< Markus 6 >

1 Yesu ya tashi daga can ya tafi garinsa, tare da almajiransa.
耶穌從那裏起身,來到自己的家鄉,門徒也跟了他來。
2 Da Asabbaci ya kewayo, sai ya fara koyarwa a cikin majami’a, mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki. Suna tambaya, “Ina mutumin nan ya sami waɗannan abubuwa? Wace hikima ce wannan da aka ba shi, har da yana yin ayyukan banmamaki haka!
到了安息日,他便開始在會堂裏教訓人:眾人聽了,就驚訝說:「他這一切是從那裏來的呢﹖所賜給他的是什麼樣的智慧﹖怎麼藉他的手行出這樣的奇能﹖
3 Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗan’uwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe,’yan’uwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa.
這人不就是那個木匠嗎﹖他不是瑪利亞的兒子,雅各伯、若瑟、猶達、西滿的兄弟嗎﹖他的姊妹不是也都在我們這裏嗎﹖」他們便對他起了反感。
4 Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa kaɗai, da kuma cikin’yan’uwansa, da cikin gidansa ne, annabi ba shi da daraja.”
耶穌對他們說:「先知除了在自己的本鄉、本族、和本家外,是沒有不受尊敬的。」
5 Bai iya yin ayyukan banmamaki a wurin ba, sai dai ɗibiya hannuwansa da ya yi a kan mutane kima da suke da cututtuka, ya kuwa warkar da su.
耶穌耶穌在那裏不能行什麼奇能,祇能給少數的幾個病人覆手,治好了他們。
6 Ya kuwa yi mamaki ƙwarai don rashin bangaskiyarsu. Sai ya Yesu zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.
因他們的無信心而感到詑異,遂周遊各村施教去了。
7 Ya kira Sha Biyun nan wurinsa, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko bisa mugayen ruhohi.
耶穌叫來十二門徒,開始派遣他們兩個兩個地出去,賜給他們制服邪魔的權柄,
8 Ga dai umarnansa, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, sai dai sanda ba burodi, ba jaka, ba kuɗi a ɗamararku.
囑咐他們除了一根棍杖外,什麼也不要帶:不要帶食物,不要帶口袋,也不要在腰帶裏帶銅錢;
9 Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa.
卻要穿鞋,不要穿兩件內衣。
10 Duk sa’ad da kuka shiga wani gida, ku zauna nan sai kun bar garin.
又對他們說:「你們無論在那裏,進了一家,就住在那裏,直到從那裏離去;
11 In kuwa a wani wuri ba a karɓe ku, ba a kuwa saurare ku ba, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita, a matsayin shaida a kansu.”
無論何處不接待你們,或不聽從你們,你們就從那裏出去,拂去你們腳下的塵土,作為反對他們的證據。」
12 Suka fita, suna yi wa’azi, suna ce wa mutane su tuba.
他們就出去宣講,使人悔改,
13 Suka fitar da aljanu da yawa, suka shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka kuwa warkar da su.
並驅逐了許多魔鬼且給許多病人傅油,治好了他們。
14 Sarki Hiridus ya ji wannan labari, gama sunan Yesu ya bazu a ko’ina. Waɗansu suna cewa, “An tashe Yohanna Mai Baftisma daga matattu ne, shi ya sa yana da ikon yin ayyukan banmamakin nan.”
因為耶穌的名聲傳揚出去,黑落德王也聽到了。有人說:「洗者若翰從死者中復活了,為此這些奇能才能在他身上運行。」
15 Waɗansu suka ce, “Ai, Iliya ne.” Har wa yau waɗansu suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawan dā.”
但也有人說:「他是厄里亞。」更有人說:「他是先知,好像古先知中的一位。」
16 Amma da Hiridus ya ji haka, sai ya ce, “Ai, Yohanna ne, mutumin da na yanke masa kai, shi ne ya tashi daga matattu!”
黑落德聽了,卻說:「是我所斬首的若翰復活了!」
17 Gama Hiridus da kansa ya ba da umarni a kama Yohanna, ya kuma sa aka daure shi, aka sa shi a kurkuku. Ya yi haka saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, wadda ya aura.
