< Markus 3 >

1 Wani lokaci, da ya sāke shiga majami’a, sai ga wani mutum mai shanyayyen hannu.
He entered again into the synagogue, and there was a man there whose hand was withered.
2 Waɗansu daga cikin mutane suna neman dalilin zargin Yesu, sai suka zuba masa ido, su ga ko zai warkar da shi a ranar Asabbaci.
They watched him, whether he would heal him on the Sabbath day, that they might accuse him.
3 Yesu ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.”
He said to the man whose hand was withered, “Stand up.”
4 Sai Yesu ya tambaye su ya ce, “Me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri, ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a yi kisa?” Amma suka yi shiru.
He said to them, “Is it lawful on the Sabbath day to do good or to do harm? To save a life or to kill?” But they were silent.
5 Sai ya kalle su da fushi, don taurin zuciyarsu ya ɓata masa rai sosai. Sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
When he had looked around at them with anger, being grieved at the hardening of their hearts, he said to the man, “Stretch out your hand.” He stretched it out, and his hand was restored as healthy as the other.
6 Sai Farisiyawa suka fita, suka fara ƙulla shawara da mutanen Hiridus yadda za su kashe Yesu.
The Pharisees went out, and immediately conspired with the Herodians against him, how they might destroy him.
7 Yesu da almajiransa suka janye zuwa tafkin, taro mai yawa kuwa daga Galili ya bi shi.
Jesus withdrew to the sea with his disciples; and a great multitude followed him from Galilee, from Judea,
8 Mutane da yawa daga Yahudiya, da Urushalima, da Edom, da kuma yankunan da suke ƙetaren Urdun, da kewayen Taya, da Sidon suka zo wurinsa, don sun ji dukan abubuwan da yake yi.
from Jerusalem, from Idumaea, beyond the Jordan, and those from around Tyre and Sidon. A great multitude, hearing what great things he did, came to him.
9 Saboda taron, sai ya ce wa almajiransa su shirya masa ƙaramin jirgin ruwa, don kada mutane su matse shi.
He spoke to his disciples that a little boat should stay near him because of the crowd, so that they wouldn’t press on him.
10 Gama ya warkar da mutane da yawa, masu cututtuka suka yi ta ƙoƙarin zuwa gaba, don su taɓa shi.
For he had healed many, so that as many as had diseases pressed on him that they might touch him.
11 Duk sa’ad da mugayen ruhohi suka gan shi, sai fāɗi a gabansa, su ɗaga murya, su ce, “Kai Ɗan Allah ne.”
The unclean spirits, whenever they saw him, fell down before him and cried, “You are the Son of God!”
12 Amma yakan tsawata musu, kada su shaida ko wane ne shi.
He sternly warned them that they should not make him known.
13 Yesu ya hau gefen wani dutse, ya kira waɗanda yake so, suka kuma zo wurinsa.
He went up into the mountain and called to himself those whom he wanted, and they went to him.
14 Ya naɗa sha biyu, ya kira su manzanni don su kasance tare da shi, domin kuma yă aike su yin wa’azi,
He appointed twelve, that they might be with him, and that he might send them out to preach
15 don kuma su sami ikon fitar da aljanu.
and to have authority to heal sicknesses and to cast out demons:
16 Ga sha biyun da ya naɗa. Siman (wanda ya ba shi suna Bitrus);
Simon (to whom he gave the name Peter);
17 Yaƙub ɗan Zebedi da kuma ɗan’uwansa Yohanna (ga waɗannan kuwa ya sa musu suna Buwarnajis, wato, “’ya’yan tsawa”);
James the son of Zebedee; and John, the brother of James, (whom he called Boanerges, which means, Sons of Thunder);
18 Andarawus, Filibus, Bartolomeyu, Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Taddayus, Siman wanda ake kira Zilot,
Andrew; Philip; Bartholomew; Matthew; Thomas; James, the son of Alphaeus; Thaddaeus; Simon the Zealot;
19 da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.
and Judas Iscariot, who also betrayed him. Then he came into a house.
20 Sai Yesu ya shiga wani gida, taro kuma ya sāke haɗuwa, har shi da almajiransa ma ba su sami damar cin abinci ba.
The multitude came together again, so that they could not so much as eat bread.
21 Da’yan’uwansa suka sami wannan labari, sai suka tafi don su dawo da shi, suna cewa, “Ai, ya haukace.”
When his friends heard it, they went out to seize him; for they said, “He is insane.”
22 Malaman dokokin da suka zo daga Urushalima suka ce, “Ai, yana da Be’elzebub! Da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”
The scribes who came down from Jerusalem said, “He has Beelzebul,” and, “By the prince of the demons he casts out the demons.”
23 Sai Yesu ya kira su, ya yi musu magana da misalai ya ce, “Yaya Shaiɗan zai fitar da Shaiɗan?
He summoned them and said to them in parables, “How can Satan cast out Satan?
24 In mulki yana gāba da kansa, wannan mulki ba zai tsaya ba.
If a kingdom is divided against itself, that kingdom cannot stand.
25 In gida yana gāba da kansa, wannan gida ba zai tsaya ba.
If a house is divided against itself, that house cannot stand.
26 In kuwa Shaiɗan yana gāba da kansa, ya kuma rabu biyu, ba zai tsaya ba, ƙarshensa ya zo ke nan.
If Satan has risen up against himself, and is divided, he can’t stand, but has an end.
27 Tabbatacce, ba mai shiga gidan mai ƙarfi yă kwashe dukiyarsa, sai bayan ya daure mai ƙarfin, sa’an nan zai iya yin fashin gidansa.
But no one can enter into the house of the strong man to plunder unless he first binds the strong man; then he will plunder his house.
28 Gaskiya nake gaya muku, za a gafarta duk zunubai da kuma saɓon mutane suka yi.
“Most certainly I tell you, all sins of the descendants of man will be forgiven, including their blasphemies with which they may blaspheme;
29 Amma duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a taɓa gafara masa ba. Ya aikata madawwamin zunubi ke nan.” (aiōn g165, aiōnios g166)
but whoever may blaspheme against the Holy Spirit never has forgiveness, but is subject to eternal condemnation.” (aiōn g165, aiōnios g166)
30 Ya faɗi haka domin suna cewa, “Yana da mugun ruhu.”
—because they said, “He has an unclean spirit.”
31 Sai mahaifiyar Yesu tare da’yan’uwansa suka iso. Suna tsaye a waje, sai suka aiki wani ciki yă kira shi.
His mother and his brothers came, and standing outside, they sent to him, calling him.
32 Taron yana zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Mahaifiyarka da’yan’uwanka suna waje, suna nemanka.”
A multitude was sitting around him, and they told him, “Behold, your mother, your brothers, and your sisters are outside looking for you.”
33 Ya yi tambaya ya ce, “Su wane ne mahaifiyata, da’yan’uwana?”
He answered them, “Who are my mother and my brothers?”
34 Sai ya dubi waɗanda suke zaune kewaye da shi ya ce, “Ga mahaifiyata da’yan’uwana!
Looking around at those who sat around him, he said, “Behold, my mother and my brothers!
35 Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da’yar’uwata, da kuma mahaifiyata.”
For whoever does the will of God is my brother, my sister, and mother.”

< Markus 3 >