< Markus 10 >
1 Sai Yesu ya tashi daga nan ya tafi yankin Yahudiya, da kuma ƙetaren Urdun. Taron mutane suka sāke zuwa wurinsa, ya kuma koya musu kamar yadda ya saba.
Κἀκεῖθεν ἀναστὰς ἔρχεται εἰς τὰ ὅρια τῆς Ἰουδαίας διὰ τοῦ πέραν τοῦ Ἰορδάνου· καὶ συμπορεύονται πάλιν ὄχλοι πρὸς αὐτόν· καί, ὡς εἰώθει, πάλιν ἐδίδασκεν αὐτούς.
2 Waɗansu Farisiyawa suka zo suka gwada shi, ta wurin yin masa tambaya cewa, “Daidai ne bisa ga doka, mutum yă saki matarsa?”
Καὶ προσελθόντες Φαρισαῖοι ἐπηρώτησαν αὐτόν, Εἰ ἔξεστιν ἀνδρὶ γυναῖκα ἀπολῦσαι, πειράζοντες αὐτόν.
3 Ya amsa ya ce, “Me Musa ya umarce ku?”
Ὁ δὲ ἀποκριθεὶς εἶπεν αὐτοῖς, Τί ὑμῖν ἐνετείλατο Μωσῆς;
4 Suka ce, “Musa ya ba da izini mutum yă rubuta takardar saki, yă kuma kore ta.”
Οἱ δὲ εἶπον, Μωσῆς ἐπέτρεψε βιβλίον ἀποστασίου γράψαι, καὶ ἀπολῦσαι.
5 Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka.
Καὶ ἀποκριθεὶς ὁ Ἰησοῦς εἶπεν αὐτοῖς, Πρὸς τὴν σκληροκαρδίαν ὑμῶν ἔγραψεν ὑμῖν τὴν ἐντολὴν ταύτην·
6 Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’
ἀπὸ δὲ ἀρχῆς κτίσεως, ἄρσεν καὶ θῆλυ ἐποίησεν αὐτοὺς ὁ Θεός.
7 ‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa,
Ἕνεκεν τούτου καταλείψει ἄνθρωπος τὸν πατέρα αὐτοῦ καὶ τὴν μητέρα, καὶ προσκολληθήσεται πρὸς τὴν γυναῖκα αὐτοῦ,
8 su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya.
καὶ ἔσονται οἱ δύο εἰς σάρκα μίαν. Ὥστε οὐκέτι εἰσὶ δύο, ἀλλὰ μία σάρξ.
9 Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yă raba.”
Ὃ οὖν ὁ Θεὸς συνέζευξεν, ἄνθρωπος μὴ χωριζέτω.
10 Da suna cikin gida kuma, sai almajiran suka tambayi Yesu game da wannan.
Καὶ ἐν τῇ οἰκίᾳ πάλιν οἱ μαθηταὶ αὐτοῦ περὶ τοῦ αὐτοῦ ἐπηρώτησαν αὐτόν.
11 Ya amsa ya ce, “Duk wanda ya saki matarsa, ya auri wata, yana da laifin aikata zina a kan matar da ya saki.
Καὶ λέγει αὐτοῖς, Ὃς ἐὰν ἀπολύσῃ τὴν γυναῖκα αὐτοῦ καὶ γαμήσῃ ἄλλην, μοιχᾶται ἐπ᾽ αὐτήν·
12 In kuma ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”
καὶ ἐὰν γυνὴ ἀπολύσῃ τὸν ἄνδρα αὐτῆς καὶ γαμηθῇ ἄλλῳ, μοιχᾶται.
13 Mutane suka kawo ƙananan yara wurin Yesu don yă taɓa su, amma almajiran suka kwaɓe su.
Καὶ προσέφερον αὐτῷ παιδία, ἵνα ἅψηται αὐτῶν· οἱ δὲ μαθηταὶ ἐπετίμων τοῖς προσφέρουσιν.
14 Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.