原來這個黑落德,為了他兄弟, 斐理伯的妻子黑落狄雅的緣故,因為他娶了她為妻,曾遣人逮捕了若翰,把他押在監裏;
18 Gama Yohanna ya yi ta ce wa Hiridus, “Ba daidai ba ne bisa ga doka, ka ɗauki matar ɗan’uwanka.”
因為若翰曾寫信給黑落德說:「你不可佔有你兄弟的妻子。」
19 Saboda haka, Hiridiyas ta ƙulla munafunci game da Yohanna, ta kuma so ta kashe shi. Amma ba tă iya ba,
黑落狄雅便懷恨他,願意殺害,他只是不能,
20 domin Hiridus yana jin tsoron Yohanna, ya kuma kāre shi sosai, da sanin cewa shi mutum ne mai adalci da kuma mai tsarki. Duk sa’ad da Hiridus ya saurari Yohanna, yakan damu ƙwarai, duk da haka, yakan so yă ji shi.
因為黑落德敬畏若翰,知道他是一個正直聖潔的人,曾保全了他;幾時聽他講道,就甚覺困怠惑,但仍樂意聽他。
21 A ƙarshe, ta sami zarafi. A ranar murnar haihuwar Hiridus, ya yi biki domin hakimansa, da shugabannin sojojinsa, da kuma manyan mutanen Galili.
好機會的日子到了:當黑落德在自己的生日上,為自己的重要官員、和加里肋亞的顯要,設了筵席的時候,
22 Sa’ad da diyar Hiridiyas ta shigo, ta kuma yi rawa, sai ta gamshi Hiridus tare da baƙinsa. Sai Sarkin ya ce wa yarinyar, “Ki tambaye ni kome da kike so, ni kuwa zan ba ki.”
那個黑落狄雅的女兒便進來跳舞,獲得了黑落德和同席人的歡心。王便對女孩子說:「你要什麼,向我求罷! 我必賜給你!」
23 Ya yi mata alkawari da rantsuwa cewa, “Duk abin da kika roƙa, zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.”
又對她發誓說:「無論你求我什麼,就是我王國的一半我也必定給你!」
24 Sai ta fita ta ce wa mahaifiyarta, “Me zan roƙa?” Ta ce, “Kan Yohanna Mai Baftisma.”
她便出去問她的母親說:「我該求什麼﹖」她母親答說:「洗者若翰的頭。」
25 Nan da nan, sai yarinyar ta yi hanzari zuwa wajen sarki da roƙon, “Ina so ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a cikin tasa, yanzu-yanzu nan.”
她; 便立刻進去,到王面前要求說:「我要你把洗者若翰的頭,放在盤子裏給我! 」
26 Sai sarki ya yi baƙin ciki ƙwarai, amma saboda rantsuwar da kuma baƙinsa, bai so yă hana ta ba.
王遂十分憂鬱;但為了誓言和同席的人,不願對她食言,
27 Nan take, sai ya aiki mai aiwatar da kisa da umarni ya kawo kan Yohanna. Mutumin ya je ya yanke kan Yohanna a kurkuku.
王遂即差遣衛兵,吩咐把若翰的頭送來。衛兵便去,在監斬了若翰的頭,
28 Ya kuma kawo kan a tasa ya ba yarinyar. Ita kuma ta ba wa mahaifiyarta.
把他的頭放在盤子裏送來,交給了那女孩子,那女孩子便交口了自己的母親。
29 Da almajiran Yohanna suka sami labari, sai suka zo suka ɗauki jikinsa suka binne a kabari.
若翰的門徒聽說了,就來領去了他的屍身,把他安葬在墳墓裏。
30 Manzannin suka taru kewaye da Yesu, suka ba shi rahoton duk abin da suka yi, da kuma suka koyar.
宗徒們聚集到耶穌前,將他們所作所教的一切,都報告給耶穌。
31 To, saboda mutane da yawa suna kai da kawowa, har ma ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita inda ba kowa don ku ɗan huta.”
