< Markus 11 >

1 Sa’ad da suka yi kusa da Urushalima, suka zo Betfaji da Betani wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki biyu daga cikin almajiransa,
כאשר התקרבו לירושלים והגיעו לבית־פגי ובית־עניה, שעל הר הזיתים, פנה ישוע אל שניים מתלמידיו ואמר:
2 ya ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku, da shigarku, za ku tarar da wani ɗan jaki a daure a can, wanda ba wanda ya taɓa hawa. Ku kunce shi ku kawo nan.
”לכו אל הכפר ממול, ובכניסה תראו עַיִר קשור שאיש עדיין לא רכב עליו. התירו את העיר והביאו אותו אלי.
3 In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke yin haka?’ Ku gaya masa cewa, ‘Ubangiji yana bukatarsa, zai kuma dawo da shi ba da jimawa ba.’”
אם מישהו ישאל אתכם מה אתם עושים, אמרו לו,’האדון זקוק לעיר, אך הוא ישיב אותו בהקדם‘. “
4 Suka tafi, suka kuwa tarar da wani ɗan jaki a waje, a titi, daure a ƙofar gida. Suna cikin kunce shi ke nan,
שני התלמידים נכנסו אל הכפר ומצאו את העיר עומד על השביל, קשור לשער אחד הבתים. בהתירם את העיר שאלו מספר אנשים שעמדו שם:”מה אתם עושים? לאן אתם לוקחים את העיר?“
5 sai waɗansu mutane da suke tsattsaye a wurin suka ce musu, “Me kuke yi da kuke kunce ɗan jakin nan?”
6 Suka amsa kamar yadda Yesu ya ce su yi. Mutanen kuwa suka ƙyale su.
התלמידים השיבו שישוע ביקש מהם להביא לו את העיר, והאנשים לא התנגדו יותר.
7 Da suka kawo shi wajen Yesu, sai suka shimfiɗa rigunarsu a bayansa. Yesu kuwa ya hau ya zauna bisansa.
הם הביאו את העיר לישוע, וכל התלמידים הניחו את מעיליהם על גבו, כדי שישוע יוכל לשבת בנוח.
8 Mutane da yawa suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza rassan itatuwan da suka sara daga gonaki.
רבים מן הקהל פרשו את מעיליהם על הדרך לפני ישוע, ואחרים כרתו ענפים והניחו אותם על הדרך.
9 Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!”
הקהל, שנמלא התלהבות, נדחף ונדחק אל ישוע מכל עבר וקרא:”הושע־נא! ברוך הבא בשם ה׳!
10 “Mai albarka ne mulkin nan mai zuwa na mahaifinmu Dawuda!” “Hosanna a can cikin samaniya!”
תבורך מלכות דוד הבאה עלינו! הושע־נא במרומים!“
11 Yesu ya shiga Urushalima ya kuma tafi filin haikali. Ya dudduba kome duka, amma da yake yamma ta yi, sai ya tafi Betani tare da Sha Biyun.
כל הקהל הזה ליווה את ישוע אל תוך העיר. מאוחר יותר נכנס ישוע לבית־המקדש והביט סביבו בתשומת לב מרובה, אולם מאחר שהשעה הייתה מאוחרת הוא עזב את המקום והלך עם תלמידיו לבית־עניה.
12 Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa.
למחרת בבוקר, בעזבם את בית־עניה, היה ישוע רעב.
13 Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin’ya’yan ɓaure ba ne.
הוא ראה מרחוק עץ תאנה עם עלים ירוקים ורעננים. ישוע התקרב אל העץ וחיפש תאנים, אולם לא מצא דבר מלבד עלים, כי טרם הגיעה העונה.
14 Sai ya ce wa itacen, “Kada kowa yă ƙara cin’ya’yanka.” Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka. (aiōn g165)
ישוע קילל את התאנה ואמר:”מהיום והלאה איש לא יאכל תאנים ממך!“והתלמידים שמעו זאת. (aiōn g165)
15 Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru,
הם חזרו לירושלים וישוע הלך ישר לבית־המקדש. הוא החל לגרש משם את הסוחרים והקונים, הפך את השולחנות של מחליפי הכספים ואת הדוכנים של סוחרי היונים,
16 ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki.