Ἰδὼν δὲ ὁ Ἰησοῦς ἠγανάκτησε, καὶ εἶπεν αὐτοῖς, Ἄφετε τὰ παιδία ἔρχεσθαι πρός με· μὴ κωλύετε αὐτά· τῶν γὰρ τοιούτων ἐστὶν ἡ βασιλεία τοῦ Θεοῦ.
15 Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”
Ἀμὴν λέγω ὑμῖν, ὃς ἐὰν μὴ δέξηται τὴν βασιλείαν τοῦ Θεοῦ ὡς παιδίον, οὐ μὴ εἰσέλθῃ εἰς αὐτήν.
16 Sai ya ɗauki yaran a hannuwansa, ya ɗibiya musu hannuwansa, ya kuma albarkace su.
Καὶ ἐναγκαλισάμενος αὐτά, τιθεὶς τὰς χεῖρας ἐπ᾽ αὐτά, εὐλόγει αὐτά.
17 Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?” (aiōnios )
Καὶ ἐκπορευομένου αὐτοῦ εἰς ὁδόν, προσδραμὼν εἷς καὶ γονυπετήσας αὐτὸν ἐπηρώτα αὐτόν, Διδάσκαλε ἀγαθέ, τί ποιήσω ἵνα ζωὴν αἰώνιον κληρονομήσω; (aiōnios )
18 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai.
Ὁ δὲ Ἰησοῦς εἶπεν αὐτῷ, Τί με λέγεις ἀγαθόν; Οὐδεὶς ἀγαθός, εἰ μὴ εἷς, ὁ Θεός.
19 Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’”
Τὰς ἐντολὰς οἶδας, Μὴ μοιχεύσῃς, μὴ φονεύσῃς, μὴ κλέψῃς, μὴ ψευδομαρτυρήσῃς, μὴ ἀποστερήσῃς, τίμα τὸν πατέρα σου καὶ τὴν μητέρα.
20 Mutumin ya ce, “Malam, ai, tun ina yaro na kiyaye duk waɗannan.”
Ὁ δὲ ἀποκριθεὶς εἶπεν αὐτῷ, Διδάσκαλε, ταῦτα πάντα ἐφυλαξάμην ἐκ νεότητός μου.
21 Yesu ya kalle shi da ƙauna ya ce, “Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.”
Ὁ δὲ Ἰησοῦς ἐμβλέψας αὐτῷ ἠγάπησεν αὐτόν, καὶ εἶπεν αὐτῷ, Ἕν σοι ὑστερεῖ· ὕπαγε, ὅσα ἔχεις πώλησον, καὶ δὸς πτωχοῖς, καὶ ἕξεις θησαυρὸν ἐν οὐρανῷ· καὶ δεῦρο, ἀκολούθει μοι, ἄρας τὸν σταυρόν.
22 Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, gama yana da arziki sosai.
Ὁ δὲ στυγνάσας ἐπὶ τῷ λόγῳ ἀπῆλθε λυπούμενος· ἦν γὰρ ἔχων κτήματα πολλά.
23 Yesu ya dudduba, sai ya ce wa almajiransa, “Yana da wuya fa masu arziki su shiga mulkin Allah!”
Καὶ περιβλεψάμενος ὁ Ἰησοῦς λέγει τοῖς μαθηταῖς αὐτοῦ, Πῶς δυσκόλως οἱ τὰ χρήματα ἔχοντες εἰς τὴν βασιλείαν τοῦ Θεοῦ εἰσελεύσονται.
24 Almajiransa suka yi mamakin kalmominsa. Amma Yesu ya sāke ce musu, “’Ya’yana, yana da wuya fa a shiga mulkin Allah!
Οἱ δὲ μαθηταὶ ἐθαμβοῦντο ἐπὶ τοῖς λόγοις αὐτοῦ. Ὁ δὲ Ἰησοῦς πάλιν ἀποκριθεὶς λέγει αὐτοῖς, Τέκνα, πῶς δύσκολόν ἐστι τοὺς πεποιθότας ἐπὶ χρήμασιν εἰς τὴν βασιλείαν τοῦ Θεοῦ εἰσελθεῖν.