耶穌向他們說:「你們來,私下到荒野的地方去休息一會兒!」這是因為來往的人很多, 以致他們連吃飯的工夫也沒有。
32 Sai suka tafi a jirgin ruwa su kaɗai, inda ba kowa.
他們便乘船私下往荒野的地方去了。
33 Amma mutane da yawa waɗanda suka ga tashinsu, sun gane su, sai suka ruga da gudu a ƙafa daga dukan birane, suka riga su kaiwa can.
人看見他們走了。許多人也知道他們要去的地方,便從各城徒步,一起往那裏奔走,且在他們以先到了。
34 Da Yesu ya sauka, ya ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu, gama kamar tumaki suke waɗanda ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.
耶穌一下船,看見一大夥群眾,就對他們動了憐憫的心,因為他們好像沒有牧人的羊, 遂開口教訓他們許多事。
35 A lokacin nan yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce masa, “Wurin nan ƙauye ne, ga shi kuma lokaci ya ƙure.
時間己經很晚了,他的門徒來到他跟前說:「這地方是荒野,且時間已經很晚了,
36 Ka sallami mutanen su shiga ƙauyukan da suke kurkusa, su sayi wa kansu wani abu, su ci.”
請你遣散他們,好叫他們往四周田舍村莊去,各自買東西吃。」
37 Sai ya amsa ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.” Suka ce masa, “Ai, wannan zai ɗauki albashin wata takwas na mutum! Mu je mu kashe yawan kuɗin nan a burodi mu ba su su ci?”
耶穌卻回答說:「你們自己給他們吃的罷!」門徒向他說:「我們去買兩百塊銀錢的餅給他們吃嗎﹖」
38 Sai ya yi tambaya ya ce, “Burodi nawa kuke da su? Je ku duba.” Da suka duba, sai suka ce, “Biyar da kifi biyu.”
耶穌問他們說:「你們有多少餅﹖去看看!」他們一知道了,就說:「五個餅,兩條魚。」
39 Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa.
於是耶穌吩咐他們,叫眾人一夥一夥地坐在青草地上。
40 Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin.
人們就一組一組地坐下:或一百人,或五十人。
41 Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka.
耶穌拿起那五個餅和那兩條魚來,舉目向天,祝福了,把餅擘開,遞給門徒,叫他們擺在眾人面前,把兩條魚也分給眾人。
42 Kowa ya ci, ya ƙoshi,
眾人吃了,也都飽了;
43 almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu.
人就把剩餘的碎塊收了滿滿十二筐;還有魚的碎塊。
44 Yawan mutanen da suka ci kuwa maza dubu biyar ne.
吃餅的,男人就有五千。
45 Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yă sallami taron.
耶穌即刻催迫門徒上船,先到那邊貝特賽達去,這期間他遣散了群眾。
46 Bayan ya bar su, sai ya hau kan dutse don yă yi addu’a.
耶穌辭別了眾人之後,便往山上祈禱去了。
47 Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai.
到了夜晚,船已在海中,耶穌獨自在陸地上。
48 Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su,
他看見門徒艱苦地在搖櫓,他們正遇著逆風。約夜間四更時分,耶穌步行海面,朝著他們走來,有意越過他們。
49 amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu,
門徒看見他步行海上,以為是個妖怪,就都驚叫起來,
50 domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata. Nan da nan ya yi magana da su ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”
因為眾人都看見了他,遂都驚慌不已。耶穌連忙與他們講話,向他們說:「放心! 是我。不要怕!」
51 Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki,
遂到他們那裏上了船,風就停了。他們心中越發驚奇,
52 gama ba su fahimci al’amarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare.
因為他們還不明白關於增餅的事,他們的心還是遲鈍。
53 Da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret, suka daure jirgin a ƙugiya.
他們渡到了陸地,來到革乃撒勒,就靠了岸。
54 Da fitowarsu daga jirgin, sai mutane suka gane Yesu.
他們剛一下船,人立刻認出他來。
55 Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake.
便跑遍那全地域,開始用床把有病的人,抬到聽說耶穌所在的地方去。
56 Duk inda ya shiga, cikin ƙauyuka, birane ko karkara, sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yă bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke.
凡耶穌所到的地方,或村莊,或城市,或鄉間,人都把患病的人放在街道上,求耶穌容許他們,至少摸摸他的衣邊;凡摸到他的,就都痊癒了。

< Markus 6 >