< Markus 16 >
1 Da Asabbaci ya wuce, sai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub, da kuma Salome suka sayi kayan ƙanshi domin su je su shafa wa jikin Yesu.
2 A ranar farko ta mako, da sassafe, bayan fitowar rana, suna kan hanyarsu zuwa kabarin ke nan,
3 sai suka tambaye juna suka ce, “Wane ne zai gungura mana dutsen daga bakin kabarin?”
4 Amma da suka ɗaga kai, sai suka ga cewa, an riga an gungura dutsen. Dutsen kuwa babba ne.
5 Da suna shiga cikin kabarin, sai suka ga wani saurayi sanye da farar riga, yana zaune a hannun dama, sai suka firgita.
6 Ya ce, “Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi.
7 Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa da kuma Bitrus cewa, ‘Ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.’”
8 Da rawan jiki da kuma ruɗewa, matan suka fita a guje daga kabarin. Ba su kuwa gaya wa kowa ba, don suna tsoro.
9 (note: The most reliable and earliest manuscripts do not include Mark 16:9-20.) Da Yesu ya tashi daga matattu da safe, a ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magdalin, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta.
10 Ta je ta gaya wa waɗanda dā suke tare da shi, waɗanda kuma suke makoki da kuka.
11 Da suka ji cewa Yesu yana da rai, har ma ta gan shi, ba su gaskata ba.
12 Daga baya Yesu ya bayyana a wani kamanni dabam ga biyunsu, yayinda suke tafiya ƙauye.
13 Waɗannan kuwa suka koma suka shaida wa sauran, amma su ma ba su gaskata ba.
14 Bayan haka, Yesu ya bayyana ga Sha Ɗayan, yayinda suke cin abinci. Ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu, da yadda suka ƙi gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi.
15 Ya ce, musu, “Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta.
16 Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka.
17 Waɗannan alamu za su kasance tare da waɗanda suka gaskata. A cikin sunana za su fitar da aljanu, za su yi magana da sababbin harsuna.
18 Za su ɗauki macizai da hannuwansu. In kuwa suka sha mugun dafi, ba zai cuce su ba ko kaɗan. Za su ɗibiya hannuwansu a kan marasa lafiya, su kuwa warke.”
19 Bayan Ubangiji Yesu ya yi musu magana, sai aka ɗauke shi zuwa sama, ya kuma zauna a hannun dama na Allah.
20 Sai almajiran suka fita, suka yi wa’azi ko’ina. Ubangiji kuwa ya yi aiki tare da su, ya tabbatar da maganarsa ta wurin alamu da suke biye da maganar.