25 Ya fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”
Εὐκοπώτερόν ἐστι κάμηλον διὰ τῆς τρυμαλιᾶς τῆς ῥαφίδος εἰσελθεῖν, ἢ πλούσιον εἰς τὴν βασιλείαν τοῦ Θεοῦ εἰσελθεῖν.
26 Almajiran suka yi mamaki ƙwarai, suka ce wa juna, “To, wa zai sami ceto ke nan?”
Οἱ δὲ περισσῶς ἐξεπλήσσοντο, λέγοντες πρὸς ἑαυτούς, Καὶ τίς δύναται σωθῆναι;
27 Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah, wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah.”
Ἐμβλέψας δὲ αὐτοῖς ὁ Ἰησοῦς λέγει, Παρὰ ἀνθρώποις ἀδύνατον, ἀλλ᾽ οὐ παρὰ Θεῷ· πάντα γὰρ δυνατά ἐστι παρὰ τῷ Θεῷ.
28 Bitrus ya ce, “Mun bar kome domin mu bi ka!”
Ἤρξατο ὁ Πέτρος λέγειν αὐτῷ, Ἰδού, ἡμεῖς ἀφήκαμεν πάντα καὶ ἠκολουθήσαμέν σοι.
29 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko’yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko’ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara,
Ἀποκριθεὶς ὁ Ἰησοῦς εἶπεν, Ἀμὴν λέγω ὑμῖν, οὐδείς ἐστιν ὃς ἀφῆκεν οἰκίαν, ἢ ἀδελφούς, ἢ ἀδελφάς, ἢ πατέρα, ἢ μητέρα, ἢ γυναῖκα, ἢ τέκνα, ἢ ἀγρούς, ἕνεκεν ἐμοῦ καὶ ἕνεκεν τοῦ εὐαγγελίου,
30 sa’an nan yă kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da’yan’uwa mata, da’yan’uwa maza, da uwaye, da’ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma yă sami rai madawwami. (aiōn , aiōnios )
ἐὰν μὴ λάβῃ ἑκατονταπλασίονα νῦν ἐν τῷ καιρῷ τούτῳ, οἰκίας καὶ ἀδελφοὺς καὶ ἀδελφὰς καὶ μητέρας καὶ τέκνα καὶ ἀγρούς, μετὰ διωγμῶν, καὶ ἐν τῷ αἰῶνι τῷ ἐρχομένῳ ζωὴν αἰώνιον. (aiōn , aiōnios )
31 Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, na ƙarshe kuma, za su zama na farko.”
Πολλοὶ δὲ ἔσονται πρῶτοι ἔσχατοι, καὶ ἔσχατοι πρῶτοι.
32 Suna haurawa a hanyarsu zuwa Urushalima ke nan, Yesu yana a gaba, almajiran suna bin sa suna mamaki, waɗanda suke bi kuma suna ji tsoro. Ya sāke kai Sha Biyun nan gefe, ya gaya musu abin da zai faru da shi.
Ἦσαν δὲ ἐν τῇ ὁδῷ ἀναβαίνοντες εἰς Ἱεροσόλυμα· καὶ ἦν προάγων αὐτοὺς ὁ Ἰησοῦς, καὶ ἐθαμβοῦντο, καὶ ἀκολουθοῦντες ἐφοβοῦντο. Καὶ παραλαβὼν πάλιν τοὺς δώδεκα, ἤρξατο αὐτοῖς λέγειν τὰ μέλλοντα αὐτῷ συμβαίνειν·
33 Ya ce, “Za mu haura zuwa Urushalima, za a bashe Ɗan Mutum, ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa, a kuma ba da shi ga Al’ummai,
ὅτι Ἰδού, ἀναβαίνομεν εἰς Ἱεροσόλυμα, καὶ ὁ υἱὸς τοῦ ἀνθρώπου παραδοθήσεται τοῖς ἀρχιερεῦσι καὶ γραμματεῦσι, καὶ κατακρινοῦσιν αὐτὸν θανάτῳ, καὶ παραδώσουσιν αὐτὸν τοῖς ἔθνεσι,
34 waɗanda za su yi masa ba’a, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kuma kashe shi. Bayan kwana uku kuma yă tashi.”
