< Markus 12 >

1 Sa’an nan ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ya shuka gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa rami domin matsin inabin, ya kuma gina ɗakin gadi. Sai ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, sa’an nan ya yi tafiya.
Sai Yesu ya fara koyar da su da misalai. “Wani mutum ne ya yi gonar inabi ya shingen ta, ya haka ramin matse inabin, ya kuwa gina hasumayar tsaro. Ya ba wandansu manoma jinginar gonar, sa'an nan ya tafi wata kasa mai nisa.
2 Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki wani bawa wajen’yan hayan, don yă karɓo masa’ya’yan inabin daga wurinsu.
Da lokaci ya yi, sai ya aika masu wani bawansa domin ya karbi wadansu daga cikin amfanin gonar.
3 Amma suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannun wofi.
Amma manoman suka kama shi, suka yin masa duka, suka kore shi hannu banza.
4 Sai ya sāke aikan wani bawa wurinsu, amma suka bugi wannan mutum a kai, suka wulaƙanta shi.
Ya sake aikar wani bawan. Shi kuma suka raunata shi aka, suka wulakanta shi.
5 Har yanzu ya sāke aikan wani. Wannan kuwa suka kashe. Ya aika waɗansu da yawa; suka bubbuge waɗansu, sauran kuwa suka kashe.
Ya sake aiken wani. Shi kam, suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da wadansu da yawa, sun dodoki wadansu, suka kuma kashe wadansu.
6 “Sauran mutum ɗaya da ya rage ya aika, ɗa, da yake ƙauna. Daga ƙarshe sai ya aike shi, yana cewa, ‘Za su girmama ɗana.’
Yanzu dai yana da sauran daya tak, shine kaunatacen dansa. Daga karshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, ai za su bashi girma.
7 “Amma’yan hayan suka ce wa juna, ‘Aha! Wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon kuma yă zama namu.’
Amma manoman nan suka ce wa juna, “ai, wannan shine magajinsa, 'ku zo mu kashe shi, gadon ya zama namu.”
8 Sai suka kama shi suka kashe, suka jefa shi bayan gonar inabin.
Sai suka kamo shi, suka kashe shi, suka jefar da shi bayan shinge.
9 “To, me, mai gonar inabin zai yi ke nan? Zai zo yă karkashe dukan’yan hayan nan, ya kuma ba wa waɗansu gonar inabin.
To, me mai gonar inabin zai yi? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba wadansu gonar.
10 Ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba, “‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kusurwan gini.
Ashe, ba ku karanta wannan nassi ba? cewa, ' Dutsen da magina suka ki, shi ne ya zama mafi mahmimanci.
11 Ubangiji ya yi wannan, ya kuma yi kyau a idanunmu’?”
Wannan daga Ubangiji ne, kuma ya yi dai dai a idanunmu.”'
12 Sai manyan Firistoci da malaman dokoki da shugabanni suka nemi hanyar da za su kama shi, domin sun gane ya yi misalin a kansu ne. Amma suka ji tsoron taron, saboda haka suka bar shi suka yi tafiyarsu.
Sai suka nemi su kama shi, don sun lura a kansu ne ya yi masalin, amma suka ji tsoron jama'a. Don haka suka kyele shi, suka tafi.
13 Daga baya, sai suka tura waɗansu Farisiyawa da mutanen Hiridus zuwa wurin Yesu, domin su sa masa tarko a cikin maganarsa.
Suka aika masa da wadansu farisiyawa da Heridiyawa, don su sa masa tarko da kalamai cikin maganarsa.
14 Suka zo wurinsa suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci. Ba ka bin ra’ayin mutane, don ba ka nuna bambanci. Amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. Daidai ne a biya wa Kaisar haraji, ko babu?
Da suka zo, suka ce masa, “Malam, gaskiya kana koyar da maganar Allah sosai, ba ka nuna bambanci tsakani mutane, sai koyar da tafarkin Allah kake yi sosai. “Shin, mu biya haraji ga Kaisar, ko a a?”
15 Mu biya ko kada mu biya?” Amma Yesu ya san munafuncinsu, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku kawo mini dinari in ga.”
