubansa, tare da tsarkakan mala’iku.”
For he that shall be ashamed of me, and of my words, in this adulterous and sinful generation: the Son of man also will be ashamed of him, when he shall come in the glory of his Father with the holy angels.