καὶ ἐμπαίξουσιν αὐτῷ, καὶ μαστιγώσουσιν αὐτόν, καὶ ἐμπτύσουσιν αὐτῷ, καὶ ἀποκτενοῦσιν αὐτόν· καὶ τῇ τρίτῃ ἡμέρᾳ ἀναστήσεται.
35 Sai Yaƙub da Yohanna,’ya’yan Zebedi maza suka zo wurinsa suka ce, “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙa.”
Καὶ προσπορεύονται αὐτῷ Ἰάκωβος καὶ Ἰωάννης οἱ υἱοὶ Ζεβεδαίου, λέγοντες, Διδάσκαλε, θέλομεν ἵνα ὃ ἐὰν αἰτήσωμεν, ποιήσῃς ἡμῖν.
36 Ya tambaye su ya ce, “Me kuke so in yi muku?”
Ὁ δὲ εἶπεν αὐτοῖς, Τί θέλετε ποιῆσαί με ὑμῖν;
37 Suka amsa suka ce, “Ka bar ɗayanmu yă zauna a damarka, ɗayan kuma a hagunka, a cikin ɗaukakarka.”
Οἱ δὲ εἶπον αὐτῷ, Δὸς ἡμῖν, ἵνα εἷς ἐκ δεξιῶν σου καὶ εἷς ἐξ εὐωνύμων σου καθίσωμεν ἐν τῇ δόξῃ σου.
38 Yesu ya ce, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya shan kwaf da zan sha, ko a yi muku baftisma da baftismar da aka yi mini?”
Ὁ δὲ Ἰησοῦς εἶπεν αὐτοῖς, Οὐκ οἴδατε τί αἰτεῖσθε. Δύνασθε πιεῖν τὸ ποτήριον ὃ ἐγὼ πίνω, καὶ τὸ βάπτισμα ὃ ἐγὼ βαπτίζομαι βαπτισθῆναι;
39 Suka ce, “Za mu iya.” Yesu ya ce musu, “Za ku sha kwaf da zan sha, a kuma yi muku baftisma da aka yi mini,
Οἱ δὲ εἶπον αὐτῷ, Δυνάμεθα. Ὁ δὲ Ἰησοῦς εἶπεν αὐτοῖς, Τὸ μὲν ποτήριον ὃ ἐγὼ πίνω πίεσθε, καὶ τὸ βάπτισμα ὃ ἐγὼ βαπτίζομαι βαπτισθήσεσθε·
40 amma zama a damana ko haguna, ba ni nake ba da izinin ba. Waɗannan wurare na waɗanda aka riga aka shirya musu ne.”
τὸ δὲ καθίσαι ἐκ δεξιῶν μου καὶ ἐξ εὐωνύμων οὐκ ἔστιν ἐμὸν δοῦναι, ἀλλ᾽ οἷς ἡτοίμασται.
41 Da sauran goman suka ji wannan, sai suka yi fushi da Yaƙub da Yohanna.
Καὶ ἀκούσαντες οἱ δέκα ἤρξαντο ἀγανακτεῖν περὶ Ἰακώβου καὶ Ἰωάννου.
42 Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani waɗanda aka san su da mulkin al’ummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko.
Ὁ δὲ Ἰησοῦς προσκαλεσάμενος αὐτοὺς λέγει αὐτοῖς, Οἴδατε ὅτι οἱ δοκοῦντες ἄρχειν τῶν ἐθνῶν κατακυριεύουσιν αὐτῶν, καὶ οἱ μεγάλοι αὐτῶν κατεξουσιάζουσιν αὐτῶν.