AmmaYesu ya gane munafuncinsu, ya ce masu, “Don me kuke gwada ni? ku kawo mani dinarin in gani.”
16 Suka kawo masa kuɗin, sai ya tambaye, su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne wannan?” Suka ce, “Na Kaisar.”
Suka kawowa Yesu daya. Ya ce masu, “Kamar waye da kuma rubutun wanene? suka ce masa, “Na Kaisar ne.”
17 Sai Yesu ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku ba wa Allah kuma abin da yake na Allah.” Suka yi mamakinsa ƙwarai.
Yesu ya ce, “to, ku ba Kaisar abinda yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah. Sai suka yi mamakinsa kwarai.
18 Sa’an nan Sadukiyawa da suke cewa, babu tashin matattu, suka zo masa da tambaya.
Sai Sadukiyawa suka zo wurinsa, su dake cewa babu tashin matattu. Suka tambaya shi suka ce,
19 Suka ce, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, in ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata babu’ya’ya, dole mutumin ya auri gwauruwar, yă kuma samo wa ɗan’uwansa’ya’ya.
“Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan dan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba da, lallai ne dan'uwan mutumin ya auri matar, ya haifa wa dan'uwansa 'ya'ya.'
20 To, an yi waɗansu’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu babu’ya’ya.
To an yi wadansu 'yan'uwa maza guda bakwai, na farko ya yi aure, ya mutu bai bar 'ya'ya ba.
21 Na biyun ya auri gwauruwar, sai shi ma ya mutu, babu’ya’ya. Haka kuma na ukun.
Na biyu kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba 'ya'ya. Na ukun ma haka.
22 A gaskiya, ba ko ɗaya daga cikin bakwai ɗin da ya bar’ya’ya. Daga ƙarshe, macen ta mutu.
Haka dai duk bakwai din, ba wanda ya bar 'ya'ya. A karshe kuma ita matar ta mutu.
23 To, a tashin matattu, matar wa za tă zama, don duk su bakwai nan sun aure ta?”
To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai din nan sun aure ta”.
24 Yesu ya ce, “Ashe, ba a cikin kuskure kuke ba saboda rashin sanin Nassi, ko ikon Allah?
Sai Yesu ya ce, “Ba saboda wannan dalili ne kuka yi kuskure ba, wato don ba ku san littafin ba, kuma ba ku san ikon Allah ba?
25 Sa’ad da matattu suka tashi, ba za su yi aure ba, ba kuwa za a ba da su ga aure ba. Za su zama kamar yadda mala’iku suke a cikin sama.
Domin in an tashin daga matattu, ba a aure, ba a auraswa, amma sun zama kamar malaiku a sama.
26 Game da tashin matattu kuwa, ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’?
Amma game da mattattun da suka tashi, ashe, ba ku taba karantawa a littafin Musa ba, yadda Allah ya ce masa? “Ni ne Allah na Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu'?
27 Shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne. Kun yi mummunan kuskure!”
Ai, shi ba Allahn mattatu bane, amma na rayyayu ne. Hakika kun yi kuskure “.
28 Wani daga cikin malaman dokoki ya zo ya ji suna muhawwara. Da ya lura cewa Yesu ya amsa musu daidai, sai ya tambaye shi ya ce, “A cikin dukan dokoki, wacce ta fi girma duka?”
Sai wani malamin attuara ya zo ya ji suna muhawara da juna. Da dai ya ga Yesu yana ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, “Wanne Umarni ne mafi girma dukka?”
29 Yesu ya ce, “Wadda ta fi girma duka, ita ce wannan. ‘Ku saurara, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.
Yesu ya amsa yace, “mafi girma shine, 'ku saurara ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji daya ne.
30 Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’
Sai ka kaunaci Ubangiji Allah da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka da dukkan tunaninka, da dukkan karfinka.
31 Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’Ba wata doka da ta fi waɗannan.”
ta biyu itace, 'ka kaunaci makwabcinka kamar kanka, Ba wata doka da ta fi wadannan.''