ולא הרשה לאיש לשאת כלים וסחורה דרך המקדש.
17 Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’? Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon’yan fashi.’”
ישוע פנה אל הקהל הנדהם:”כתוב בכתבי־הקודש:’ביתי בית־תפלה ייקרא לכל העמים‘. אולם אתם הפכתם אותו למאורת גנבים!“
18 Manyan firistoci da malaman dokoki suka ji wannan, sai suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, saboda dukan taron suna mamakin koyarwarsa.
ראשי הכוהנים והסופרים שמעו על מה שישוע עשה, והחלו לתכנן כיצד להיפטר ממנו. למעשה הם פחדו ממנו, מפני שכל העם העריץ אותו ואהב את מה שלימד.
19 Da yamma ta yi, sai Yesu da almajiransa suka bar garin.
באותו ערב יצאו ישוע ותלמידיו אל מחוץ לעיר.
20 Da safe, da suke wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya yanƙwane tun daga saiwarsa.
בבוקר שוב עברו ליד עץ התאנה, ונדהמו לראות שהעץ יבש לגמרי.
21 Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, “Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka la’anta, ya yanƙwane!”
פטרוס נזכר במה שישוע עשה יום קודם ואמר:”ראה, רבי – העץ שקיללת התייבש לגמרי!“
22 Yesu ya amsa ya ce, “Ku gaskata da Allah.
”פשוט האמינו באלוהים“, אמר ישוע.
23 Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa.
”אילו באמת האמנתם בכוחו של אלוהים, יכולתם לצוות על ההר הזה לזוז ממקומו ולהיזרק לים. אם תאמינו ולא תטילו ספק יתקיים דברכם.
24 Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku.
דעו לכם, אתם יכולים להתפלל בעד כל דבר, ואם תאמינו שתקבלו את אשר ביקשתם, באמת תקבלו!
25 A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku.”
אבל בשעה שאתם מתפללים עליכם לסלוח תמיד לכל מי שאתם שומרים לו טינה, כדי שאביכם שבשמים יסלח גם לכם על חטאיכם.
אם לא תסלחו לאחרים – גם אביכם שבשמים לא יסלח לכם!“
27 Suka sāke dawowa cikin Urushalima. Da Yesu yana tafiya a filin haikali, sai manyan firistoci, malaman dokoki da kuma dattawa suka zo wurinsa.
בינתיים ישוע ותלמידיו חזרו לירושלים, וישוע שב לבית־המקדש. אחדים מראשי הכוהנים הסופרים וזקנים באו אליו ושאלו בכעס:”באיזו רשות אתה עושה את כל הדברים האלה?“
28 Suka tambaye, shi suka ce, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Wa kuma ya ba ka ikon yin wannan?”
29 Yesu ya ce, “Zan yi muku tambaya guda. Ku ba ni amsa, ni kuma zan gaya muku, ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa.
”אני אענה לשאלתכם בתנאי שאתם תענו לשאלתי“, השיב ישוע.
30 Baftismar Yohanna, daga sama ce, ko daga mutane? Ku faɗa mini!”
”אמרו לי, האם נשלח יוחנן המטביל על־ידי אלוהים או על־ידי בני־אדם?“
31 Sai suka tattauna a junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
הם התייעצו ביניהם:”אם נאמר שאלוהים שלח אותו, ישוע ישאל אותנו מדוע לא האמנו בו.
32 In kuma muka ce, ‘Daga wurin mutane ne’; suna jin tsoron mutane, don kowa ya ɗauka cewa, Yohanna, annabi ne na gaskiya.”
אולם אם נאמר שלא אלוהים שלח אותו, כל העם יתנפל עלינו, כי כולם חושבים שיוחנן היה נביא שנשלח על־ידי אלוהים.“
33 Saboda haka, suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”
לבסוף השיבו:”איננו יודעים.“על כן השיב להם ישוע:”אם כן, גם אני לא אענה לשאלתכם.“

< Markus 11 >