43 Ba haka ya kamata yă zama da ku ba. A maimakon, duk wanda yake so yă zama babba a cikinku, dole yă zama bawanku.
Οὐχ οὕτω δὲ ἔσται ἐν ὑμῖν· ἀλλ᾽ ὃς ἐὰν θέλῃ γενέσθαι μέγας ἐν ὑμῖν ἔσται ὑμῶν διάκονος·
44 Duk wanda kuma yake so yă zama na farko, dole yă zama bawan kowa.
καὶ ὃς ἐὰν θέλῃ ὑμῶν γενέσθαι πρῶτος, ἔσται πάντων δοῦλος.
45 Gama ko Ɗan Mutum ma, bai zo domin a bauta masa ba, amma don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”
Καὶ γὰρ ὁ υἱὸς τοῦ ἀνθρώπου οὐκ ἦλθε διακονηθῆναι, ἀλλὰ διακονῆσαι, καὶ δοῦναι τὴν ψυχὴν αὐτοῦ λύτρον ἀντὶ πολλῶν.
46 Sai suka iso Yeriko. Sa’ad da Yesu da almajiransa tare da taro mai yawa suke barin birnin, wani makaho da ake kira Bartimawus kuwa (wato, “ɗan Timawus”), yana zaune a gefen hanya yana bara.
Καὶ ἔρχονται εἰς Ἰεριχώ· καὶ ἐκπορευομένου αὐτοῦ ἀπὸ Ἰεριχώ, καὶ τῶν μαθητῶν αὐτοῦ, καὶ ὄχλου ἱκανοῦ, υἱὸς Τιμαίου Βαρτίμαιος ὁ τυφλὸς ἐκάθητο παρὰ τὴν ὁδὸν προσαιτῶν.
47 Da ya ji cewa Yesu Banazare ne, sai ya ɗaga murya, yana cewa, “Yesu Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”
Καὶ ἀκούσας ὅτι Ἰησοῦς ὁ Ναζωραῖός ἐστιν, ἤρξατο κράζειν καὶ λέγειν, Ὁ υἱὸς Δαυίδ, Ἰησοῦ, ἐλέησόν με.
48 Mutane da yawa suka kwaɓe shi, suka ce yă yi shiru, amma ya ƙara ɗaga murya yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”
Καὶ ἐπετίμων αὐτῷ πολλοί, ἵνα σιωπήσῃ· ὁ δὲ πολλῷ μᾶλλον ἔκραζεν, Υἱὲ Δαυίδ, ἐλέησόν με.
49 Yesu ya tsaya ya ce, “Ku kira shi.” Sai suka kira makahon suka ce, “Ka yi farin ciki! Tashi tsaye! Yana kiranka.”
Καὶ στὰς ὁ Ἰησοῦς εἶπεν αὐτὸν φωνηθῆναι· καὶ φωνοῦσι τὸν τυφλόν, λέγοντες αὐτῷ, Θάρσει· ἔγειραι, φωνεῖ σε.
50 Ya jefar da mayafinsa waje ɗaya, ya yi wuf, ya zo wurin Yesu.
Ὁ δὲ ἀποβαλὼν τὸ ἱμάτιον αὐτοῦ ἀναστὰς ἦλθε πρὸς τὸν Ἰησοῦν.
51 Yesu ya tambaye shi ya ce, “Me kake so in yi maka?” Makahon ya ce, “Rabbi, ina so in sami ganin gari.”
Καὶ ἀποκριθεὶς λέγει αὐτῷ ὁ Ἰησοῦς, Τί θέλεις ποιήσω σοί; Ὁ δὲ τυφλὸς εἶπεν αὐτῷ, Ῥαββουνί, ἵνα ἀναβλέψω.
52 Yesu ya ce, “Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi.
Ὁ δὲ Ἰησοῦς εἶπεν αὐτῷ, Ὕπαγε· ἡ πίστις σου σέσωκέ σε. Καὶ εὐθέως ἀνέβλεψε, καὶ ἠκολούθει τῷ Ἰησοῦ ἐν τῇ ὁδῷ.