32 Mutumin ya ce, “Malam, ka faɗi daidai. Daidai ne da ka ce, Allah ɗaya ne, babu kuma wani sai shi.
Sai malamin attaura ya ce masa, “Hakika gaskiyarka malam, Allah daya ne, ba kuma wani sai shi.
33 Nuna ƙauna ga Allah da dukan zuciyarka, da dukan ganewarka, da dukan ƙarfinka, da kuma nuna ƙauna ga maƙwabcinka kamar kanka, ya fi dukan hadayun ƙonawa da sadakoki.”
A kaunace shi kuma da dukkan zuciya, da dukkan hankali, da dukkan karfi, a kuma kaunaci makwabci kamar kanka, ai ya fi dukkan hadayu na konawa.”
34 Da Yesu ya ga ya amsa da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka da nisa da mulkin Allah.” Daga lokacin, ba wanda ya yi karambani yin masa wata tambaya.
Da Yesu ya ga ya yi masa magana da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka nesa da mulkin Allah.” Bayan wannan kuma ba wanda ya sake tambayarsa wani abu.
35 Yayinda Yesu yake koyarwa a filin haikalin, sai ya yi tambaya ya ce, “Yaya malaman dokoki suke cewa Kiristi ɗan Dawuda ne?
Yesu ya amsa a lokacin da yake koyarwa a Haikali, ya ce “Yaya malaman attaura suke ce wa Kristi dan Dauda ne?
36 Dawuda da kansa ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin sawunka.”’
Domin Dauda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ubangiji ya ce wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na kaskantar da makiyanka'.
37 Dawuda da kansa ya kira shi ‘Ubangiji.’ To, ta yaya zai zama ɗansa?” Taro mai yawa suka saurare shi da murna.
Dauda da kansa ya kira shi 'Ubangiji; To, ta yaya ya Almasihu zai zama Dan Dauda?” Babban taron jama'ar suka saurare shi da murna.
38 Sa’ad da Yesu yake koyarwa ya ce, “Ku lura da malaman dokoki. Sukan so yin tafiya a manyan riguna, a kuma dinga gaishe su a wuraren kasuwanci.
A koyarwa sa Yasu ya ce, “ku yi hankali da malaman attaura, masu son yawo da manyan riguna, suna so a gaishesu a kasuwa,
39 Sukan kuma nemi wuraren zama mafi daraja a majami’u, da kuma wuraren zaman manya a bukukkuwa.
da kuma son wuraren zama masu daraja a haikali, da wurin bukukuwa.
40 Suna ƙwace gidajen gwauraye, kuma don nuna iyawa, sukan yi dogayen addu’o’i. Irin mutanen nan, za su sha hukunci mai tsanani sosai.”
Sun kuma kwace gidajen gwauraye, da yin doguwar addu'a, don mutane su gani. Wadanan mutanen zasu sami hukunci mai tsanani.”
41 Yesu ya zauna ɗaura da inda ake bayarwa, ya kuma dubi yadda taron suke sa kuɗinsu a cikin ɗakunan ajiya haikali. Masu arziki da yawa suka zuba kuɗaɗe masu yawa.
Sai ya zauna a gaban akwatin baiko a Haikalin, yana duban yadda jama'a suke zuba kudi a ciki.
42 Amma wata matalauciya gwauruwa, ta zo ta saka anini biyu, da suka yi daidai da rabin kobo.
Wadansu masu arziki da yawa suna zuba kudi masu tsoka. Sai gwauruwa mara abin hanu ta saka anini biyu a ciki akwatin baikon.
43 Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, abin da matalauciya gwauruwan nan ta zuba cikin ɗakunan ajiya nan ya fi na sauran dukan.
Ya kira almajiransa, ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, abinda gwauruwa nan ta saka a akwatin baikon nan ya fi na sauran dukka.
44 Dukansu sun bayar ne daga cikin arzikinsu; ita kuwa, daga cikin talaucinta, ta ba da kome, duk abin da take da shi na rayuwa.”
Su duk sun bayar daga yalwa tasu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta bada duk abinda take da shi.”

< Markus 12 >